Aniversary

170 10 0
                                    

A kan matakalen bene taci karo da Abdulkareem. Wanda a take suka saki murmushi gaba dayan su.

"Good morning sir"
Khairi ta gaishe shi tana murmushin

"Bazan ansa ba shine baki jira ni ba yau. Naje gidan me gadi yace kin tafi kuma ina ta kiran phone dinki switched off"

"Kayi hakuri, wayar ce babu charji shiyasa amma yanzu na samu charji da nazo office"

"Baku da wuta ne"
Ya tambaya tare da yi mata kallon tuhuma.

Se da ta dan duburbuce saboda karyar da tayi, da kyar ta iya kwakulo wata karyar
"Charger ce ta lalace"
Ta fada tana yake

Shide ya ji ta ne amma be yarda ba, ya san tana gudun shi ne kawai. Amman Yayi understanding abunda yasa tayi hakan.
"Ina zaki je ne haka kike sauri"
Ya tambaya tare da kare mata kallo, lallai khairin tashi yar kwalliya ce, duk abunda tasa kyau yake mata

"Ina so na je gurin su intisar na dan taya su wani aiki nasan aiki yayi musu yawa, duk da time ya kusa yi ma"
Ta answer tare da duba agogon da ke hannun ta

"Would you like to see my office"
Ya tambaya fuska cike da shauki.

Khairi tayi dariya ganin yadda da yayi tambayar kamar karamin yaro sannan tace

"Lead the way"

"No ladies first"

Suka tuntsure da dariya, haka suka jero suna hira gwanin sha'awa, gashi duk sanda suka jera se sun dauki ido saboda yadda suke matukar yin kyau tare.
A haka har suka isa office dinsa, yayi mata iso cikin office wanda ya hadu komai tsaf tsaf se kanshi ke tashi.

Da sauri ya janyo mata kujerar sa da yake zama irin me jujjuyawar nan.

"Na zauna a kujerar oga kuwa"
Ta fada tare da rike habarta da mamaki

"Kema oganiyar ce ay"

"To shikenan bari na zauna"

Khairi ta zauna tana dan jujjuya ta a hankali. A kan table dinsa ta ci karo da wayarsa wanda tayi haske alamar sako ya shiga wayar. Idon ta ya kai kan wayar se ta ga hoton cheery 🍒 akan wallpaper wayar. Bata san me yasa hoton cherry ya tsaya mata a rai ba, haka kawai taji kamar tana da alaka da wannan hoton amma duk yadda ta so ta tuno menene abun ya ci tura. Haka ta hakura ta mika masa wayar tare da cewa

"Kamar anyi maka message"

Ak ya karba wayar sannan yace
"Thank you maam"

"Wace maam din kuma"
Khairi tayi masa hararar wasa

"Ke mana"

Daga haka yayi ta tsokanar ta dan Duk maganar da tayi se ya ce mata. "Yes maam". Tun tana bata rai har ta koma dariya.

Haka sukayi ta hira amma a kasan zuciyar khairi tausayin Abdulkareem take, tasan yana son ta. Domin soyayyar da yake mata ba abun da yake buya bane.

Kwata kwata yaki ya yarda su taso da maganar abunda ya faru, baya son ya bawa abun mahimmanci sosai duk da yasan umar babban threat ne a alakar su. Ya gwammace yayi bearing pain din shi kadai, ya gwammace yayi masking nashi pain din ko dan ya samu walwalar khairi.
idanun sa sunyi zurfi daga ganin shi kasan be samu wani isasshen bacci me kyau ba.

Suna cikin hirar ne secretary na building ya shigo yana tambayar Ak slides din presenntation da Ak zeyi a wajen event din aniversary.
Ak ya manta ya bar flash din a mota haka yace ma khairi ta bashi minti kadan yaje ya dauko flash din, suka fita da secretary tare.

Bayan fitar su ne khairi ta tuno itama ta manta bata dauko jakar ta daga office ba garin sauri. gashi har 11 din ta kusa. Haka ta koma office dinta tare da adduan Allah yasa kar ta hadu da umar.

Cikin sanda ta shiga cikin office din da zummar daukan jakar ta fito ba tare da tayi motsin da ze san tana wajen ba. Kofar da ta hada office dinta da tashi a bude take, ta hango shi a tsaye amma ya juya mata baya yana waya.

Sand'ar ta ci gaba da yi kamar barauniya har ta kai inda jakar take a kan table. Kafin ta dauki jakar ne taji muryar umar yana magana a waya, yana cewa

" this aniversary will be the last aniversary in this company, i will destroy it today"
(Wannan aniversary shine na karshe a company nan dan se na ruguza shi yau)

Bata san abunda wanda yake wayar da shi ya fada ba, se maganar umar da ta sake ji

"I have the evidences, i have everything to destroy it, all records ,all transactions, all documents of agreement every thing and i will present everything today for the world to see, I've already invited my lawyers and today is the day silver construction will be no more"
(Ina da hujjoji da zan iya lalata komai. Inada takardun komai hade da takardun fita da shigar kudade, takardun yarjejeniya da komai da komai. yau zan nuna komai a gurin taro saboda duniya ta gani, na riga na kira lauyoyina saboda haka yaune ranar karshe ma silver construction)

Tsananin mamaki da tsoro ne ya kamata har ta saki jakar da ta dauka a kasa wanda ya janyo hankalin umar ya juya ya ganta a tsaye. Daga ganin yadda tsoro ya bayyana a fuskarta yasan taji komai, taji duk abubda ya fada.

Da sauri ya kashe wayar tare da yin wani tsalle ya karaso inda take, Se ganin shi tayi a gaban ta.

"Me nake ji??"
Ta fada duk da tana ji kamar a mafarki, companin baban na shi, kode daman Alh Ibrahim ba babansa bane. Me yake nufi da ze ruguza company? Anya umar bashi da tabin hankali kuwa. Mene a tsakanin shi da Alh ibrahim? Tunani ne barkatai tayi su a sakwanni da basu wuce 20 ba.

"Me kike yi a nan"
Ya fada tare da hade rai

"Me kaka shirin yi de"
Ta maida masa tun kafin a ya ajye numfashi.

"this is my business, babu ruwanki a ciki. This is my plan all along and you will do nothing about it.

Ya kare hade rai tare da takowa da sauri ze nufi kofa. Cikin zafin nama tayi wuff ta sha gaban sa tare da bude hannayen ta, ta tare shi akan baze wuce ba

"Move!!!!"
Ya fada da karfi

🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Bintu. A
09034346763

SarkakiyaWhere stories live. Discover now