Babymorry

174 8 0
                                    

🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Da kyar ta iya tashi washe gari, duk jikin ta ciwo yake. Da ta san abun akwai wahala baza ta taba yarda ba duk da umar a hankali yayi mata da lallashi da laluma har aka gama. Da asuba yayi steaming bathroom din yadda zata ji dadin wanka. Ya nannado ta cikin bedsheet ya kawo ta toilet, khairi ta kasa hada ido da shi da Matsanaicin kunyar sa take ji. Ta shiga toilet tayi wanka sannan ta fito ta shirya tayi sallah asuba.

Shima umar dakin sa ya koma yayi wanka ya kintsa sannan yayi sallah. Yana idar wa ya koma dakin khairi ya tarar da ita ta shige cikin bargo ta lulluba har kai, yayi yai ya bude bargon amma khairi ta ki ta nannade jikinta gaba daya da bargon.

Umar ya kyaleta tare da fadin
"To ni na tafi daki na, daman nazo na gaishe ki ne tunda bakya so bari na koma daki na"
Daga nan ya nufi hanyar waje.

bayan mintuna kadan da khairi ta tabbatar ta dena jin motsin sa ta bude bargon a hankali tana leke, tana gama budewa su kayi ido hudu da umar da ke labe a jikin bango, Khairi ta saki wani kara tana dariya tare da maida kanta cikin bargon, ta kara dunkunkune fuskarta cikin pillow

Ba abun da umar yake se dariya har da kyakyatawa.
Umar ya karasa bakin gadon ya dauko ta cak daga ita har bargon har pillow, Abun ka da abu kamar a hure

Khairi ta fara shure shure da kafa cikin shagwaba tace
"Ni ka ajye ni"

Umar yana dariya yana fadin
"Lets bless the other room"

Ba shiri khairi ta bude fuskar ta tare da zaro ido
"What do you mean?"

"Marital bliss"
Umar ya fada tare da kashe mata ido

Khairi ta fara kukan shagwaba shi kuwa umar se dariya yake har ya kaita dakin sa ya ajye ta a gado. Daga nan aka dorawa daga inda aka tsaya a karatun jiya.
A wannan round dinne khairi ta dan fuskanci abun da akeyi compared to na jiya da romance din kawai ta gane da aka shiga deep deep se ta dena fuskanta komai se wuyar da ta ji.
Amma na yau ba laifi har ta iya fuskantar me akayi. Bacci me nauyi ne ya dauke su su biyun bayan sun gaba dabbaka sunnah

Tun daga wannan ranar rayuwar su ta koma ta cikakkun ma'aurata masu so da kaunar junan su. Sun shayar da zuma da madarar kauna ma junan su. Akwai abu daya da khairi ta lura shine umar baya taba yarda yayi shuka, daga abun yazo yake fitar da shi waje, Ta rasa me yasa yake hakan. a tunanin ta ko baya so su samu karuwa da wuri ne. Itama abun be dame ta ba saboda bata shirya wa haihuwa yanzu ba. haka suka ci gaba da rayuwa cikin nishadi da soyyayya.

Se yanzu ta kara tabbatar wa tana son umar tun fil azal, se yanzu ta tabbatar zuciya bata da kashi and the matter of the heart is very complicated. Zuciya zata iya son mutum fiye da daya kuma ta ajye su a ciki ba tare da conflict ba. shiyasa har namiji yake iya auren mata fiye da daya. biyu, uku har hudu, kuma dukkan su samu guri na musamman a cikin zuciyar sa.

A haka har sukayi wata 5 cikin zallan soyyaya da kaunar juna.

🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
A bangaren su maryam kuma soyayyar Abdulkareem tana dada ginuwa a cikin zuciyar ta, duk wannan surutun da shirmen ta rage su. Idan ma yana gari wani nutsuwa da hankali ne yake shigar ta. Duk abun da aka ce na Abdulkareem ne tana ririta shi. Idan ze dawo ita take shiga ta kalkale masa daki da toilet har ta balbala turaren wuta a ciki. Abincin ranar ma ita zata dafa, har koyo recipes take don ta girka masa
ranar da ze dawo kuma ta shalla kwalliya idan hajja ta tambaye ta ko zata fita ne se tace kwalliyar juma'a tayi tunda duk ranar friday yake dawowa.

Se de hajja tayi murmushi saboda ta gane duk take taken ta, abun yayi mata dadi sosai. Fatan ta shine Abdulkareem ya so ta shima tunda ita ma maryam din ba baya bace, ga kyau ga diri ga yarinta haske kawai khairi zata nuna mata saboda maryam chocolate ce.

SarkakiyaWhere stories live. Discover now