Fire🔥🔥

152 7 0
                                    

🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Tun bayan rashin lafiyar da tayi ta fara sakewa a gidan, Yanzu bata kulle kofar tunda taga shima umar consummating auren ba a gaban shi yake ba shiyasa ta saki jiki. Sai dai A ko da yaushe cikin tunanin Abdulkareem take, kamar ta tafi ta same shi a duk inda yake tayi mishi bayanin ba lefin ta bane.

Guiltiness se hunting dinta yake, gashi se tai ta mugayen mafarkai a kan shi saboda tasa abun a ranta. Wani lokaci taga Ak yazo mata duk a rikice yana shake wuyanta yana cewa meyasa tayi mishi haka har se ta razana ta tashi daga baccin. Mafarkai de na tashin hankali haka takeyi.

Yau gaba daya bata fita parlour ba ma taji shigowar bashariyya amma bata leka ba har ta gama gyara gyaren ta tayi musu breakfast. Ta kawo wa khairi nata sannan ta ajyewa umar nashi a kan table. Daman haka suka saba yi a gidan, da yawan lokaci ma umar ba cin abincin yake ba

Khairi tana kwance a rigingine ta janyo wayarta da tafi sati biyu a kashe ta kunna. Tana kunnawa taga messages rututu a wayar duk masu tambayar da gaske anyi auren ta?, ba wadannan bane damuwar ta dan Messages din Ak kawai take nema, Ay kuwa ta gan su rututu, tun na daren kafin ranar auren ta da ya kira be same ta ba, Messages din ranar masu nuna soyayya da missing dinta da yayi lokacin da be same ta a waya ba.

Daga nan kuma babu abun da ya dinga turawa se kalma daya
"WHy?"

Taga "why" ya fi sau 100, don a rana ma se ya tura mata why sau biyar ko shida at different times.
Kuka ta dinga yi sosai har se da idon ta ya kumbura, se da tayi me isar ta sannan tayi dailing number sa.
Wayar tayi ta ringing ba'a daga ba, ta kira ya kai sau 10 baa daga ba har ta gaji da kiran.

Wani tunani ya fado mata ta kira number intisar
Se da Wayar ta kusa tsinkewa sannan intisar ta daga, tayi sallama murya ciki ciki Suka gaisa intisar de bata wani sake jiki ba
"Ya akayi? Me yasa kike nema na yau"
Intisar ta fada a dakule

Khairi da muryar kuka tace
"Dan Allah intisar tambayar ki zanyi, nasan akwai maganar da ya kamata mu fara yi amma wannan tambayar is urgent, zanyi miki bayanin komai"

"Ina jin ki"

"Yauwa dan Allah tambayar ki zanyi oga Ak yana zuwa aiki kuwa?

Intisar ta bushe da wata dariyar takaici sannan tace
"Amma ummulkhair kin ban mamaki, nayi tunanin kin dauke ni a matsayin kawa ashe duk shirme na ne. A tunani na ba za kiyi aure ba tare da kin sanar da ni ba, auren ma da MD, haba khairi ko kina tunanin zan miki bakin ciki ne. Se yanzu saboda damuwar ki ce zaki neme ni?"

Khairi ta kara matse hawayen da suka zubo mata sannan tace
"Wlh Intisar na san bani da kalaman da zan wanke kai na a wajen ki. Sannan ba lallai idan na baki labarin abubuwan da suka faru da ni a cikin kwanakin nan ki yarda ba. Na shiga wani irin sarkakiyar rayuwa da ubangiji ne ze fitar dani daga damuwar da nake ciki"

Khairi ta bawa intisar labarin komai daga yadda umar a dare daya ya zama cousin din ta, yadda suka kusa yin aure da oga Ak da yadda alamari ya juya aka aura mata umar"

Intisar se da ta zubda hawaye itama, lallai yanzu ta gane komai, da haushin khairi take ji yanzu kuma da taji abun da ya faru se ta tausaya mata. Hakika kaddara wani abu ne da bawa be isa ya kawar da shi tabbas matar mutum kabarin sa.

Bayan intisar ta gama jajanta mata khairi ta sake dawo da tambayar da tayi ma intisar da farko
Intisar tace
"Gaskiya oga Ak be dawo aiki ba, be dauki excuse ba ma. kuma a yadda naji labari idan an kira wayar sa baya picking, ga pending ayyuka da yawa da ya kamata yazo ya karasa"

Hawaye ya kara bin kuncin khairi.
"Ban san ya zanyi da guiltiness din da ke ci na a rai ba, i have caused this. Ban san da wani baki zan roki Abdulkareem gafara ba, sannan to top it up ban san ta yaya zan cire soyayyar sa da tayi min katutu a cikin zuciya ba. Ina jin son sa like molten magma gushing out from my heart. Wallahi intisar bazan taba dena son Abdulkareem ba har karshen rayu......

Kafin ta karasa magana taji an janyo kafar ta da karfi wanda yasa ta gangaro daga kan gadon zuwa kasa, tana juyowa taga umar se huci yake. Idanun sa sunyi jawur, matsanaicin bacin rai ta gani kwance a fuskar sa.
Nan da nan gaban ta ya dinga faduwa ta fara innalillahi wa inna ilaihi rajiun a cikin zuciyar ta.

Yasa hannu biyu ya dago ta tsaye yana girgiza ta kamar ze balla ta.
"Me yasa kika tsane ni haka? Why khairi ?why?"

"WHY" kalmar da kowa yake tambayar ta da shi kenan. Why din da ta rasa answer da zata basu daga umar har Abdulkareem din. Itama tana da WHY dinnan da ya kamata ta tambaya fa

Umar ya tura ta har ta kai bango sannan ya sa hannu ya riko kugun ta, ya tsura mata ido cike da sadness maganganun da ta fada se dawo masa kunne suke.
Ya kula da yadda idanun ta suka kumbura fuskar tayi jawur alaman kukan da ta sha. Haka take son Abdulkareem? He is dying to see a glimpse of love a idon ta amma be gani ba, why is it someone else ba shi ba. Me yasa baza ta so shi ba?

Shi kan sa hawaye ne a idon sa. Cikin daskararriyar murya yace
"Meyasa ummulkhair"
Ya fada da murya kasa kasa kamar me rada, alamun gajiya da sadness.

Cikin kuka tace
"Meyasa ka aure ni nima bayan kasan ba sonka nake ba, auren ka tashin hakali ya zame min, my life will never be thesame bayan forcing dina da kukayi akan auren nan"

Tana kaiwa full stop taji mutum ya rufe lips dinta da kiss, hot deep kiss that nearly made her breathless. Da kyar ta iya ture shi dan ta samu ta shaki iska.
Ta saka hannayen ta biyu ta rufe bakin ta da shi tana girgiza kai.

Umar yayi magana da husky voice
"I am your husband!! baze yu kina matsayi matata kina maganar wani katon a waje ba. Bari na nuna miki ni mijin ki ne kuma nine nake da hakkin ki so ni"

Yana gama fadin haka ya sunkuce ta ya jefa akan gadon sannan ya bi baya ya rufe ta,
Khairi na kuka tana rokan shi amma be ji ta ba, ya ware hannayen ta biyu ya danne da nashi hannun,
Khairi ta ci gaba da shure shure duk a banza wai an mintsini kakkausa, baza ta iya hada karfin ta da nashi ba.

Haka ya kara kissing dinta roughly , irin kiss me mantar wa mutum komai a duniya, se da ya kusa minti biyar yana abu daya.
Ta damtse idanun ta gam, tun tana shure shure har ta gaji ta saduda ta zubawa sarautar Allah ido. Jikin ta har ciwo ya fara yo sabode damben da tayi akan ya sake ta

A hakali umar ya saki lips dinta bayan ya gama sweetly torturing her with senseless kiss ya dago ya kalli kyayyawar fuskar ta. dukkan baccin rai da yake ji ya rasa shi a kankanin lokaci, She is damn too pretty, lips dinta har ya kara pink ya zama puffy saboda matsar da ya sha.

Har a lokacin bata bude idanun ta ba, bata son kallon shi kwata kwata. A hankali shima ya tashi daga rumfar da yayi mata tare da fadin
"This is your punishment"
Daga haka ya nufi hanyar fita daga dakin

Khairi ta kasa motsi, ta kasa bude idon ta ma gaba daya se da taji ya bar dakin.
Tana jin fitar sa ta tashi da gudu tayi toilet, ko da ta isa toilet mudubi ta duba saboda a tunanin ta ya ji mata ciwo a lips ma. Babu ciwo amma lips din sun kumbura, ta ma kasa yin kukan saboda takaici Se daga baya ta bude shower tayi wanka.

Bayan ta gama wanka ta shirya sannan ta kwallawa bashariyya kira, bashariyya ta zo da sauri, khairi ta roke ta da Allah ta kwana a gidan yau saboda tsoro take ji. tayi ma bashariyya karyar wai tana jin kamar ana tafiya a dakin da cikin dare,
Bashariyya ta zare ido
"Kai aunty😳😳, wlh nima ina jin tsoro sosai. Tafiya fa kika ce kina ji a dakin. To ki ce yallabai ya taya ki kwana mana"

Khairi ta galla mata uwar harara wanda yasa bashariyya ta gane kwafsin da tayi.

"Ba abun da ze faru zamuyi addu'a ay, bari na kira mamakin na fada mata zaki kwana a nan"

Bashariyya bata so haka ba dan ba yadda zatayi ne.
Ranar throughout khairi bata fito parlour ba har dare.

Tare da bashariya suka kwana a kan gado saboda tana tsoron kar umar ya sake dawowa dakin.
Ta dade batayi bacci ba tana ta tunani, abun mamakin shine ta kasa cire hannun ta a kan lips din, se shafawa take tana tuno abun da ya faru tsakanin su. Wannan ne kiss dinta na farko a duniya, kiss daga mijin da take ikirarin bata so. A lokacin da abun ya faru baza ta iya cewa taji wani abu ba saboda a tsorace take amma yanzu da take tunowa se ta kasa gane yanayin da ta shiga

Shi kuwa gogan ku se juyi yake a kan gado, guy was on fire 🔥 dan ya shiga cikin wani yanayi , Yana ta tuno lallausan pink lips din ta da yasa ya kusa fita a hayyacin sa.

🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Bintu. A
09034346763

SarkakiyaWhere stories live. Discover now