🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Abdulkareem yayi ta sintiri a reception yana jiran fitowar khairi daga office dinsu amma shiru Se kawarta intisar da ke kai kawo ita kadai, da yawan lokaci yana ganin su tare. intisar tana kara fitowa Ak ya tare ta, suka gaisa sannan ya tambayeta ummulkhair"An canza mata office "
Intisar ta sanar da shi"An chanza mata office zuwa ina kuma"
Ak ya kara tambaya"An sata a matsayin secretary ta MD"
"Secretary?? MD???"
Ji yayi kamar an daura masa dutse a kai, me ze hada ummulkhair da umar. A wani dalili zaa bashi ita, umar din da duk secretary dinsa se da suka sha wahala a gurin sa. Innaaaa baze yu ba.Da sauri ya haura sama har yana yin tuntube. Yana isa office din ummulkhair ya ja ya tsaya ya kasa kwankwasa kofar. Idan ya shiga me ze ce mata
Se dayayi kamar minti 5 shi be shiga ba shi be tafi ba. Yana tsayen messenger ya tadda shi a bakin kofar office din, ya gashe shi sannan Ak ya tambayi messenger
"Aiko ka akayi?"
"Eh madam jidda ce tace na fadawa madam din office dinnan nan da minti 10 zasuyi meeting din"
Messenger ya fada masa"Nima zan shiga ne, je ka kawai zan fada mata"
Ak ya fada masa sannan ya fara kwankwasa kofar a hankali. Yayi murnar haduwa da massenger ko ba komai ya samu excuse din shiga office dinDaya ji ba'ayi magana ba kuma ba'a bude ba zuciyarsa ta fara raya masa munanen abubuwa, yasan halin umar yanzu haka yana nan yana muzguna mata. Beyi wani tunani me zurfi ba ya murda handle din kofar ya shiga a hankali
Yana shiga ya ganta a kan sofa tasa hannun ta tallafo kuncin ta kamar me tagumi amma ba tagumi take ba bacci ne ya kwashe ta.
A hankali cikin sanda Ak ya karaso inda take, be san lokacin da ya fara murmushi ba. Ya nade hannun sa a kirji ya jingina da bango yana aikin kallon ta ita kuwa Bacci takeyi hankalinta a kwance. Ya fi minti biyar a haka daga baya kuma ya tsuguna a gabanta yadda ze dinga hango fuskarta da kyau Yana jin sonta ta shiga har cikin bargon jikin sa.
🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Jidda ta gaji da jiran khairi gashi lokacin da zasu hadu da Alh ibrahim yayi bata ganta ba, shiyasa ta aika mata da wuri saboda kar a samu delay.
Messenger da ta aika ne ya shigo da tarkacen folders a hannun sa."Yauwa baba isiya ka fada ma ummulkhair sakon da nace"
Jidda ta tambayi messenger"Eh to....na tarar da oga Abdulkareem a bakin office din ze shiga , shine yace ze fada mata"
"Abdulkareem???"
Jidda ta fada da karfi yayin da tayi zumbur ta mike."Me yasa baka fada min ba tun tuni"
Ta fada da masifa muryar ta a sama"Naga.....,"
Kafin baba isiya ya karasa magana jidda ta fice fuuuu daga office din.Tana zuwa office din khairi ta bude shi da karfi ba tare da ta kwankwasa ba tana wani irin haki, idon ta yayi ja, zuciyarta kamar zata fashe saboda bakin ciki.
Wannan budewa da karfin da tayi ne yasa Ak saurin tashi daga tsugunnan dayake, ya shagaltu da kallon khairi har yaji kamar babu kowa a duniyar daga shi se ita, karar bude kofar da jidda tayi ne ya dawo da shi daga duniyar soyayyar da ya fada.
"Me kakeyi a nan????
Jidda ta fada da mamaki cike a fuskar ta,
A wannan lokacin ne khairi ta tashi saboda maganar da jidda tayi, tana bude ido taga Ak a tsaye a kusa da ita jidda kuma a bakin kofa ta rike handle din kofar. Cikin confusions khairi ta mike tsaye"Lafiya??"
Ta tambaya da idon bacci, baccin be sake ta ba. Bata san ya akayi ta fara baccin ba ma yayin da take jiran jidda ta kira ta. Ko dayake sanyin Ac ma kadai ya isa ya sa mutum bacci.Abdulkareem ya rude ya rasa wa ze bawa answer, da sauri ya wayen ce
"Nazo ganin MD ne"
Jidda de tasan kawai ya fada ne, don me ma yake hada Ak da umar da har ze zo office dinshi takanas. Se de ya rainawa khairi hankali ba de ita ba.Jidda ta juya kallonta zuwa ga khairi
"Baki samu sako na bane, na turo ace miki ki shirya meeting da CEO"
Jidda cikin confusion tace
"Ni???, ba wanda ya fada min"Abdulkareem yayi murmushi ganin yadda tayi maganar gwanin sha'awa, yar cute da ita. Sannan yace
"To ay bacci kike yi shiyasa""Kuyi hakuri, bacci ne ya kama ni ban sani ba"
Khairi ta fada tana murza idoJidda da ke tsaye ji tayi kamar ta harbe khairi saboda takaici.
Suna cikin wannan yanayin ne umar ya bude kofar da ta hada office dinsa da na khairi, yahaniyar da yake ji ta fara yawa.Kallan kallo aka fara yi a cikin office din, duk suka kasa magana daga karshe umar ne yayi magana
"Wow wow, what a surprise.To whom did i owe this pleasure, naga kamar ana meeting ne a office dina"
Yayi maganar da gatseShi de ya san Se ayi wata guda babu wanda ya doshi hanyar office dinsa amma a ranar farko da khair ta zo office din mutane sun biyo ta.
Babu wanda ya bashi answer se jidda da ta ce wa khairi
"Malama mu tafi"Umar yayi charab yace
"Kuje ina, i want her here, what is even your name "
Ya kalli khairi yana daga gira"Ummulkhair"
Ta fada a hankali"Ummu whatever you call yourself i need you here, ku kuma zaku iya tafiya"
"She is coming with us"
Abdulkareem ya fada yana kallon umar ido cikin ido, ya hade girar sama da kasa.Jidda ta ga Abu karami yana son komawa babba dole ta shafawa abun ruwan sanyi, duk da itama ranta a bace yake. dadin dadawa tasan ogan ta jiran khair yake yana son suyi magana. Duk wani delay da zaa kara samu ze janyo mata matsala.
"Afwan sir, akwai abunda zatayi ne. It won't take long Zata dawo nan ba da dadewa ba.
Khairi da ake wannan abun a kanta kallo kawai take bin kowa, babu wanda yake ta ita ma.
Jidda ta ja hannun ta suka fito daga office din tare🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Bintu. A
09034346763
YOU ARE READING
Sarkakiya
RomanceLabarin tsantsar soyayya me cike da sarkakiya ce ta kullu a tsakanin su. Ummulkhair ta zamo Allura cikin ruwa wanda me rabo ne ze dauka. Shin wa zata zaba a cikin su? Boyayyen masoyi Abdulkareem wanda yayi dakon soyayyar ta na tsahon lokaci ko kuma...