Birthday

183 12 0
                                    

🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Knock .....knock .......
yaji ana kwankwasa kofar office dinsa, ko baa fada ba yasan wacece.
"Come in" yace a takaice
Jidda ta shigo da murmushi hannun ta rike da jaka. ta gaishe shi shima ya amsa da sakin fuska.

"Na tura maka link din ta email dinka" ta fada tana wasa da hannun ta

"Okay ban kula ba, bari na duba"
ya fada yana kokarin bude lap top dinsa. Ya bude yayi dan dube duben sa sannan yace

"Yes na ganshi, thank you jidda"

Tayi murmushi "anything for you sir"

Ta sa hannu a cikin jaka sannan ta fito da wani karamin box. zatayi magana kenan wayar sa tayi kara, se ta dakata ya gama abunda yakeyi sannan tayi magana

Da sauri ya bude wayar saboda sunnan cherry da ya gani. Yau shine message na biyu da ta taba yi mishi. Yayi mamakin ganin text dinta ya shigo.

" stop playing with my head, I know who you are. Just come clean malam jabir"
(Ka dena wasa da hankali na, nasan wanene kai. Ka fito fili kawai malam jabir)

Message din da yaga ta turo kenan

Kan shi ne ya daure da message dinta, fuskarsa cike da mamaki. waye kuma malam jabir, meyasa zata ce masa malam jabir. Ko wani malamin ne ke son ta a makarantar
Tambayar da yayi ma kansa kenan

Bayan yan mintuna ya tuno da karyar da yayi ma yarinyar da ta bashi number. Shi har ya manta yace mata malamin makarantar su ne.
Dariya me karfi ce ta kufce masa, ya fara yinta ba kaukautawa. Shi kam yarainyar tana bashi dariya.

Jidda da ke tsaye a bakin kofa bude baki  tayi saboda bata taba ganin yana dariya haka ba. Shiru tayi ta tsaya kallon sa, dariyar ta kara masa kyau. Fararen hakoransa sun fito, bata san lokacin da ta fara murmushi ba itama.

Se da taga ya tsagaita da dariyar ya tsurawa wayar ido yana murmushi a sanyaye sannan tayi masa magana

"Happy birthday sir"
ta fada tare da miko masa box wanda cake ne a ciki

Ya dago yana kallonta da murmushin a fuskar sa
" ya akayi kika san yau ne birthday na"

"Na gani ne a profile dinka" ta fada tana soso jirar ta irin na jin kunyan nan.

"I don't celebrate birthdays, amma nagode kwarai da gaske, yau nima na zama birthday boy"

Dariya tayi sannan ta matso kusa da table din ta ajye cake din. Ta juya da sauri ta bar office din saboda kunya.

Tana fita ya maida idonsa kan message din khairi ta turo ya ci gaba da murmushi ko kula cake din beyi ba 💔💔💔
🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒

Yau gaba daya bata jin dadin jikinta , abinda malam jabir yake mata a tuananin ta beyi mata adalci ba. Be kamata yayi mata wasa da hankali haka ba. Gwara ma da tayi mishi message din Ya gane cewar ta san shine yake mata messages dinnan.

Tana tsaye a bakin gate bayan an tashi daga makaranta taga mallam jabir yana janyo machine dinsa yana fitowa da shi daga makarantar. Kura mata ido yayi itama ta kura masa nata dara daran idon.
Ya matso inda take sannan yayi mata murmushi sanna yace mata

"Barka da rana malama Ummulkhairi"

"Barka de malam jabir" ta amsa masa tare da hade rai

"Tafiya zakiyi ne" ya tambaya
'Aa zama zanyi' abinda ta fada a ranta amma a zahiri se tace

"Eh tafiya zan yi"

" a ina kike naji ko hanyar mu daya na rage miki hanya"

Lallai ta tabbatar mal jabir dan rainin hankali ne. Mutumin da har gidan su yaje ya karbi number ta shine yake tambayar ta a wani unguwa take.

" ba ka san gidan namu bane?"
Ta tambaya tare da yi masa kallon tuhuma.

"Aa, a ina zan san gidanku malama ummu" ya fada tare da yin dariya

" shikenan, tunda kace haka, kaje kawai zan samu abun hawa"

Ba musu ya tada machine dinsa yayi gaba. Ya barta a tsaye cike da mamakin yanda yayi kamar be san komai ba. Kuma tayi tunanin zeyi mata bayani bayan message din da ta tura masa amman be ce komai ba, yi yayi kamar basan tayi ba.
Ta bi shi da harara se da taga ya kule sannan ta nima abun hawa ta nufi gida.

Tana isa gida ta tarar da su inna asabe ana ta kai kawo ana hada kayan tafiya kano don gobe da sassafe zasu wuce. Ta shiga daki ta dauko wata leda ta  kowowa inna ta sa a cikin kayanta tana so a kaiwa umman ta tsaraba.

"Inna ga wannan dan Allah a kaiwa umma na"
ta fada tare da mika mata ledar

Da masifa inna tace
"Har kin iya yi ma uwarki tsaraba, amman da zan tambayeki kudi se ki ce baki da shi. An de yi gadon bakin hali"

Khairi da ke tsaye takaici ne ya kamata, tana hakuri da bakaken magana da ake yaba mata a kullum amma fa turar ta fara kaiwa bango. Allah Allah takeyi ta gama service dinnan ta koma gida ko ta huta da masifar yan gidan

Inna asabe ta wafci ledar sannan ta bude, turarruka ne da takalmi a ciki. Ta kyabe baki sannan ta tura ledar cikin akwatin ta

"Yau zaki tafi gidan saadatun, don gobe bayan asuba zamu tafi. Kuma ina son kulle gidana kafin mu tafi"

To kawai ta ce mata sannan ta wuce daki.

A ranta tana cewa 'Yanzu zasu je kano su fara yi ma mutane fafar daga Abuja suke. Ita kam da wannan abujar gwara a ce a dambatta take'

🍒🍒🍒🍒🍒
Bintu. A

SarkakiyaWhere stories live. Discover now