🍒🍒🍒🍒🍒🍒
"Farida na rasa yadda zanyi na shanyo hankalin sa, duk abun da kika ce nayi na yi su duka amma be san ina yi ba"Jidda ta fada tare da sauke ajiyar zuciya sannan ta tsurawa computer da ke gaban ta ido tana sauraron abunda kawar ta take fada a waya.
"Ba kya jin shawara ai, na fada miki akwai hanyoyi da yawa amma taurin kai baze bar ki ba"
Farida ta fada da masifa a muryar ta"Yaya kike so nayi farida, ni de duk hanyar da za'a kauce daga tauhidi bana so"
Jidda ta fada har da hade rai kamar faridar tana gaban ta"Wa ya fada miki kaucewa za'ayi, kawai taimako ne za'a baki wanda ze janyo hankalin sa. Ba ze wuce dan turare da kwalli da mallam ze baki kiyi amfani da shi, shikenan fa"
Jidda ta girgiza kai sannan tayi murmushi
"Aa gaskiya bana son wannan taimakon, bana so na sabi ubangiji na akan rayuwar duniya sannan nafi son ya so ni a ni din ba tare da influence na wani tsibbu ba"Ran farida ya fara baci cikin hasala ta maida mata
" ke fa banza ce, ni ki daina kawo min matsalar ki tunda baza ki dauki shawara ba, mutane nawa ne sukayi aure ta sanadiyar hakan kuma suna nan suna zaman lafiya a gidajen su"Jidda tayi sauri ta katse ta
"Haka suka fada miki, kin san yadda suke zaune ne?
Ni dan Allah mu bar wannan maganar, ki bani wata shawarar kawai"Farida tayi shiru tana tunanin me zata ce mata, bayan yan mintuna tace
"Yauwa ba kince se da wannan shegiyar yarinyar tazo office din hakalin sa ya koma kanta gaba daya ba? Mene ma sunan ta"Jidda ta ja dogon tsaki jin farida ta ambaci khairi, ranta a bace tace
"Me ya kawo maganar ta kuma"Farida ta kara hasala
"Wai ke meyasa banza ce, kina tunanin idan yarinyar tana office dinnan ze iya ganin wata mace bayan ita? Ai ita ce babbar matsalar ki, kokari zakiyi ki fattatake ta daga office din."Kuma fa haka ne, me yasa banyi tunanin haka ba tun farko"
Jidda ta fada tana nanata abun a zuciyar ta"Oho miki kuma, daman ke duk abun da ya kamata kiyi ba yi kike ba se aikin kwalliya, an fada miki kwalliyar ki ce kawai zata janyo hankalin sa"
"To amma munyi magana da MD akan zamu kikrkira plan din da zamu raba su. Na bakin labarin ay"
Jidda ta fada ma kawar tataFarida ta ja dogon tsaki sannan tace
"Ke se ki zauna zaman jiran shi, ni wlh kina bani haushi idan kina irin maganar nan, zauna jira ruwa kwado yayi miki kafa""Aa na yarda da maganar MD, kin ma tuna min yanzu zan je na same shi muyi magana"
Ran farida a bace tace
"Ni ki rabu da ni dan bata min rai kike yi wlh, se anjima kawai"Jidda tayi dariya tana tsokanar ta
"Haba kawalliya kar ki fushi mana, kar ki damu duk yadda mukayi zan kira na fada miki"Jidda tayi sallama da kawarta sannan ta tashi ta nufi office din umar. Da sallama ta shiga bayan ya bata izni, ta samu guri ta zauna sannan ta gaishe shi.
A dakire ya amsa sannan yace mata
"Me ya kawo ki"Jidda tayi murmushi ganin mulkin nasa ya motsa sannan tace
"Kai ma kasan abun da ze kawo ni""To ya akayi"
Ya tambaya kamar be san me take nufi ba"Munyi magana da kai akan plan din da zamu ruguza oga AK da waccen yarinyar"
Ta fada harda yar masifar ta"Ummulkhair sunan ta ba waccen yarinyar ba"
Umar ya maida mata tare da daure fuska"To naji, amma munyi magana da kai kuma naji shiru shiyasa nazo takanas"
Ummar yayi ajiyar zuciya sannan yace
"Jidda mu bar wani maganar plan yanzu har se na shanyo hankalin ta tukunna"Jidda ta Wangale baki tana mamaki yadda ze chanza baki, mutumin da rumi rumi sukayi da ita don su samu abun da suke so.
Maganar sa ce ta katse mata tunani"Ke ma shawarar da zan baki shine kiyi kokarin shanyo hankalin wanda kike so daga baya se mu san abun yi"
"Hmm"
Jidda tayi ajiyar zuciya saboda ta rasa abun cewa, dole ta bi shawarar kawar ta tun da umar yayi crushing karamin hope dinta.
Jiki babu kwari ta bar masa office din ba tare da ta kara magana ba.
🍒🍒🍒🍒🍒🍒Yau da wuri khairi ta bar wajen aiki bayan wasan buya da ta dinga yi da umar, tana jin alamar shigowar sa take ficewa, se taje office din su intisar ta sha hira sannan ta dawo, ko tsoron umar ma batayi.
Zancen tsoro ya kare tunda ya kuskura ya furta yana sonta sede tayi shayin sa.Yau a gajiye ta dawo daga aiki, me taxi ya sauke ta a daidai kofar estate dinsu, tun tana cikin motar take ganin kamar wata motar na binsu a baya, da ta lura da kyau se taga umar ne a cikin motar,
Kamar da wasa ta ga ya soka kan motar alaman ze shiga gidan maimakon yayi parking a waje
Umar yayi horn a gate din estate dinsu, me gadi na rawar jiki ya bude masa harda washe baki yana gaishe shi kamar daman ya san shi.
Khairi ta wangale baki tana mamakin wani mukami ne yasa ze biyo ta har cikin estate dinsuCikin fushi ta shigo gidan me gadi na gaishe ta amma bata bi ta kansa ba ta karasa inda umar yayi parking mota.
"Lafiya na ganka a gidan mu"
Ta tambaye shi lokacin ya bude motar yana kokarin fitowa daga ciki.."Lafiya"
Ya bata ansa a gajarce sannan ya wuce fuu ya barta a tsaye.Da zafin nama ta bisa har ta cin masa
"Magana nake, ina zaka je ne"Be kula ta ba ya ci gaba da hawa benen da yakeyi Itama ta bishi da sauri har tana tuntube. Har suka kai 2nd floor inda gidan su yake suna abu daya, yana tafe tana binshi da tambayoyi wanda be bata ansar su ba.
Gadan gadan taga yayi hanyar gidansu wanda yasa da gudu ta sha gabansa har tana haki saboda gudun da tayi
"Me zakayi a gidan mu"
"Ki matsa na wuce"
Ya fada a sanyaye"Idan da ni kake son magana gani ay, ba se ka je gidan mu ba"
Ta fada murya na sarkewa saboda hakin da takeyi"Wa yace ke nake son gani, ki matsa ina so na shiga gida na"
Ya fada yana nuna mata kofar apartment din da ke kallon nasu"Gidan ka????"
Ta fada tare da zare idanu dan ta kasa fahimtar maganar maDariya yayi sosai ganin yadda mamaki ya bayyana a fuskar ta karara. A ko wani lokaci kyau take masa, ko yaya tayi da fuskarta burge shi yake.
Ya godewa Allah da yasa ya samu hayan apartment din da ke kusa da nasu don se da ya shiga ya fita a yan kwanakin nan sannan aka bashi hayar apartment din da kyar.Apartment din na wani yaron senator da ba zama yake a gidan ba, kwai gidan ne na shakatawar sa. Se ya shekara biyu be zo gidan ba. Makudan kudi umar ya biya sannan yaron senator ya ba shi hayan gidan na wata 6. Akwai komai na gida a cikin gidan.
"Lets see how you can avoid me"
Ya fada yana kallon cikin kwayar idonta. Daga karshe ya rabe ta jikin ta ya wuce apartment dinsa,
Ya bude ya shige ya barta a tsaye fuska cike da tsananin mamaki🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Bintu. A
09034346763
YOU ARE READING
Sarkakiya
RomanceLabarin tsantsar soyayya me cike da sarkakiya ce ta kullu a tsakanin su. Ummulkhair ta zamo Allura cikin ruwa wanda me rabo ne ze dauka. Shin wa zata zaba a cikin su? Boyayyen masoyi Abdulkareem wanda yayi dakon soyayyar ta na tsahon lokaci ko kuma...