🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Cikin kuka khairi ta gama bawa Abdulkareem labarin abun da ya faru tun daga farko, tun daga lokacin aniversary har yau da take kulle a office din ss.Kwakwalwar sa ta kasa processing information din, kansa ya kulle gaba daya, kar ma ayi maganar tsananin bacin rai da takaici da ya sarke zuciyar sa. Ya rasa me ze ce se kuka da yakeyi shima.
Lokacin karfe 6 na yamma tayi, tun lokacin da officer nan yazo yayi mata tambayoyi bata sake ganin wani ya shigo ba balle ta san matsayar ta. Ta fada ma Aunty Maimuna ma a waya wadda cikin tashin hankali tazo office din ss, tayi da su su barta ta ga khairi suka hana se da ta kwashe awanni a wajen sannan ta koma gida don ta kawo mata abinci hankali duk a tashe.
Khairi da Ak sunyi kuka me isar su sannan suka zubawa juna ido ta video call, ji yakeyi kamar ya tsuntsu ya dawo nigeria. Tausayin ta yake ji matuka domin yasan a tsorace take gaba daya.
Ya ci gaba da lallashin khairi sannan daga baya sukayi sallama yace ze kira ta anjima.
Yana kashewa ya kira jidda video call. Jidda na gani kiransa gaban ta ya fadi, abun da take ta tsoro ne ze faru. Se da ya kira sau hudu bata daga ba daga baya de tayi picking.
Ko da ta ganshi a video fuskar nan a murtuke, gaban ta yayi ta faduwa ta kasa cewa uffan.
Abdulkareem ne yayi magana
"Na kira ki ne saboda ina son jin me ya faru"Jidda ta fara kame kame, tace wannan ta ce wancen duk surutun da takeyi Ak be gane komai a ciki ba, magana takeyi babu kan gado saboda rudewe
"Kin ga jidda just ko straight to the point, me ya faru yau da har ss suka tafi da khairi"
Jidda ta fara zubar da hawaye, yau ga masoyinta ya kira amma kiran ba na dadi bane kiran da baza ta taba fatan yayi mata irin shi ba, kiran titsiye, titsiyen ma itace me laifi. Wannan abun kunya da me yayi kama
Tana kukan take ce masa
"Kayi hakuri lefi na ne, nice ummul'aba'isin komai da ya faru, ni nayi abun da ban taba tunanin zanyi a duniya ba. Ka yafe min Oga Ak, ka yafe min""Me kikayi mata
Ak ya tambaya muryar sa a samaJidda ta bashi labarin yadda ta shiga office din khairi ta dauko flash ta kaiwa Alh ibrahim duk dan a kore ta daga aiki.
Mamaki ya kama Abdulkareem, me khairi ta tsare mata da zatayi mata wannan muguntar? jiddan da yake ganin hankalin ta. Shi har yanzu be gama yarda jidda ce zata iya wani abu makamancin wannan ba
.Cikin bacin rai yayi magana"You have disappointed me jidda, i never thought you will stoop this low. Me khairi ta tsare miki, me tayi miki haka da tsanani........... ki ansa min me tayi miki haka"
Jidda ta kara fashewa da kuka jin yadda Ak yake mata masifa, Tayi nadama sosai ta tsani kanta, duk saboda soyayyarsa da taso ta wulla ta ga halaka
"Duk saboda kai. Kai ne dalilin da yasa nayi hakan"
"Ni kuma?? Me hada ki da ni a wannan maganar"
Ak ya fada yana mamakin sharrin da take kokarin yi masa"baka taba noticing dina ba all these years that I've known you. Ko da wasa baka taba la'akari da feelings dina game da kai ba, duk a lokacin nan i have loved you amma baka taba kallo na a matsayin wadda zaka so ba. you've never looked at me twice.
Jidda ta sauke nauyayyen ajiyar zuciya sannan ta ci gaba
"A kullum ina addua da fatan zaka juyo ka kalle ni, kayi noticing son da nake maka amma bakayi ba.
Ya kake so nayi da wutar sonka da ke addabar zuciya ta. Wallahi Nayi nayi na cire ka amma na kasa, me kake so nayi"Jidda ta kara fashewa da kuka, abun da ta dade shekara da shekaru tana boyewa yau ta fito da shi, Bata taba tunanin akwai ranar da zata iya fada masa haka ba, idan ma zata fada not in a situation like this
Abdulkareem kam sankarewa yayi yana sauraron ta, ji yakeyi kamar a mafarki. Be taba yi ma jidda kallon so ba hasali ma ya sa ta a matsayin kanwar sa, dai dai da wasa be taba tunanin son ta ba tun kafin khairi ta zo company ma.
Be iya fadan komai ba se tausayi da ta bashi saboda yasan so, yasa abunda so ze iya sawa, so cuta ne da maganin sa se da taimakon Allah. Balle ita da take son maso wani, to some extent he can understand her amma haka baze bata damar tayi abun da tayi ba yanzuTaci kukan ta sannan ta katse video call din, bata san da wani ido zata kara iya kallon sa ba bayan yadda ta fayyace mada sirrin zuciyar ta, sirrin da ta dade tana boyewa.
🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Umar ya dawo office din ss bayan magrib, yayi da su su barshi ya ganta suka ki, Daga karshe se cewa yayi shine master mind din komai, Tare da kahiri sukayi komai dan haka a hada har da shi a rufe.
Officer ya rasa yadda zeyi da umar, ya kira Alh ibrahim ya sanar da shi abun da ke faruwa. Alh Ibrahim ya basu go ahead su hada da shi su rufe. Aka tattara umar aka tura a dakin da aka ajye khairi.
Shi kam Burin sa ya cika, daman ya kudiri niyan ba ze bari khairi ta kawana agurin ita kadai ba.Kafin a kulle shi ya hadu da Aunty maimuna a farfajiyar office din. ya kwantar mata da hankali sannan yace ta koma gida ze kula da khairi. Sannan ya tabbatar mata da idan Allah ya yarda gobe zaa sake ta. Aunty maimuna ta tafi gida tana matse hawaye zuciya cike alhinin abun da ya faru da khairi. Ta kasa fadawa kowa saboda kar hankalin su ya tashi
Aka shigar da umar dakin da khairi take wanda Khairi tayi mamakin ganin sa a wannan lokacin domin bayan magrib ne. Ta riga ta saduda a wajen zata kwana
"Me ya dawo da kai"
Ta fada murya a dashe saboda gajiya da tayi da kuka"Nazo na taya ki kwana ne"
Ya fada tare da neman gurin zama, ya zauna a kasa opposite da ita ya sa ta a gaba da kallo, a cikin awanni kadan har ta rame, tayi zuru zuru .🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Bintu. A
09034346763
YOU ARE READING
Sarkakiya
RomanceLabarin tsantsar soyayya me cike da sarkakiya ce ta kullu a tsakanin su. Ummulkhair ta zamo Allura cikin ruwa wanda me rabo ne ze dauka. Shin wa zata zaba a cikin su? Boyayyen masoyi Abdulkareem wanda yayi dakon soyayyar ta na tsahon lokaci ko kuma...