Malam Jabir

187 12 0
                                    

🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
"I want the list of vacancy we have in each department"
(Ina bukatar lis din gurbin maaikata da muke dasu a ko wani bangare)

Ya fada da tsawa sannan ya wurgo mata takardun da ke hannun sa.
Rabewa tayi a jikin bango a tsorace, ya ci gaba da
Yin masifa ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba.

Maryam itace secretary ta huda da umar yayi a zuwan sa office din, Duk ukun na baya basu iya zama da shi ba saboda masifar sa. Biyun ma barin aikin sukayi gaba daya. Dayar ce ma  aka chanzawa  aiki a company. Maryam dinma ta gaji da shi kiris take jira ta bar aikin gaba daya ma.

Masifar da yakeyi ne ya janyo hankalin jidda da office dinsu yake  kusa da juna.  Ta shigo da sauri  ta samu maryam a tsaye a jikin bango da takardu a barbaje a kasa. Ta kalli umar da ke zaune a kujera se huci yakeyi. Kallon banza ya watsa mata sannan yace mata

"I want you both out of my office"
(Ina son ku fita ku bar min office ku biyun)

Yana magana yana duba wani file a kan table dinsa.

Ok sir tace masa sannan ta kama hannun maryam suka fito daga office din.
Suna fitowa maryam ta fashe da kuka

"Jidda na gaji, na gaji da yadda yake treating dina. Ni secretary sa ce am not his slave. Zan kai kara human resource kawai"

"Maryam kin san abunda kike fada kuwa? Kina nufin zaki kai karar MD? To ki shirya resignation letter ki kawai. Maslaha shine zan miki kokari a maida ki wani department din. Kinga yanzu muna da karancin maaikata idan kika bar aiki gaba daya zamu kara samun short"

Jidda ta fada tana kokarin shanyo hankalinta kar ta yanke hukunci cikin fishi.

Suna saukowa daga bene suka hadu da AK ze hau sama, yadda ya gansu sunyi jugum jugum yasan akwai matsala.
Suka gaishe shi, ya amsa sannan ya tambaya abinda ya faru. Jidda ta fada mishi duk abunda ya faru.
Ranshi ne ya baci, wai shi umar dinnan me yake nufi ne. Yana mamakin yadda Alh ibrahim ya barshi yake yin abunda yaga dama tunda yasan Alh ibrahim din mutun ne me discipline.

Ya basu hakuri sannan yayi musu sallama ya wuce. Har yayi gaba sannan ya juyo yayi ma jidda magana da har yanzu kallonsa kawai takeyi. Tana kara jin matsayinsa yana karuwa a zuciyar ta.

"Naji kamar ana bukatar more staff ko?"

"Yes sir, zaayi hiring new staff soon" ta fada a takaice

"Slot nawa ne ake bukata"

"Ze kai 7 sir"

"Yaya zaayi hiring din"
ya kara tambaya, tare da tattaro gaba daya hankalinsa gareta.

"Zaa saka advert ne da link, wadanda sukayi applying zasu zo interview sannan ayi selecting wanda suka cancanta"
Ta yi masa bayani dalla dalla.

"Please idan an gama inason wani alfarma, ki turo min link din da zaayi applying"

"Okay sir"

"Thank you i really appreciate" ya fada yana murmushi sannan ya juya ya tafi.

Tasan cewar abinda ya sa tayi mishi ya sabawa tsarin aikin ta amma bazata taba hana shi wani abu da ze nema a wajen ta ba. Duk abunda yake so inde tana da iko akai zatayi mishi balle wannan abu da be taka kara ya karya ba. Murmushin da yayi mata ma ya isa ya narkar da zuciyar ta.
🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒

Tunda zainab ta fadawa khairi malamin makarantar su ne ya karbi numbar ta, ta sawa ko wani malami ido a makarantar musammam wadanda basu da aure. Mutane 3 take zargi a cikin malaman. Biyu basu da aiki se shishige mata. Su a lallai se sun nuna mata yadda akeyin aikin, ga son hira da tsokana. Wadannan ko a kafa aka daura mata baza ta ja su ba.

Se kuma dayan malam Jabir, shi kuma bashi da surutu sosai, Be cika yi mata magana ba ma. dan gaye ne gashi baza ka ce masa mumuna ba. Hankalin ta yafi karkata kan malam jabir dinne. Inde malam jabir ne bata san ma me zatayi ba, ita de baza ta ce zata iya kula shi ba Amma gaskiya da kyar ta so shi.

Yau ma haka sukayi clashing, tun daga nesa yake kallon ta amma har suka wuce juna be ce mata komai ba. Zargin ta ya fara tabbata, tana so ta kamo bakin zaren. Sannan ta kudure a ranta yau zaayi ta ta kare kawai. Ko shi ne ko ba shi bane

Ta fito da wayar ta a jaka,  tasan cewar zata ga messenge dinsa a wayarta. Tana budewa taga sakon sa

"Hi beautiful, just checking on you to know how you are doing, i hope the students are not giving you headache"

( hi me kyau, ina son sanin ya kike ne, da fatan daliban basa baki ciwon kai)

Dariyar tayi na takaici, lallai mal jabir ya raina mata hankali.

Cikin fushi ta rubuta masa reply sannan ta ajye wayar a jaka ta shiga class.

🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Bintu. A
09034346763

SarkakiyaWhere stories live. Discover now