Hutu

215 14 0
                                    

🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Rayuwarta khairi ta ci gaba da tafiya yadda ta fara a cikin gidan, babu abinda ya canza, daga san kudin inna asabe har rashin kunyar su farida, jira sukeyi ta shiga huriminsu suyi mata nasu rashin mutunci. Dayake khair ba me son hayaniya bace tana kokarin kiyaye duk abunda ze hada ta da su.

Saadatu ma cikin ta se kara girma yake, yanzu zama da kyar tashi da kyar, tana watan ta na tara haihuwa yau ko gobe. duk da halin da take ciki suna yawan samun sabani da mijin ta Alh Audu.

Yau juma'a, yau ne ranar da zasuyi hutu a makaranta, tana ta murna zata koma gida kano hutu. Idan ta dawo daga makaranta da wuri ma a yau din zata dau hanya. Ta gama hada kayan ta tsaf a jaka.

Ak ya riga da ya gama gane yanayin dawowar ta daga makaranta. Yasan cewa ranar juma'a da wuri ake tashi sannan ana tashi  take tafiya, da wuri ya shira ya tafi  saboda  kar ya maraka yazo be same ta ba.
Karfe 11:50 ce tayi mishi a kusa da gate din, me gadi yana ganin sa yazo suka gaisa. Daman duk sanda yazo se ya je sun gaisa, shi kansa abun daure masa kai yakeyi yadda yake zuwa ya shafe minti talatin wani lokacin awa daya yana jiran ta, kuma idan ta fito ba magana yake mata ba

Bayan sun gama gaisawa me gadi yake fada mishi yau zasuyi hutun makaranta, hutun kuma na wata guda domin hutun shiga sabon zangon karatu ne.
Nan da nan annurun fuskar sa ta dauke . Lalle wannan bakin labari ne, be taba tunanin zasu iya yin hutu ba ma a lissafin sa. Hutun ma har na sati 4.

Zuciyar sa ta saba da ganin ta, ta saba da tunanin ta be san ya rashin ganin nata ze masa illa ba. Yayi ajiyar zuciya sannan yace da me gadin.

"Ka samo min sunnan nata"

"Eh yallabai, sunan ta malama Ummulkhairi"

"Ummulkhairi, Ummulkhairi" 
uwar alkhairi kenan ya fada a ransa

Yaji dadin sunan ta da ya sani yanzu. Anyi wata da watanni be san sunan wadda yake so ba. Tabbas sha'anin so yana da bakar wahala. Ya juya ya kalli me gadin

"Yanzu abinda zakayi min shine ka samo min number ta dan Allah, yanzu ma de saka min taka number"

Ak Ya fada tare da miko masa wayar sa.

"A A yallabai bari de na baka waya ta se ka sa min number ka idan yaso se na kira ka ga tawan"

"Hakan ma yayi"
Ya karbi wayar me gadin ya saka masa numbar sa sannan ya daura

"Dan Allah kayi min wannan kokarin. Zan dinga kiran ka naji ko an samu number"

"Ba komai yallabai insha Allah zanyi kokari, kar ka damu"

Ak ya sa hannu a aljihu ya fito da dubu 10 ya bashi, se da me gadin yayi mamaki ba shiri ya durkusa yayi ta godiya yana masa addua.

Kamar yadda ta saba fitowa haka ta fito yau din ma, fuskar nan babu alamun murmushi, be taba ganin murmushin ta ba se ma kukanta da ya gani.

Yanzu shikenan baze kara ganin ta ba se bayan sun dawo. Ko da yake yasan gidan su ay. Ya san inda ze same ta. Wannan karon kuwa ze je har gidan su yayi sallama da ita. Ze cire duk wani tsoro ya tunkare ta. Tunanin da yayi a ransa kenan.

Yau ma haka ta wuce shi ta shiga napep ta tafi, shima ya bita har se da ta shiga gidansu sannan ya koma gurin ayki.
🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒

Shigowa yayi cikin company da izza, receptionist din tana masa magana amma be bata answer tambayar da tayi mishi ba hasali ma amsa mata yayi da tasa tambayar

"Where is the director's office"
Kai daga jin turancin ma kasan na masu abun ne.

"Do you have an appointment sir?
Kallan banza ya watsa mata sannan yace

"Show me where it is if you really want to keep your job"

Yau ga ikon Allah, mutumin da bata taba gani a company ba ze yi mata bazarana da aikin ta, bata bashi answer ba ta dauko telephone din kan tabble ta kira jidda, wadda daman itace secretary director din.

Jidda ta sauko dan jin ba'asin dake faruwa. Ta tarar da shi a tsaye yana shan shan kamshi. Ta gaishe shi sannan ta tambaya me yazo nima.

"Where is the Director's office"
Tambayar da ya sake yi kenan. Jidda ta kara tambayar sa ko yana da appointment, be bata ansa ba ita ma.  tace mishi ya jira ta tana zuwa, ta koma sama, bene na 3 sannan ta dawo rike da takar a hannun ta, ta mika masa takardar sannan tace

" please fill this form, i will book an appointment for  you"

Kallon banza ya watsa mata sannan ya nufi benen da ya ga ta hau da zata dauko masa paper, da gudu ta bishi tana kokarin dakatar da shi. Tana magana da karfi

"Dan Allah malam mene haka,"
Turancin ma guduwa yayi ta fara hausa abinta, haka ya janyo hankalin ma'aikatan company kowa ya fito don jin me yake faruwa.

Tureta gefe yayi ya ci gaba da tafiyar sa. Se da ya hau har zuwa bene na ukun ita kuma tana binshi a baya tana kokarin tare shi. Ya tsaya a daidai office din da yaga an rubuta  "Executive director" ko kwankwasawa beyi ba ya muda office din ya shiga,

ALH ibrahim ne a zaune tare da bakin sa mutum 2 da suke yin meeting, mamaki ne ya kama shi da yaga umar a kansu a tsaye. Kasa magana yayi saboda tsananin mamaki. Me ya kawo shi office dinsa, umar din da ya bari a gida.

Umar beyi ma kowa magana ba ya bude jakar bayan sa ya dauko wasu takardu ya zuba a wulakance a kan table a gaban Alh umar. Sannan ya juyo ya kalli jidda da ke tsaye a bakin kofa tana maida numfashi saboda saurin da ta dinga yi don ta hana shi shiga.

"I need your resignation letter by monday"

Ya karaso gurin da take tsaye a bakin  kofar. ya watsa mata kallon banza da kallon tsana, se lokacin ta gane ta tare mishi hanyar fita, ta matsa jiki a sanyaye ya fice ya barsu cike da mamaki, daga Alh ibrahim, jidda harda bakin da ke zaune.

Duk wannan hayaniyan Ak Romeo yana can  yawon soyayya

🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Bintu. A
09034346763

SarkakiyaWhere stories live. Discover now