Jigo

260 15 0
                                    

🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Shigowar nadiya a guje ne yasa alhaji  tashi a razane " lafiya !!!!" Don a kashingide yake kan kujera a wani katafaran falo da yasha kaya. Jallabiya ce a jikinsa da carbi a hannunsa yana ja dawowarsa daga mallasaci sallar asuba kenan.

" lafiya" ya kara maimaitawa don nadiya se haki takeyi saboda gudun da ta sha.

" yaya umar ne..... daddy yayaumar ne ya dawo"

Se da yaji gabansa ya fadi sosai domin beyi  tunanin dawowar sa a wannan lokacin ba, kuma babu wanda ya kira ya fada masa. Yakamata mallam inuwa ya sanar dashi dawowar sa. Cikin sauri ya fara  laluba wayarsa a cikin aljihun jallabiyar sa yana son kiran malam inuwa ya ji makasudin dawowar umar

umar ya shigo cikin falon, Kallo daya yayi ma mahaifin nasa ya juyar da kansa, domin kuwa ya tsani kallon sa, ya tsani tsayuwa da shi karkashin inuwa daya, kai ya tsani shakar iskar da ke daki daya da mahaifin nasa. Ya juya ya kalli nadiya da jan ido da har yanzu kallonsa take cikin mamaki. Ta razana sosai da kallon tsanar da yayi mata don tasan yayan nata be taba kaunar ta  ba balle ya dauke ta matsayin kanwa.

Be ce musu komai ba ya wuce ya fara hawa matattakalar bene da ke tsakiyar falon. Ya kai kusan rabin benan mahaifin nasa ya daka masa tsawa

" kai!!! me ya dawo da kai gidan nan."

Umar ya ja birki daga hawa matakalar bene ya tsaya chak  amma be juyo ya kalli mahaifin nasa ba sannan ya ci gaba da tafiyarsa kamar ba da shi din ake magana ba.

Ya karasa hawa sama sannan ya bude wata kofa ya shiga dakinsa. Yadda ya bar dakin haka ya dawo ya same shi. Dakin kacha kacha kamar bola, an watsar da komai a kasa. Plates din ya yake cin abinci suna nan da dattinsu kamar yadda ya barsu.

Ya kwanta da bayansa  a kan gadonsa da babu masaka tsinke saboda kaya ne a jibge a kai, baa gane  mai datti da mai kyau. Kallon ceilling yake yana tuno rayuwa. Yana tuno lokacin da rayuwar babu kunci babu bakin ciki, rayuwa cike da farin ciki da annashuwa, rayuwar jin dadi da soyayya. Ya tuno kyakkyawar fuskar mahaifiyar sa, maganar ta, dariyar ta.
Hawaye ne ya gangaro ta gefen idonsa, daya na bin daya. Yayi kewar ta sosai. Ya rasa wani babban jigo a  cikin rayuwarsa da babu wanda ze iya cike shi.

Alhaji ya dauko wayarsa yayi dailing number malam inuwa bugu daya malam inuwan ya dauka kamar wanda yake jira a kira shi.

" Alhaji umar ya gudu"
Malam inuwa ya katse alhaji  tun be ce komai ba.

"Na sani, ya dawo, yanzu haka yana gidana"
Alh ya tari numfashin sa

"Alhamdulillah tunda nan din yayi," cewan malam inuwa yana ajiyar zuciya sannan ya dora

" jiya da shi mukayi sallar isha ya tafi makwancin sa, yau kuma muna tashi da asuba bamu ganshi ba. Munyi duban har mun gaji"

" ba komai mallam mun gode da dawainiyar da kukayi da shi, Allah ya saka da alkhairi se kaji sako daga gare ni"

Sukayi sallama da mallam inuwa sannan ya zauna a kan kujera ya kalli nadiya da har yanzu a tsaye take.

"Je ki fadawa hajjiya binta umar ya dawo"

🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒

Ummulkhairi ta fara koyarwa a makarantar secondary ta mata da ke BWARI ta fara jin dadin aikin nata duk da akwai yar tafiya daga gidan kawun nata a USHAFA zuwa makarantar.

Yau ma kamar kullum ta tashi da sassafe tana shirin tafiya makaranta matar kawun nata inna asabe ta shigo cikin dakin, yaran inna asabe uku ne. Dukkan su mata.
Babbar yarinsu sa'ar khairi tayi aure da yaranta biyu itama tana nan a USHAFA, layuka biyu ya rabata da gidan iyayen ta. Se kanwarta farida wadda ta shekara biyu da gama secondary sannan autarsu zainab da ake cewa zainu da ke jss 3

Inna asabe ta shigo tana yatsuna fuska sannan tace
"yau babanki be bar komai ba ya fita Gaareji, kawo kudi a siyo kosai" ta fada a gadararce

Khairi ta danyi jimm kadan domin ta fara gajiya da yadda inna asabe ke karbar kudi a hannunta. Itama kudin da ake bata na alawee be taka kara ya karya ba ga kudin motar da takeyi, ga dan abunda baza a rasa ba na yau da kullum. Gashi tana son turawa ummanta wani abu itama domin kuwa bata sanaar komai.

Ta dauko jakarta ta ciro 300 ta bata. 
A wulakance inna asabe ta karba kudin.

" amman de baza ki ci ba ko, domin kuwa kosan dari uku baze ishe mu ba dukan mu".

" karki damu inna azumi nakeyi ma"
Khairi ta fada tana kokarin rataya jakat ta

Inna asabe tayi gaba abinta kamar daman bata damu da answer da zata bata ba. Ita de ta gama maganar ta.

Khairi ta fito domin tafiya makaranta a hanya take  tunanin yadda inna asabe ke da son kudin banza. Bata bar kawun nata ba.  kullum a cikin tambayar kudi take ga rashin godiyar Allah duk da kawun nata yana kokari ko yaya ya samu zeyi cefene ya kawo gida. Idan aiki yayi kyau ranar har tsire da balangu yake dawo musu da shi. Tasha jin fadan su akan ya bata kudi ayi abu da shi a gida ita kuma tayi zubin adashi da shi.

SarkakiyaWhere stories live. Discover now