Wacece ita

486 21 0
                                    


Wacece wannan?
Menene labarinta?
Daga ina take?
Ina kuma zata je?
Menene sunanta?

Tambayar da yayi ma kansa kenan da ya gagara bawa kansa answer. Ya kwanta a kan gado yana kallon ceiling yana tunano yanayin yadda ya gamu da ita. Tausayinta ya kama shi duk da be gama gane makasudun kukan nata ba.

Ya tunano yadda ta dago kai tana juye juye a adaidaita sahun tana kokarin gane inda take, kumatunta da hancin ta yayi jaaa kamar wadda aka mara. how can someone looked this cute while crying.

Yarinyar akwai sanyi kyau wanda nutsuwa ce kadai ze sa kaga ainiyin sanyayyan kyaun da Allah yayi mata, Gashi ta bace batt be san ta ina ze fara neman ta ba, Yaya zeyi ya kara ganinta? Yarinya kamar aljana ta tafi da hankalinsa daga haduwa daya.

Yana cikin wannan tunanin hajja tashiga dakin da sallama ta nimi guri ta zauna a gefen gadon da yake kwance.
" lafiya kake kwance da tsakar ranar nan"
Ta fada Fuskarta da dan damuwa sannan ta daura da cewar
"Ko bazaka fitan bane?

Ya gyara kwanciyarsa ya tokare kansa da pillow domin ya samu damar kallonta da kyau  
"hajja ina son na dan huta ne se zuwa anjima zan fita. Ina saddiq ne ko be dawo daga gyaran motar ba?"

Hajja cikin fada tace
"se da nace masa jiyan nan ya duba motar da safe kafin ya tafi dauko ka a airport saboda ta dade baa hauta ba, dayake yana da kunen kashi be duba ba gashi ya barka da hawa adaidaita sahu ruwa yayi maka duka"

murmushi ya kubce masa ba, ya fara shafa gemu yana murmushin
hajja cike da mamaki tace
  " kai kuma lafiya kake murmushi"

se a lokacin yasan murmushin ma yakeyi. Fadar adaidaita sahun da hajja tayi ne ya sa shi murmusawa ba tare da yayi la'akari ba. Yayi sauri ya dan maze sannan ya ja numfashi

"Hajja dan Allah ina son kiyi min addua"

ya dan tsaya jimm kamar me tunani sannan ya ci gaba
"ina neman wani abu ne idan da Alkhairi Allah ya tabbatar min da ganin sa"

Hajja tayi murmushi sannan tace
" duk abun da kake nema na alkhairi Allah ubangiji ya tabbatar maka shi babana"

Ya amsa da ammeen yana jin wani dadi a ransa. Hakan abdulkareem da hajja sukayi ta hira har laasar tayi sannan yayi mata sallama ya fita zaga gari.

( shi me tambayan wacece ita, shi din wanene)

Abdulkareem shine babba a gidansu yana da kanne 4, saddiq, Ibrahim, faiza da sumayya. Shekarar sa 38 Mahaifinsu ya rasu tun autar su sumayya batayi shekara 1 ba.
Asalin iyayensa mutanen azare ne don shi kansa abdulkareem a azaren aka haife shi sannan suka dawo kano. Mahaifinsa karamin maaikacin gwamnati ne wanda albashinsa be taka kara ya karya ba. Haka sukayi  ta lallaba rayuwa cikin rufin asira.

Abdulkareem tun yana karaminsa yaro ne me hazaka da neman na kan sa.
Lokacin da baban sa ya rasu yana dan shekara 16 tundaga wannan ranar dawainiyar gidansu ta hau kansa. Yayi sanao'in hannu kalla kalla duk don kar su tozarta.
Me nema yan tare da samu haka Allah yayi ta buda masa har ya kammala karatunsa na jami'a inda ya karanta Engineering

Cikin rufin asiri Allah ya taimake shi ya samu aiki a wanni babban construction company dake abuja. Dayake shi me hazaka ne da girmama nagaba dashi, haka akayi ta kara masa girma har ya zama shine head engineer  na construction company din.

Budi kam Alhamdulillah ya samu budi sosai, ya gina musu gida flat matsaikaci me kyau a unguwar jan bulo, ya siya ma mahaifiyarsa mota ana kaita duk inda zata je. Ya kan zo gida duk karshen wata yayi musu weekend sanan ya koma aikinsa. Kaninsa saddiq ya gama karatunsa shima yana aiki a banki har yayi aure ma. Kannensa mata duk sunyi aure suna zaman lafiya a gidan mazajensu.

🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Ummulkhair na kwance a kan gado tayi wanka ta shirya amma ta kuma neman guri ta kwanta zuciyarta cike da tausayin bawan Allah da ta gani jiya

A wani hali yake? Me suke masa? Meyasa suka kamashi ?
ita kam zuciyarta ta kasa mantawa dashi. To meyasa beyi ihu ba da suka sa shi a mota ya nima taimakon mutane? Ko dayake ruwa akeyi kafa ta dauke a titin. Ta gama yan sake sakenta sannan ta tashi domin hada jakarta na tafiya zamfara inda akayi posting dinta service. Bata taba tafiya mai nisa ba se yanzu da bautar kasa yayi kira. Iya karshen tafiyarta kaduna ne. Ta gama hada jakarta ta zumbulo hijab ta nufi parlor inda iyayenta suke.

Ta shiga da sallamarta ta tarada abba a kan carpet yana yin breakfast ta tsuguna ta gaishe shi. Ya amsa cike da murmushi a fuskarsa yana cewa

"ummu yan mata an girma yau se bautawa kasa"
tayi dariya tace

"abba nifa tsoron hanya nakeyi wallahi ba don yaya Aminu yace ze raka ni ba bansan ya zanyi ba."

Tana cikin magana umma ta shigo dauke da plate a hannunta ta miko mata
"ga abun kari kiyi sauri ki ci yayanki ya gama shiryawa ke yake jira"

ta karba ta gyara zaman ta ta fara lodar abinci saboda yunwar da ke cikin ta.

Sun kammala yin breakfast iyayenta sukayi mata adduan kariya da nasara ba don sun so tafiyarta ba se don babu yadda zasuyi. Yayanta Aminu ya fita ya samo musu adaidaita sahun da ze kai su tasha daga nan se zamfara.....

Wacece ita din?
Mahaifin Ummulkhairi mutumin kano ne haka zalika mahaifiyarta bata san wani gari ba se kano duk da de kakannin mahaifiyarta ance daga syria suka shigo Nigeria. Labarin babu musu idan akayi la'akari da hasken 'ya'ya da jikokin gidan. Domin kuwa gidansu mamanta a cikin gari ana masa inkiya da gidan JAJAYE.

Mahaifinta karamin dan kasuwa ne da ke siyar da huluna a kwari.  suna zaune cikin rufin asiri. Suna rayuwarsu gwanin ban shaawa. Mahaifinsu yana da burin ganin yaransa sunyi karatun boko me zurfi shiyasa beyi kasa a gwiwa ba wajan ganin sunyi makaranta me kyau.  Ta gama jami'a har tana shirye shiren bautar kasa.

Su uku ne kawai a gurin iyayensu. Yayan Ummulkhairi aminu, Se ita sannan kanin ta Abdullah.

SarkakiyaWhere stories live. Discover now