Al'ada 2

197 11 0
                                    

🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Tunda tayi parking take kallon su, yayin da suke kokarin fita daga motar su. Abu kadan se yace mata sannu. Jidda ji tayi kamar zuciyarta zata buga saboda bakin ciki. A take taji bakinta yana daci kamar mara lafiya, wani irin tashin hankali take fuskanta a zaune, ita kadai tasan me take ji na bakin ciki.

Khairi tana juyowa taga jidda a zaune a mota daman taji motar a bayansu amma batayi tunanin jidda bace. Duk da marar ta na ciwo haka be hana ta kwakulo murmushi ba
"Ina kwana aunty jidda"

Jidda ji tayi Maganar ta makale a makogwaro kamar ta hadiyi rai ta huta da bakin ciki
Maganar Abdulkareem tasa suka maida hankali kanshi
"Ahh jidda ashe kina baya na"

Maimakon taji sanyi yayi mata magana, ji tayi kamar ya kara iza wutar kunci ne a cikin zuciyar ta. Da kyar ta iya ansawa

"Eh nice"
Tun daga nan be kara ce mata komai ba ya maida hankalin sa gaba daya akan khairi da ta ci gaba da yamutsa fuska saboda yadda take ji marar na kara murdawa.

Khairi bata kara bin ta kan jidda ba ta doshi hanyar tafiya, Abdulkareem ma binta yayi kamar jela. Sun ma manta da wata jidda da ke cikin mota bakin ciki ya hana ta fitowa.

Idon jidda yana kan Abdulkareem shi kuma idon Abdulkareem yana kan khairi, wannan wani irin kaddara ce.

Suna tafiya taji wani zaffefen hawaye na bin kumatun ta. Hausawa sunyi gaskiya_ so maso wani koshin wahala. Yau ta tabbatar Ak be taba mata kallon macen da ze iya so ba. A nata tunanin Ak ya fara noticing dinta amma zuwan khairi ya dauke masa hankali daga kanta gaba daya.

Me khairi zata nuna mata idan ba haske ba. Inde kyau ne ta tabbata tafi khairi kyau, ga diri da Allah yayi mata, jidda irin matan nan ne masu hips. Diri kam ta diru masha Allah Inde ta fannin diri ne khairi bata isa ta tsaya kusa da jidda ba don babu hade.
Khairi da take siririya, abubuwan de babu yabo babu fallasa. Kirjin ma ba wani abun kirki a wajen, Tana da daidai nata de.

Ak da khairi suka jera har cikin company duk da tana tsoron kar umar ya gansu tare, tasan kalar masifar sa balle ma har barazana yayi mata.

Se da suka kai bene na biyu sannan suka rabu. Ak yayi kokarin raka ta office dinta amma ta dakatar da shi. Tana tsoron kar umar ya gansu ya fara sabon drama. Be so hakan ba amma ya hakura yace mata idan baza ta iya zama ba ta kira shi ya maida ta gida.

A hankali taja kafarta ta haura bene na 3. tana cikin tafiya taji an janyo ta da karfi ta baya wanda ya sa ta kai ga faduwa a kasa. A fusace ta juyo taga waye zeyi mata wannan ketar.

Jidda ta gani a tsaye a kanta tana mata wani irin kall0 sannan tace
"Ahh ban san na taka ki ba, hijab dinki yayi tsawo da yawa, sannan dan Allah ki dinga tsayawa a dai dai matsayin ki"

Tayi mata wani kallon baza hade da wani makirin murmushi sannan ta wuce.

Tunda jidda ta gansu tare a mota zuciyar ta ke tafasa, bayan ta hawo sama ma ta kara ganin su a tsaye suna magana, bata san me suke cewa ba amma ji tayi ta kai makura. Idan batayi ma khairi wani abu ba bazata samu sassauci ba. Shiyasa ta biyo ta ta take mata hijab din da yake jan kasa, tare da sa hannu ta finciko ta da karfi se da ta kai kasa.

Khairi kuwa mamaki ne ya hana ta magana, ta tabbata janyo ta tayi domin taji yadda aka finciki hijab din ta baya. To me tayi mata ne haka da tsanani.
Ranar da suka fara haduwa da sakin fuska ta karbe ta shiyasa ma duk inda ta ganta take gaishe ta. bayan nan ne taga chanji kuru kuru amma batayi tunani wani abu ba. Yanzu kam ta tabbatar akwai abun da yasa tayi treating dinta haka.

Ta tashi jiki ba kwari ta da duba jikinta ko ya baci, Allah yaso gurin da kyaun shi ma. Ta karasa office dita zuciyar ta cike da kuncin abunda jidda tayi mata.

SarkakiyaWhere stories live. Discover now