🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Tass .... TasssssKhairi taji Saukar mari sau biyu a fuskarta da babu zato ba tsammani har se da ta fadi kan kujera saboda zafin marin. Rike kuncin ta tayi ta kalli saadatu da ke kallon ta tana huci
Tayi wani kukan kura ta rarumi Alh audu ta kwalar rigarsa ta manna shi a bango tana wani irin ihu na tashin hankali
"Ka cuce ni, ka cuce ni. Allah ya isa ban yafe maka ba"
Abunda tayi ta fada kenan ta ci gaba da ihun tana kai masa duka ta ko ina.Khairi kuma da ke zaune zamowa tayi daga kujerar ta zauna a kasa ta dasa nata zazzafan kukan. Hawaye ne daya na bin daya ke sauka tare da shasheka. Wanann shine ga mari ga tsinka jaka. Ita da za'a ketawa hakki ita da shan mari. Ji tayi wani malolon bakin ciki ya tokareta a wuya, Zuciyar ta a cushe, Tunanin ma ta kasa yin sa tayi
Alh audu barin saadatu yayi ta gama dukan sa har ta gaji sannan itama ta zame tayi zaman dabaro a kasa. Ta kasa yin kukan ma .
Yana ganin haka ya sulale ya barsu a falon ya fita daga gidan. Yau ko giyar wake ya sha ba ze kwana a gidan ba.Se da aka dauki kusan awa daya babu wanda yayi magana daga karshe de saadatu ta budi baki da kyar tace
"Me yayi miki"
Murya na rawa khairi ta ansa
"Beyi min komai ba""Kar kiyi min karya"
ta fada da tsawaKhairi da saadatu sa'oi ne, Dan khairi ma ta girme ta da watannin Amma yau khairi ta bar mata girma gaba daya. Khairi ta kara cewa
"Beyi min komai ba wallahi, ina bacci ya shigo ya fara taba ni har nayi ihu sannan ya rufe min baki, da kyar na samu na kwace........"
Kuka ne ya kwace mata ta kasa karasa abunda zata ce. Se alokacin itama saadatu kukan ya zo mata. Se da sukayi me isar su sannan saadatu tace su je su kwanta washe gari zasuyi magana.
Jiki babu kwari kowa ta tafi daki don yin bacci amma baccin kauracewa yayi. Da kyar bacci ya kwashi khairi ita kuwa saadatu yadda taga rana haka taga dare.
🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒Washe gari da safe babu wanda ya iya fitowa daga daki a cikin su, 10 na safe ma ta gota sannan saadatu ta shigo dakin da khairi ke kwana rike da babyn ta khalifa a hannu. Ta zauna a gefen gado sannan ta kwantar da khalifa da ke bacci a gefe.
Ta tarar da khairi ta shirya tahada kayanta tsaf a jaka. Dan kam yau ba abinda ze sa ta kara kwana a gidan su. Yau se kano."Tafiya zakiyi ne kika hada kayan ki"
Saadatu ta tambaya"Eh tafiya zanyi. Zan koma kano"
Saadatu tayi saurin kama hannun ta sanan fashe da kuka.
"Na roke ki da Allah khairi kada ki fada wa kowa abunda ya faru a gidan nan, ki taimaka ki rufa min asiri ki bar wannan abun a tsakanin mu"
Mamaki ne ya kama khairi da ta kasa magana ta ci gaba da sauraron abinda saadatun ke cewa
"Nasan abinda Alhaji yayi miki be kyauta ba. Kuma bazaki taba mantawa da shi ba, ban ce ki yafe masa ba kuma bazan ce zan baki hakurin abun da yayi miki ba don bani da bakin da zan baki hakuri ko na roke ki gafara. Nide fata na ki rufa min asiri kada aure na ya mutu"
Kallon mamaki khairi tayi mata amma still ta kasa magana saboda kwakwalwar ta ta daskare
"Nasan zakiyi mamakin abunda na fada miki, amma babu yadda zanyi ne. Ina son na ceci aure na. Idan nace miki basan Alhaji yana bin mata ba nayi miki karya. Amma ban taba tunanin ze bi har yar uwata ba"
Saadatu ta tsaya da yin magana saboda yadda hawaye ke zuba a idon ta. Ta sa kanta ta kan hannun khairi da ke rike ta ci gaba da kukan.
Khairi ta dago da kanta tana share mata hawaye sannan tace
"Ba komai saadatu, Allah ya fitar dake daga matsalar da kike ciki"
Bata san abunda zata ce ba, idan tace zata fadi abunda ke ranta bazeyi ma saadatu dadi baTa miki tsaye tana kokarin yafa mayafin ta. Saadatu ta kara janyo hannun ta
" ki taimaka min khairi, aure na da yarana nake ji, bazan iya zaman zawarci ba. Ina kan adduan Allah ya shirya min shi. Khairi bazan iya barin gidan nan ba"
Duk yadda khairi tayi kokarin danne takaicin da ke cinta se da ta hasala
"Baza ki iya barin gidan nan ba? To ay kuwa zaa fitar da gawar ki idan ya kwaso wata cuta ya sa miki"
Saadatu tayi wani dariyar takaici sannan tace
"Me kuma ya rage khairi? Me ya rage kuma, ay aikin gama ya riga ya gama. Abunda zan guda ma ya riga ya same ni, to gudun me zanyi kuma"Khairi ta dawo ta zauna tana zare ido.
"Saadatu......???""Saadatu ta kara yin wani murmushin takaici me ciwo
"Hmmm Hiv kike nufi ba? dukkan mu ni da Alhaji muna shan magani"Khairi cikin tashin hankali ta kalli khalifa dake kwance yana bacci
"Khalifa fa??""Khalifa Lafiya qalau, tun a cikin salma (yar ta ta biyu) na san ina dauke da ciwon, an bamu shawarwari yadda yaran baza su kamu ba. Alhamdulillah salma bata dauka ba. Shima khalifa ina bashi magani kafin na bashi nono"
Khairi tayi ajiyar zuciya sannan ta maida kallon ta kan saadatu
"Yanzu saadatu kin san da wannan abu kike zaune a gidan nan"Saadatu ta kara yin dariyar takaici sannan tace
"Yaya kike so nayi khairi, aikin gama ya gama ay, ko na bar gidan ma wa zan samu na aura. Dole se de me ciwon, Duk wanda zan aura shima idan aka bibiya halin su daya da Alhaji. Gwara ka zauna da mugun da ka sani da mugun da baka sani ba. Kuma bana so na bar yara na"
Kukan ta ci gaba da yi, se da tayi me isar ta sannan ta ci gaba
"Bakin alkalami ya riga ya bushe. Kuma da ban fada miki ba baza ki sani ba kwata kwata saboda Alhamdulillah ba nunawa takeyi a jiki ba"
Haka suka ci gada da jajantawa. Suyi kuka tare suyi share hawayen sannan su cigaba da magana. Se bayan azahar sannan khairi tayi mata sallama ta dauki jakar ta se kano.
🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Bintu. A
09034346763
YOU ARE READING
Sarkakiya
RomanceLabarin tsantsar soyayya me cike da sarkakiya ce ta kullu a tsakanin su. Ummulkhair ta zamo Allura cikin ruwa wanda me rabo ne ze dauka. Shin wa zata zaba a cikin su? Boyayyen masoyi Abdulkareem wanda yayi dakon soyayyar ta na tsahon lokaci ko kuma...