🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Tun bayan haduwar shi da ummulkhair a bene yake baya baya da ita, duk abunda yake yi se tunanin ta ya fado masa. Ransa har baci yake yi saboda ya kasa cire ta daga tunanin shi. Yayi yayi ya sa zuciyar sa ta dena ainayo masa ita amma inaaa abun ya gaagara, wani lokacin har bubbuga hannun sa yakeyi a kansa yana fada ma kansa "concentrate"Duk abunda ze hada shi da ita dodging dinsa yakeyi shiyasa yanzu be cika sata aiki ba, wani lokacin ma kulle office dinsa yakeyi ta gama bugun ta baze bude ba. Haka zata dawo office dinta ta ci gaba da zaman banza gashi ya hana ta fita cikin Al'uma, Har bacci take yi idan ta gaji ta tafi gida.
Dadin dadawa kuma be san me suka tautauna da baban shi ba, gwara yayi baya baya da ita tunda yasan spy din baban sa ce, dole yayi baya da duk abunda ze ruguza masa plan. Duk da cewar khairi bata cika shishige masa ba kamar sauran secretary amma yasan dole baban shi ya kitsa mata wani abun
Anniversary din company sauran kwana 5, kuma lokacin shagalin bikin anniversary yake so ya zartar da nashi aniversary shegantaka.Yau ma haka ta gama kwankwasa kofar shi be bude mata ba, ta dawo ta zauna har ta fara game a wayar ta sannan taji an murda key din kofar alamar ya bude kenan. Ta shiga office din da sallama wanda ya ansa a hankali kamar me yin rada. Ta samu guri ta chake tana jiran abunda ze ce
"Sit down"
ya fada a takaice wanda yasa tayi mamakin shine ya ce mata ta zauna, lallai zaayi ruwa da kankara. Daman tana kusa da kujerar sofa ta sulale ta zauna"Ba a nan ba, dawo nan"
Umar ya fada tare da nuna mata kujerar da ke jikin table wadda ke kallon sa.
Ba musu khairi ta dawo kujerar da yace mata.Sanyayyen kamshin turaren ta ne ya dake shi wanda yasa dole ya kalle ta, yau wani exceptional kyau tayi. Atamfa green ta saka sannan ta daura sweater me kamar jacket dayake garin ya juya daga yanayi na zafi zuwa sanyi. Ta daura dankwalin atafar sannan tasa karamin mayafi a kai, ba rolling dinsa tayi ba amma yadda ta yafa shi gwanin shaawa.
Khairi bata cika saka atamfa ba se dogayen riguna da dogayen jalbab. Yau da ta saka atamfa kamar ka sace ta ka gudu saboda kyaun da tayi.
Umar ya dauki mutuna yana tunanin ta ina ze fara mata magana, yau har wani kwarjini tayi mishi . me ze ce mata ta gane abunda yake nufi. Ya kula da zuciyar sa baza ta iya tsanar ta ba kamar yadda ya tsani sauran sakatarorin sa. Tunda baze iya tsanar ta ba, gwara ya janyo ta side dinsa.
zuciyar sa tana zafi idan ya muzguna mata, yayi yakinin ya fita jin zafin abun da yake mata.
Yayi gyaran murya sannan yace
"Bazan tambaye ki abunda kuku tattauna da CEO ba saboda nasan abunda ze aikaita. I've never been open to anyone amma yau zanyiYa dauki cup din da ke kusa da shi yana zuba brown sugar a cikin coffee din da ya hada sannan ya ci gaba.
"Idan kina son zaman lafiya da ni to ki fita daga harkar shi, mahaifina ne na fiki sanin halin shi. Its high time da zamu dinga game din hide and seek dinnan. Nasan yayi hiring dinki don ki dinga spying a kaina.
"Spying kuma??"
khairi ta fada da mamaki a muryar taDariyar takaici umar yayi sannan yace
"Ohh denying zakiyi kenan"Khairi ta girgiza kanta alamar a'a sannan tayi magana
"Ni bansan a ina ka samo zancen spy ba, illa iyaka abunda na sani shine Mahaifin ka yana matukar sonka da son ci gaban ka. Ya damu sosai a kanka, kai kuma naga kamar ba haka bane a bangaren ka. sannan yana kokarin ya samu damar da ze taimaka maka, me yasa kake blocking duk wanda ze rabe ka. Me yasa baza ka bawa mahifinka damar da ze nuna maka kulawar shi ba
Tayi maganar cikin nutsuwa yadda duk me sauraro baze gaji da jin sharhin da takeyi ba.
Umar ya kalle ta cikin ransa yana tunanin me babansa ya fada mata haka da yasa tayi maganar nan. Yadda tayi maganar cike da nuna kulawa game da Alh ibrahim
YOU ARE READING
Sarkakiya
RomanceLabarin tsantsar soyayya me cike da sarkakiya ce ta kullu a tsakanin su. Ummulkhair ta zamo Allura cikin ruwa wanda me rabo ne ze dauka. Shin wa zata zaba a cikin su? Boyayyen masoyi Abdulkareem wanda yayi dakon soyayyar ta na tsahon lokaci ko kuma...