Tambaya

159 8 0
                                    

🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
"Kinji abunda umar ya fada min jiya da yazo kafin ki shigo parlour"

Umma ta washe baki tana wani kayattacen fara'a, farin ciki ya lullube ta jin abun da abba yace. Cikin fara'a tace
" Faduwa tazo daidai da zama ay, amma naji dadi labarin nan da ka zo min da shi. Shi umar dinne ya fada maka yana son Auren khairi?

"Sau nawa zan maimaita miki ne zarah, ya ce min ita yazo gani a kano har yayi kicibus da sabon Al'amarin nan"
Abba ya fada fuska ba yabo ba fallasa

"Kaga ja'irar yarinya, bata taba fada min sun kulla wata alaka da dan uwan ta ba"
Umma ta fada tana dariya

Abba ya dan gimtse fuska
"Ke fa har yanzu na kula baki gane me nake nufi ba, kin kasa fahimtar inda gizo ke saka.
Abba ya ja dogon numfashi sannan ya ci gaba

"Yau ne fa zaa zo tambayar Ummu, iyayen wannan Abdulkareem din da ta fada mana wanda yazo jiya. na fada miki har mun gaisa a kofar gida ma"

Umma ta danyi tur sannan tace
"Wannan ay me sauki ne, idan suka zo ba se a basu hakuri ba ace akwai wanda akayi ma Alkawarin ta. Se a basu hakuri akawai, tambaya ne ba kawo kudi ko sa rana ba, naga baa bashi ita ba tukunna"

Abba ya kara girgiza kai
"har yanzu kin kasa gane abun da nake hange, bamu ji ta bakin ummu wa take so ba. Da dukkan Alamu Abdulkareem dinne tunda shi ta bawa dama suzo suyi tambaya, Idan kuma ba umar din be mata ba fa

Umma ta ja karamin tsaki
"Haba Abba daman khairi tana da bakin cewar umar be mata ba. Yaron da kafin a samu irin shi se an tona. Kuma naga da kyaun sa babu wacce umar ze ce yana so ta kasa son shi. Ga dadin dadawa dan uwanta ne, gida be koshi ba zaa kaiwa dawa? Dan Allah ka bar wannan maganar

Abba ya tsaya shiru yana tunani bayan mituna kadan yace ma umma ta kira mishi khairi. Umma ta kwalawa khairi kira
Khairi ta taho tana murza ido dan tashin ta daga bacci kenan

Ta gaishe da su sannan abba yasa ta zauna kusa da shi. Ya dan yi mata wasa kadan tayi ta dariya, daga baya kuma ya dan hade rai yace
"Uwata na kira ki ne don na tambayar ki wani abu, wanda kika ce zasu zo yau ya alakar ki take da shi"

Khairi ta danyi murmushi irin na jin kunya sannan tace
"Shima tare muke aiki da shi a Abuja"
Tana kaiwa nan tayi shiru

Abba yayi dariya sannan yace
"ba haka nake nufi ba, kina son shi ne ? kina son auren shi?"

Khairi ta rasa yadda zata bawa abba answer saboda kunya se murmushi da take ta yi kamar bakin ta ze tsage

Umma da ke gefe ta cika tayi makil da takaici, wai har abba ze tsaya bata lokacin tambayarta.

Abba ya sake magana yana murmushi
"To na gane, kina son sa kenan?

Umma ce ta katse shi da fadin
"Shi kuma umar din fa?
Tana magana tana hararar khairi. Khairi tana jin an ambaci umar gaban ta ya fadi, duk yadda akayi ya fada musu wani abu kenan

Abba ya dan bata rai ya kalli umma cikin masifa yace
"Ya kike haka ne? Ba tambayar ta nakeyi ba, Ni bana son wannan shishigin"

Ya juyo ya kalli khairi
"Ummu, kinsan maganar da umar yazo ya same ni da shi jiya? Yace shima yana son ki kuma yana neman izni auren ki daga guri na

Da sauri khairi ta dago kai tana fadin
"Abba wlh bana son shi, shima yasan da haka tun ba yau ba na fada masa sannan yasan wanda nake so ay"

Umma cikin masifa tace
"Rufe min baki mara kunya, yanzu har kin san so. Shi wanda kike so din waye haka da zaki guji dan uwanki akan shi. Lallai ma yarinyar nan, ay kuwa ki koya ma kanki son umar tun wuri"

Abba yayi saurin dakatar da umma tare da daga mata hannu
"Ya isa haka zarah, bana son kara jin wani magana"
Ya juyo ya kalli khairi
"Tashi ki tafi, zamu tattauna"

Khairi ta tashi a sanyaye bata so abba yace ta tafi ba, tafi so a daddale magana anan, tafi so ta ta kara tabbatar musu Abdulkareem ne zabin ta, tsoro take ta barsu tare kar umma ta rinjayi tunanin Abba.

Tana fita umma ta juyo kan abba
"Abba ya kake.....
Kafin ta karasa abba yace mata
"Miko min hula ta zan tafi kasuwa, zan dawo kafin la'asar saboda bakin da zasu zo"

Umma ta wangale baki tana kallon sa da mamaki
"Abba????" Ta kira sunan sa irin bata gane me yake nufi ba, da yaga ba miko masa hular zatayi ba ya tashi ya dauki hular sa a saman kujera yayi ficewar sa.

Yana fita umma ta dau waya ta fara fada ma yan uwan ta, har Aunty maimuna se da ta kira ta fadawa. Khairi de na daki tana jiyo ta. Tana ta addu'a a ranta Allah ya dora ta akan duk wanda ze zame musu matsala a alakar ta da Abdulkareem

Wajen karfe 3:30. Abba ya dawo daga kasuwa, ya taho da ruwa da lemun roba a leda harda yan sbacks da ya siyo a bakery. Yace ma umma tasa lemon a fridge ya danyi sanyi kafin bakin su karaso. Umma de ta karba rai a bace, da tana da dama ma baza ta bari bakin su zo ba.
Khairi kuwa bata shiga harkar umma ba kwata kwata a ranar saboda tasan halin babar tata.

Kafe 4 :20 bakin suka zo, Abdulkareem yayi ma khairi waya ya sanar da ita suna kofar gida, ita kuma ta tura kanin ta Abdullah ya fada ma abba su zo. Abba ya fita ya shigo da su parlour da fara'a. Ance shimfidar fuska tafi ta tabarma, sun ji dadin yadda abba ya tarbe su shi da wani aminin sa kuma mokocin sa wanda daman tun jiya ya fada masa za'a zo tambayar khairi. Ko da sukayi sallah la'asar ma tare suka dawo gidan su khairi suna jiran bakin.

Daga bisani dangin Abdulkareem suka fara bayanin abun da ya kawo su Bayan yan gaishe gaishe da dan hira irin na dattawa.
Suka gama bayanin su, tarihin Abdulkareem da duk abunda ya kamata a fada idan ana tambayar izni.

Alh shehu Abokin Alhaji ne yayi magana
"Munji dadin yadda kuka zo nemar wa dan ku iznin auren yar mu, munji dadin zuwan ku kwarai da gaske saboda duk wanda ya nuna yana son naka ay abun ka karbe shi hannu bibbiyu ne, insha Allah zamuyi namu binciken, kusan Aure se da bincike, idan muka gama shawara za mu neme ku insha Allah."

Alh shehu ya kalli abba ya ce mada
" nasan Alhaji wada ay, abokin kani na ne sa'adu don tare sukayi makarata a illorin"

Abba yayi murmushi tare da fadin
"Allah sarki kamar gida ne ay, Insha Allah baze gagara ba"

Alh wada ya amsa
"Hakane Alhaji mu ma mun fi so ayi binciken sosai, Allah ya tabbatar da Alhairi, zamu jira sakon ku insha Allah mun gode sosai da karamci"

Alh shehu yace
"To ina sirikin namu yake, ko ba'a zo da shi ba"

Alh wada yana dariya yace
"Yana kofar gida yana jiran mu"

Sukayi dariya gaba daya, Abba be cika magana ba se murmushi, daga haka kuma aka dan taba hira dayake Alh shehu ya san Alh wada se hirar tayi dadi. Akayi hira sosai suka karbi number juna sannan daga bisani sukayi sallama.

Abba da Alh shehu suka rako su har waje inda suka tarar da Abdulkareem a bakin mota se safa da marwa yake. Yana ganin su ya karaso ya durkusa har kasa ya gaishe su. Su abba suka amsa da fara'a sannan sukayi sallama da su baki daya

Bayan tafiyar su Alh shehu yake kara yi wa abba bayanin yadda ya san Alh wada saboda aminin kanin sa ne kuma ya san su mutanen kirki ne, amma zaa kara bincike kamar yadda ya bukata. Alh shehu Ya daura da cewar

"Alh ishaq naga yaron ba lefi kamar zeyi hankali da nutsuwa"

Abba yana murmushi yace
"Nima naga hakan, dan Allah Alhaji ina jiran bayanin ka nima kuma zanyi bincike ta bangare na sannan nayi shawara da yan uwa na, duk abun da muka yanke zaka ji"

Da haka Alh shehu yayi ma abba sallama ya shiga gidansa abba ma ya dawo gida.
Yana shigowa ya tarar da umma wanda daman jiran sa take

"Abba ya kukayi"
Ta fada da zakuwar son jin abun da suka tattauna

"Dadina dake zahra akwai zumudi ki bari na zauna mana zaki ji yadda mukayi, dole zan fada miki ay"

🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Bintu. A
09034346763

SarkakiyaWhere stories live. Discover now