🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Haka Rayuwa ta ci gaba da tafiya a gidan, khairi tana rage damuwa da Abdulkareem with passing of time, ba hakan yana nufin baya ranta ba. Yana nan makale a zuciyar ta, da shi take kwana da shi take tashi, ta koyi tawakkali ne kawai ka fawalawa Allah komai.Relationship dinta da umar is quite complicated, yanzu bata jin haushin sa kamar da. Takan zauna a parlor har tayi kallo, idan abun nashi ya tashi kuma yayi ta terrorizing dinta da sunan punishment, wata rana har guduwa toilet take ta rufe
Har yanzu ba abun da ya shiga tsakanin su na kwanciyar aure se teasing dinta da kullum yake. Kissing kuwa a rana se Yayi kissing dinta har tana loosing count, har ta saba da kiss din sa salo salo. Tana ganin shi take sa hannu ta rufe lips dinta amma se ya bambare hannun yayi. Se dare yayi ta juyi, shi a haka da sunan punishing dinta yake amma a zahiri kansa yake punishing.
A kwana a tashi har anyi wata 2 da auren su, khairi ta riga ta saki jikin ta dan ta san duk abunsa se dai yayi romance ya kara gaba amma babu zancen oga kwata kwata.
Ranar tana parlour umar ya tarar da ita a zaune, ya kwanta a kujerar da take tare da daura kan shi a cinyar ta. Ta ture kan, ya sake dawowa da shi, haka sukai tayi har ta gaji ta barshi ya kwanta.
Kallon ta yayi cike da murmushi a fuskar sa yana kara jin sonta yayi baka bake a zuciyar sa
" wani abu nake son na fada miki""Ina jin ka"
Khari ta ansa ba yabo ba fallasa."Jibi Insha Allah zan tafi US, zanyi one or two weeks a can"
Umar ya fada yana kallon idon ta ko ze ga alamar sadness saboda tafiyar da ze yi, amma da mamakin sa her reaction was cold, batayi showing wani emotions ba Hakan ya sa ya damu sosai saboda he is on a journey of a life and death situation."Ok"
Ansar da khairi ta bayar kenan, a zuciyar ta tana so ta tambaye shi me ze kai shi US all of a sudden amma ego dinta baze bari ba. Hasali ma kallo ta ci gaba da yi, kallon da tunda umar ya kwanta a cinyar ta ta dena ganewa.Kallon ta ya ci gaba da yi yana daga kwancen, kallo na kurrulla kamar ze cinye ta. He would missed her so much, he would missed her pretty face, he would miss her scent and everything about her.
"Mallam ka ishe ni da kallo"
Ta fada ba tare da ta kalle shi ba idon ta na kan tvUmar yayi dariya ganin yadda ta hade rai
"Akwai inda aka haramta miji ya kalli matar sa?"Ta kara hade gira
"Ban sani ba amma ni ka ishe ni"Umar ya kara dariya, she looked cute with that face. Umar ya tashi daga kan cinyar ta sa hannu biyu ya matse kumatun ta wanda yasa lips dinta suka yo gaba, ya manna mata light kiss a lips tare da fadin
"I will miss you"
Khairi kuwa ta galla masa hararaUmar ya dan zare ido
"Au hararata ma kike to bari ki gani"Ay kafin ta kara yin magana se jinshi tayi a kanta ya danne ta, ya sakar mata gaba daya nauyin shi wanda ya sa ta kurma ihu jin ze karya ta da nauyi.
Ba abun da umar yake se dariyar mugunta yana fadin
"Se kin ban hakuri zan daga ki"🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Ranar tafiyar umar da sassafe khairi ta tashi. bata san me yasa ta tashi da wuri haka ba. Haka kawai jikin ta ya bata ta shiga kitchen tayi mishi breakfast tunda tafiya zeyi. This is the little she can do for him dan Bata taba girki a gidan ba se ranarTayi mishi egg sandwich da coffee tunda tasan mayen coffee ne, har coffee maker yake da shi a gidan tunda bashariyya bata iya hada coffe ba. shi yake shiga kitchen din ya hado kayan sa.
Karfe 8 ya fito parlor a shirye hada da jakar kayansa. breakfast ya gani a kan dining table khairi kuma a zaune a kujerar sofa fuska babu yabo babu fallasa.
Ya karasa kan dining table ya zauna. yasan ba bashariyya bace tayi dan a time din bata zo ba maMurmushi yayi me kayatarwa sannan yace mata
"Good morning baby"
Ita de bata ansa masa ba .
Ya zauna yaci breakfast din tas yana ta jin dadi a ranshi ganin ana samun incredible improvement a relationship dinsu.8:30 Abdullah ya zo gidan, daman sunyi da umar ze kai shi aiport se ya dawo da motar. Ya bar ma Abdullah sallahun ya fara koya ma khairi mota da motar shi bayan ya tafi.
Umar ya mika ma khair Atm card dinsa wanda makuden kudi ne a ciki, duk abun da zata siya ze ishe ta ko shekara zeyi, Idan ma gidaje zata siya kudin da ke ciki ze isa.
Abdullah ya daukar masa jaka ya tafi sawa a mota.Umar ya kamo khairi ya rukunkumeta a kirjin shi tightly Tare da manna mata kiss duk inda ya samu
" ya isa haka"
Ta fada da murya kamar me shagwaba, shagwabar da bata san ma tayi baYa kalle ta sosai sanan yace
"I will miss this sweet lips"
Yana gama fadin haka yayi kissing dinta, har se da ta gaji ta ture shi saboda taga abun ba na karewa bane.Suna cikin haka suka ji muryar Abdullah nan da nan umar ya sake ta sannan ya tsaya yana sauraron ko zata ce mishi Allah ya kiyaye, ko de wani abun amma shiru. da yaji shirun yayi yawa se yace
"Na tafi, Allah ya dawo da ni lafiya ko dan na ga face dinki"Shi yayi ma kansa adduar tunda be ga alamar zatayi mishi ba.
Ya fita daga parlor yana weaving amma saboda karfin hali irin na Khairi weaving din ma ta kasa masa.He really wanted her to say something ko yaya ne, yaso ta tambaye shi abun da ze kaishi US, yaso ta raka shi har wajen mota amma batayi hakan ba wanda hakan ya tarwatsa zuciyar sa. This might be his last time of seeing her
🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒A kwance yake a kan gado yana kallon ceiling, kana ganin shi kasan he is lost as usual. Hajja ta shigo dakin ta zauna a kan gado kusa da shi
"Babana"
Hajja ta kira sunan sa a hankali tare da taba shi"Naam"
Ak ya amsa a sanyaye tare da yunkurin tashi zaune daga kwanciyar da yake."Ina so na kara maka tunin gobe ne komawar ka gurin aiki"
Hajja ta fada tare da tsura masa ido"Wlh hajja bana son komawa kwata kwata, bazan taba samun kwanciyar hankali a gurin aiki. Bazan iya zama inuwa daya da azzalumai ba. Gwara na nemi wani aikin kawai"
Hajja ta bata fuska
"A kul, kar na kara jin ka fadi haka. Saboda wata yarinya zaka lalata rayuwar ka, Allah beyi matar ka bace dole ka dauki hakuri da dangana. Ka fini sanin yadda neman aiki yake wuya da kake cewa zaka bar aikin. Ahir dinka wlh, bazeyu na tsura maka ido ka ruguza rayuwar ka ba akan wadda zuwa yanzu ta rungumi mijin ta ta manta da kai"Hajja ta dan saukar da murya alamar rarrashi tare da cewa
"Na sanka da tawakkali babana. Kayi hakuri ka fawallawa Allah komai Allah ze musanya maka da wadda ta fi ta. Bakin alkalami ya riga ya bushe dole ka tashi ka saita rayuwar ka saboda babu wanda ze saita maka idan ba kai din ba"Ak yasan dukkan abun da hajja ta fada gaskiya ne. Ya fara healing daga rashin ta, komawar sa aiki ze kara fama masa ciwon da ke zuciyar sa. Everything will remind him of her, daga motar sa, parking lot, stairs, reception kai komai ma ze tuna masa ita. Zafin ciwon da ze ji ze fi wanda yake ji a yanzu. Yana so ya manta da ita gaba daya a rayuwar sa amma abu ne me kamar wuya.
Washe gari da safe hajja ta hada mishi tarkacen shi aka kai mota, daman tayi ma saddiq magana yazo ya kaishi abuja idan yaso se ya dawo a motar haya.
Da sassafe saddiq din yazo. Hajja ta zaunar da Ak ta kara mishi nasiha da lallashi tare da adduo'i kala kala.
Ak yace saddiq ba se ya kaishi ba, ba ciwo yake ba da baze iya tuka kansa zuwa abuja ba.
Babu yadda hajja batayi ba ya bari saddiq ya kai shi Ak yaki yarda. Haka hajja ta hakura tayi mishi adduan Allah ya kiyaye hanya.Ko da ta dawo gida adduan ta ci gaba da yi sannan ta sha alwashin Insha Allah zata nemar wa Abdulkareem matar da zata share masa hawayen sa. Matar da zata so shi fiye da yadda yake son ta don taga yadda ya wahala akan wadda yake so din. Be iya soyayya ba saboda yaso Ummulkhairi har abun yayi over. Baza ta kara bari ya fada irin wannan tsananin soyayyar ba
🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Bintu. A
09034346763
YOU ARE READING
Sarkakiya
RomanceLabarin tsantsar soyayya me cike da sarkakiya ce ta kullu a tsakanin su. Ummulkhair ta zamo Allura cikin ruwa wanda me rabo ne ze dauka. Shin wa zata zaba a cikin su? Boyayyen masoyi Abdulkareem wanda yayi dakon soyayyar ta na tsahon lokaci ko kuma...