🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Umma da Abba da Alh ibrahim suka shigo har uwar dakin iya falmata inda khairi ke zaune, kallon su take tana jiran wani yayi magana domin ta kagu tasan results din. Umma ta zauna kusa da ita tana murmushi tare da cewa
"Munyi farin ciki da wannan labarin da muka samu yau, ubangiji Allah ya baki lafiya ya kare abun da kike dauke da shi ya raba ku lafiya"Nan da nan hawaye ya ciko a daga idanun khairi, ta rasa farin ciki zatayi na zama uwa ko kuma bakin ciki zatayi saboda umar ya rasu ba tare da yasan ya bar jinin sa a baya ba. Ya bar duniyar ba tare da ya san ya bar jinin sa a doron kasa ba
Alh ibrahim ya katse mata tunani da fadin
"Allah yayi miki Albarka ummulkhair kinyi mana kyauta me matukar tsada, babu abun da zan ce miki se Allah ya saka da Alkhairi, Allah ya sauke ki lafiya"Kwalla ta ciko idon Alh ibrahim ya sa hannun rigarsa ya share. Ya miko wa ummulkhair jakar da ke hannun sa, jakar nan ce da Alh yaje karbowa ranar da umar ya rasu
"Ga wannan jakar kamar sakon ki ne a ciki"
Khairi ta karbi jakar a sanyaye sannan tace
"Nagode"Kunya ta diga ji ga abba ga umma ga kuma sirikin ta, wai sune zasu fada mata zancen cikin da ke jikin ta. Ita de komai nata daban ne da sauran mutane
Ta sa kanta a kasa tana ta wasa da yatsun ta, da Alh ibrahim ya kula kunya take ji se yace da umma
"Mu zamu koma waje, Allah ya kara sauki. Dan Allah a kula da ummulkhair"Umma ta ansa da
"Ba komai Alhaji insha Allah zamu yi iya kokarin mu"Daga haka Abba da Alhaji suka bar dakin. Suna fita khairi ta dago ta kalli umma da ido cike da hawaye
" Dan Allah umma da gaske ciki gare ni?"Umma ta kara yin murmushi
"Ba'a wasa da irin wannan maganar ay, kuma daman jikina ya fada min hakan. Na kula da yadda yanayin ki ya chanza"Khairi de ta kasa cewa komai se zurfin tunanin da ta shiga. She is in a state of denial. Bata taba tsammanin zata dau ciki ba. Tsananin rabon da ke tsakanin ta da umar shi ya kai har akayi musu aure. Rabon nan ne yasa duk da umar yayi nashi dabarun kar ciki ya shiga se da ya shiga. Babu wani dogon bayani illa hikima da kudura ta ubagiji, Allah ya kaddarta zuria tsakanin ta da umar.
Umma ta mike daga bakin gadon da take zaune sannan tace
"Bari na kawo miki kunu, tun safe banga kin ci wani abun ba"
Tana gama fadin haka ta fita daga dakin.Hankalin khairi ya dawo kan jakar da abba ya bata, ta janyo jakar ta tsura mata ido, an fi minti 10 bata bude ba saboda ta kasa, zuciyar ta tayi nauyi sosai saboda bata shirya ganin wani part na umar ba don ze fama mata ciwon rashin sa.
A hankali ta bude jakar. Jakar tana da dan girma a
Ciki akwai babban box se kanana guda biyu se kuma wani envelope daga gani takardu ne a ciki.
Khairi ta bude babban kwalin a hankali. Tana budewa idonta ya kai kan Abayar da ya taba siya mata lokacin da tayi bata jikin ta a office, abayar da ta bar mishi a kan table a lokacin da ta maida masa yaki karba. Anyi mata ninki me kyau a saman abayar akwai note da aka rubuta"I want to see you wearing this again because when you did i couldn't control my heart and feelings. You looked majestic and i would want to see you in it again. maybe for the last time"
Kuka ne me karfi ya kubce mata. Kukan yaci karfin ta har ta dauki Abayar ta rugume katamau a girjin ta tana wani gigitancen kuka me taba zuciya, ta kifa kanta a kan pillow ta ci gaba dayi babu alamun tsayawa. Tabbas Mutuwa tayi musu sauri, mutuwa ta yanke soyayyar da ke tsakanin su, mutuwa tayi musu katsalanda bata bari ya ganta a cikin abayar da yake so ba, uwa uba bata bari yasan ya barta da cikin shi ba"
se da tayi me isarta sannan ta tashi ta bude sauran boxes din. A daya akwai agogo me matukar kyau da tsada dayan kuma cover shoe ne me tsini wanda ze shiga da Abayar. Yana kwance a Asbiti amma har ya iya arranging a kawo masa kayan kano.
Ta maida kayan cikin kwalayen su sannan ta zaro envelope din daga gani takardu ne a ciki. Khairi ta zaro takardun sannan ta fara dubawa.
Takardu ne na dukiyar sa na America da takardun banki na kudaden sa, an maida 'next of kin'da sunan khairi dan haka ko Alh ibrahim be isa ya cire kudin ba tare da yarjewar ta ba.
A wata takarda daban taga wasiya da shi da lawyer sa suka rubuta. Umar ya fadi percentage na dukiyar sa da zaa bada for sadaka da sadakatul jariya, sannan ya cire wani percentage ya mallakawa khairi. Daga nan kuma se ayi rabon gado yadda Addini ya tanadar, dukda masu samun gadon daga khairi se Alhaji ibrahim.
A lokacin da akayi rubutun be san khairi na dauke da ciki ba. Yanzu da aka gane tana da ciki magana ta tashi, idan yaron namiji ne ya cinye gado gaba daya idan kuma mace ce Alh ibrahim yana da share a dukiyar sa.Khairi ta kwanta a gadon ta ci gaba da kuka, bakin cikin ta shine yadda umar be samu wannan joy din zama mahaifi ba. She wish he knew kafin mutuwar sa.
Khairi ta shafi cikin ta da ke nan flat kamar table sannan tace
"Your daddy left us, but he is in a better place insha Allah. Allah ya gafarta maka umar, Allah ya dubi bayanka mijina💔"
Ta fada a hankali kamar me yin rada.🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Abdulkareem ya koma bakin aikin sa bayan kwana biyu da yayi a kano, kamar mara lafiya gaba daya ya zama exhausted daga strees din da ya shiga na mutuwar umar da na maryam da hajja take kokarin kakaba masa. He needs space shiyasa ma ya bar kano ya dawo aiki, sannan yayi alkawarin baze dinga komawa gida ba se bayan wata 1 ko biyu saboda ya kula idan hajja tana ganin shi a ko da yaushe shine zatayi ta kokarin tura mishi maryam. Gwara yayi nesa da ita ko ya samu lafiya.Har a lokacin hoton yadda yaga ummulkhair a gurin taaziya bata bar zuciyar sa ba. Duk yadda yaso ya cire ta a zuciyar sa ya gagara, ganin ta ya rura masa wutar sonta da ke kwance a cikin zuciyar sa. He is guilty na sa matar da bata gama takaba ba, tunanin ta da yake ma haramun ne a gare shi amma ya zeyi da abun da bashi da control a kai.
Ba abun da ze dage da shi a yanzu se addua . Adduan ubagiji ya zaba masa abun da yafi zama alkhairi a rayuwar sa.
🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Bintu. A
09034346763
YOU ARE READING
Sarkakiya
RomanceLabarin tsantsar soyayya me cike da sarkakiya ce ta kullu a tsakanin su. Ummulkhair ta zamo Allura cikin ruwa wanda me rabo ne ze dauka. Shin wa zata zaba a cikin su? Boyayyen masoyi Abdulkareem wanda yayi dakon soyayyar ta na tsahon lokaci ko kuma...