🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Abdulkareem ya bita da kallo har ta bace ma ganin sa cikin fushi ya juyo ya kalli umar wanda shima kallon hanyar da ta bi yayi."kai mugu ne, yanzu me ummulkhair tayi maka"
Ak ya fada tare da hade fuska sannan ya cigaba"Kana jin dadi ne duk sanda ka muzgunawa wani, saboda I don't understand meyasa a kullum burinka ka batawa duk wani wanda ya rabe ka. Yaunzu ma wani lefi tayi maka"
Umar ya dawo da kallon sa kan Ak sannan yace
"Kayi nesa da ita idan baka san kukanta, muddin ka rabe ta to hakan ne zeyi ta faruwa. Ranar har warning kayi min ko to nima ga nawa gargadin. Babu kai babu ummulkhair, i dont share my personal person with anyone"
Ak ji yayi kamar ya rufe shi da duka, don me zece kar ya rabe ta. Bayan shine ma ummulaba'isin zuwan ta company ma. Baze taba yiwu ba.
"Wait and see, se na raba ummulkhair da kai. Se na tabbatar ta dena aiki da kai tunda ba baiwar ka bace. Sannan baka isa ka hana alakata da ummulkhair ba don rayuwar ta ba a hannun ka take ba"
Abudulkareem yana gama fadin haka ya bar mishi gurin, ji yakeyi kamar ya shake shi. Ya dade be ga mutum me bakin hali haka ba. Duk kokarin da zeyi ya raba khairi da office dinsa se yayi. Koda kuwa ummulkhair zata bar yin aiki a company ne baki daya.
Yanzu abunda ya rage masa shine yadda ze bijiro mata da kudirin sa, yadda ze fada mata gaskiyar shine secret admirer. Zeyi kokari ya fada mata tunda yanzu alakarsu tayi karfi a waya. Sannan yayi fatan ta so shi ta karbi kudirin da ze zo mata da shi na aure
Ummulkhair tana komawa office ta ci gaba da kukan, abunda yafi bata mata rai shine yadda ya dizga ta a gaban oga Ak. Ji tayi ta kara tsanar umar sosai, da kyar ta iya tsayar da kukan da take, kana ganin ta kasan ta sha kuka don fuskarta tayi jaa sosai, hanci da kumatun ta sunfi ko ina yin ja.
A hankali taji an bude kofar da ta hada office dinta da na umar, tasan dole umar ne. Tayi mamakin shigowar sa office dinta dan tun ranar farko da ya shigo lokacin su Oga Ak na nan be sake shigowa ba, sede ita ta shiga ta same shi.
Ta ji mutum ya shigo amma ta kasa kallon sa, da sauri ta kai hannunta kan mouse din computer da ke kan table ta fara murzawa, Ita kanta bata san me take yi ba, Da ta kalli fuskarsa gwara tayi kamar aiki takeyi.
Se da yafi minti 10 a tsaye beyi magana ba ita kuma bata dago ba, yi tayi kamar bata san da shigowar wani hallita ba.
Umar yayi gyaran murya sannan yace
"Ba na ce miki ban yarda ki kula kowa a company nan ba"Shiru khairi tayi bata bashi ansa ba dukda yau tayi mamakin yayi mata maganar ba da masifa ba, hasali ma maganar kasa kasa yayi ta.
"Ba magana nakeyi miki ba"
Yanzu kam ya daga muryar sa kadan amma still be kai irin ihun da yake mata ba.A hankali ta dago kai sukayi ido hudu. Ta kauda idon ta daga kallan shi, bata son kallon bakar fuskar sa. Sannan tayi magana
"Ban taba jin inda aka hana mutum magana da dan uwan sa mutum a duniya ba, don kawai ina aiki da kai shikenan se na zama kamar baiwar ka. Ina kokari naga na kiyaye dokokin ka. Ina kokarin shanye duk wulakancin da kake min. Hakan be ishe ka bane. Kayi min tsanar da ban san me nayi maka ba. Bansan lefi na ba.
Wlh duk sanda na shigo office dinnan ji nakeyi kamar ina prison, bani da walwala bani da kwanciyar hankali, ka takura min, ka takurawa rayuwa ta, numfashi me kyau ma bana iya shaka se na bar office dinnan, na tsani zama a cikin sa"Wani zafaffen hawaye ne ya fara zuba daga idon ta daya na bin daya. Ta saka kanta a kan desk ta cigaba da kuka.
Hawayen da umar yaga tayi a kasa yasa jikinsa yayi sanyi. Shiyasa ma ya biyo ta office dinta dukda be san me ze ce mata ba idan ya shigo din. Tun da ya shigo ya ke kallon ta, be taba tsayuwa yayi mata kallon nutsuwa ba se yau. Fuskar ta tayi jaa sosai saboda kukan da tayi. Be san ya akayi ba yaji wani abu ya tsarga masa a zuciya wanda yayi tunanin tausayi ne.
Yau shine yake tausayin wata, be taba jin tausayin wani mutum ba idan banda mamansa sarah ba. Ganin fuskar khairi ya tuno masa da mamansa sarah.Ya tuno idan tayi kuka itama haka fuskar ta takeyin ja sosai abunka da baturiya
Tunda ta fara magana yaji jikinsa ya narke da kalamun ta, maganganunta kamar kibiya ake soka masa musamman gurin da tace duk sanda ta shigo office din ji takeyi kamar prison.
Da kyar ya ja kafarsa ya koma office dinsa, ya zauna a janyo computer sa don yayi aiki amma aikin ya gagara, ya rasa me yake mai dadi.
Bayan kamar awa daya ya tashi kamar an tsunkure shi ya kara komawa office dinta
Yana shiga yaga wayam ba kowa ko jakarta babu, Da alama ta tafi gida. Ya daba agogon hannun sa lokacin karfe 1 na rana.Wunin ranar gaba daya ba a nutsuwa yayi shi ba. Ba yau ya saba saka sakatarorin sa kuka ba amma na khairi yasa shi a wani yanayi, ko dan tayi mishi kama da mamansa ne oho.
Har ya koma gida tunanin ta yakeyi, se ya ga fuskar mamanshi tana kuka se kuma yaga na khairi tana kuka. Hakan ya taso masa da ciwon me zafi da ke kwance a zuciyar sa, Maganganun khairi ma suka dinga masa yawo a kai. Da kyar ya samu yayi bacci
🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Bintu. A
09034346763
YOU ARE READING
Sarkakiya
RomanceLabarin tsantsar soyayya me cike da sarkakiya ce ta kullu a tsakanin su. Ummulkhair ta zamo Allura cikin ruwa wanda me rabo ne ze dauka. Shin wa zata zaba a cikin su? Boyayyen masoyi Abdulkareem wanda yayi dakon soyayyar ta na tsahon lokaci ko kuma...