Sorry

173 12 0
                                    

🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Washegari da safe Umar Yana zaune ya hada kai da jikin table dinsa gaba daya yau a dagule yake. Abubuwa da dama sun sha kansa baya iya tunani me kyau. Yana son ganin khairi duk da be shirya abun da ze ce mata ba
Yana zaunen yaji a kwankwasa kofa wanda yasa yaki wani farin ciki ne ya ziyarci zuciyarsa, be san ya akayi ba se ganin sa yayi a bakin kofa yana kokarin budewa. Ita yake bukatar gani, ita yake son gani.

Wa ze gani yana bude kofar
Jidda

Bacin rai ne ya mamaye dan annurin da ya ziyarci fuskar sa. Beyi tunanin ganin jidda a bakin office dinsa ba tunda a iya sanin sa babu abun da yake hada ta da shi they even started on a wrong foot. Khairi yake ta sa idon gani duk da be san ta yaya ze hada ido da ita ba bayan abun da ya hada su jiya.

Tsayawa yayi a bakin kofar yana jiran ta fadi abunda ya kawo ta.

"Won't you let me in"
Jidda Ta fada tana murmushi

"Say what you want to say and get out of here"
Ya fada fuska a mutuke

"Baza kayi nadamar sauraran abunda nazo maka da shi ba, I promise you"
Tana magana tana kallon sa har cikin ido.

Dogon tsaki ya ja tare da kokarin rufe kofar saboda yaga alamar bata masa lokaci kawai zatayi. Gashi daman yarinyar bata kwanta mishi a rai ba.

Da sauri tayi magana ganin kofar ta kusa rufuwa
"Magana ce akan ummulkhair"

Chak ya tsaya da rufe kofar da yake sannan ya kalle ta sosai. A hankali ya kara bude kofar tare da matsawa daga hanya don ta wuce.
Ko beyi magana ba tasan ya matsa daga jikin kofar don ta shigo. Wani hatsabibin murmushi ta saka sannan ta kara tura kofar ta shige office din zuciyar ta fess.

Kujera ta ja ta zauna tun kafin ya bata izini zama. Maganar ba ta tsayuwa bace shiyasa ma tazo da
wur wuri tare da adduan Allah yasa ta same shi kafin khairi ta karaso office din.

"Ina jin ki"
Ya fada jin tana bata mishi lokaci takeyi

Tayi ajiyar zuciya sannan tace
"I will go straight to the point ba tare da wani kwana kwana ba. Na zo ne don mu hada kai da kai domin cikar burukan mu, Idan nace burin mu ina nufin ka samu ummulkhair na samu Abdulkareem"

Ta dan nisa sannan ta ci gaba
"Na san baka san son da nakeyi ma oga Ak ba. He is the man my heart desire, muradin zuciya ta wanda na dade ina dakon son shi infact my life will not be complete idan ban samu Ak ba. Amma zuwan  Ummulkhairi ta sa katangar karfe a tsakani na da shi don baya ganin kowa se ita"

"Me kike so yanzu"
Umar ya katse ta dan baya son dogon surutu da sharhi

"zamu iya hada kai da kai don yanke relationship din da ke tsakanin Ak da khairi tunda nasan kaima abunda kake so kenan

Nauyayyen ajiyar zuciya yayi sanna yace
"Ya akayi kika san i want ummulkhair"

Murmushi tayi sannan tace
"Duk abun da ya faru jiya a dinner naji kuma na gani, i know everything"

Jiya a wajen dinner Jidda na ganin Ak ya bi su itama ta bi bayan sa. Daga yadda umar ya ja khairi kowa a hall din yasan ba lafiya ba, dadin dadawa Abdulkareem dinta ya bisu dan haka dole itama taje ayi komai a gaban ta.

Labewa tayi ganin lokacin da Ak ya labe shima yan kallon drama da ke faruwa.
Tayi farin ciki sosai da jin confession din umar ko ba komai zata samu hope din Abdulkareem ze iya dawowa gare ta, abun son ta abun kaunar ta. Tayi yakinin umar ze iya kwace khairi saboda yananin strong personality dinshi, kwace goruba a hannun kuturu abu ne me sauki.
Jiya tayi bacci harda munshari saboda abunda ya faru yayi mata dadi sosai.

"How do you want us to do, menene plan dinki"
Umar ya katse mata tunanin da takeyi.

"Bani da wani plan yanzu, all i want yanzu shine goyon bayanka. Plan will eventually come"

Shhhh.....
Umar ya sa yatsansa a kan lebansa yana mata alamar tayi shiru saboda motsin da yaji anayi a office din khairi, a hankali ya tashi cikin sanda yake tafiya har ya kai bakin kofa sannan ya bude shi a hankali.
Khairi ya gani da duster a hannun ta tana goge desk din ta da yayi kura, abunka da lokacin hazo.

Tana daga kai sukayi ido biyu da umar, da sauri ta dauke kanta ta ci gaba da goge table din da takeyi kamar baya gurin.
Da alama bata ji me suke cewa ba, yayi ajiyar zuciya sannan ya juya ya rufe kofar. Ya karaso inda jidda take a zaune sanna yace mata ta tashi ta fita ta dayar kofar saboda baza su iya karasa maganar ba ganin khairi tana office dinta kuma zata iya jiyo su.

Bayan tafiyar jidda Umar ya dauki waya ya kira khairi sannan yace ta shigo office dinshi ta same shi.
Khairi na ajye wayar tayi tsaki sannan ta ci gaba da gyara gyaren da takeyi.

Se da aka shafe kusan minti 30 khairi bata shigo ba, umar ya yanke hukuncin shi ze je ya same ta. Ya tashi da kaimin sa ya nufi office dinta Yana zuwa ya tarar da ita a zaune tana duba wani paper,

yau ma tayi matukar yin kyau, da yake yau ne ranar main event na aniversary wanda zaa fara karfe 11 na safe.
kwalli ne kawai a idon kamar yadda ta saba amma tayi matukar kyau. Atamfa ta saka anyi mata dinkin gown A shape wadda ta sha stones ta ko ina se kyalli takeyi. Dauri ma simple dauri tayi amma yayi mata kyau sosai bare yadda kwantatcen edges din gashin ta ya fito saboda yadda ta ja daurin baya.

Kujerar da ke kallon ta ya ja ya zauna sannan ya kafa mata ido, ita kuwa ta cu gaba da kallon papper hannun ta kamar ma babu wani hallita a gurin.

"Look at me"
Ya fada murya a kausashe me alamun gajiya ko kasawa

Shiru tayi babu answer. Tabbas da yasan haushin sa da take ji da be zo kusa da ita ba, ji takeyi kamar ta wawwaska masa mari.

Ya Fizge papoer daga hannun ta wanda yasa dole ta kalle shi ba don tayi niya ba.

Da sauri ya fara magana
"I don't know why I reacted that way yesterday, ban san me ya shiga kai na ba. Nayi nadaman abun da nayi miki, I regretted every single part of it for that i ....am,......"

Shiru yayi saboda yadda yaji maganar tayi masa nauyi a baki. Be saba ba, yayi dadewar da be san when last ya bawa wani hakuri ba maybe tun yana karami

"I am....."

ya kara yin shiru yana tunani yadda ze fadi sorry, daga karshe de ya dake ta ce
"I am really sorry for what i did and what i said"

Murmushin takaici tayi, a ranta tana tunanin tayaya zata iya son mutumin be iya cewa sorry ba se da kyar,

"You dont have to be, after all ina gama service dina zan bar company nan Nan da wata 2"

Muryar ta yaji wanda beyi tunanin zata tanka masa ba, amma da wannan answer gwara ma bata yi magana ba kwata kwata don answer ta soke shi har cikin rai, alamun ma baya gaban ta kenan

Tana gama fadin haka ta tashi ta barshi a zaune a gurin . tayi ficewar ta daga office din gaba daya dan bata son magana da shi kwata kwata

🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Bintu. A
09034346763

SarkakiyaWhere stories live. Discover now