🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
"Ajye kuliyan nan!!!!"
Maryam tayi ma noor ihu wanda ke rike da mage yana dariya yana kokarin shuna mata.
Maryam akwai tsoron mage, bata son mage a kusa da ita kwata kwata.
Noor jikan hajja ne yaron summayya, yazo hutu gidan shine ya dauko kuliyan makotan su ya shigo da ita yana shunawa maryam dayake yaron akwai kiriniya."Wlh zan dake ka idan ka saka min magen nan a jiki, wai ba magana nake maka ba!!"
Ba abun da noor yake se dariya, idan ta matsa ya bita, shi be saka mata a jiki ba shi be ajye magen ba, haka suka dinga zagaye a gidan.
Abdulkareem ne ya shigo gidan dawowar sa daga masallaci kenan tun daga kofar gida ya yake jiyo ihun maryam da dariyar noor a farfajiayr gidan inda ake parking. Yana shigowa yaga noor yana shunawa maryam mage,
Cikin fada Ak yace da noor"Kai Noor ka ci gidan ku, Aunty naka kake tsoratawa haka"
Noor yana ganin Ak ya saki magen yayi cikin gida da gudu, mage daman ta gama tsorata yana sakin ta tayo kan maryam. Maryam ta saki wata kara tayo kan Abdulkareem a guje, batayi aune ba se ji tayi sunyi karo da Ak, tana bugar sa kafarta ta gurde se jin ta tayi wanwar a kasa.
Ai kuwa maryam ta saki ihu saboda raki.
Ak ya fara salati yana mata sannu, ta bugu sosai ga kafar ta gurde, Ak ya taimaka mata ta tashi tsaye kafa daya a dage.
Tare da cewa
"Yi hakuri taka muje"Maryam ta sa kafar da ta gurde a kasa, wani irin zafi taji da yasa ta kara yin ihu tare da kara dage kafar daga kasa.
Nana da nan ta fara kuka, hawaye ya fara zuba shabe shabe.Ba abun da kukan maryam ya tuno masa se ummulkhair, how can he ever forgets the first he met her. Ko da ya aure khairi ya tabbata weekness dinsa shine ya ga kukan ta.
Da yaga tafiyar wahala take mata se ya sa ta dafa shi suka tawo tana dingisawa har parlou.
A parlor suka tadda hajja akan sallaya tana jan charbi. tana ganin yadda maryam ke dingisawa hankalin ta ya tashi. Ta taso da sari ta karaso inda suke"Maryam me ya faru, me ya same ki"
Ba abun da maryam take se kuka"Ina fitinannan yaron nan yake"
Ak ya fada ran sa a baceHajja tace
"Ina sallah naji ya shigo da gudu yayi daki, noor!!! Noor!!! Kana ina ne?"
Hajja ta fara kwalla masa kira."Barshi hajja bari naje na same shi a dakin"
Ak ya fada tare da zaunar da maryam a kujera sannan ya nufi dakin fuuuu .Ya fito rike da kunnen noor yana ja har parlour, ba abin da noor yake fadi se
"Dan Allah kayi hakuri uncle wlh bazan sake ba"Abdulkareem ya mammake shi sannan yace yayi kneeldown ya bawa maryam hakuri. Noor ya tsugunna ya bata hakuri tare da fadin baze kara ba.
"Tashi ka bawa mutane guri mara kunyan banza, saura na kara gani ko jin kayi wani kiriniyar se na saba maka, kuma ko bayan na tafi zan sa a sanar da ni duk fitinar da kayi, zan dawo ranar na zane ka"
Noor ya tashi zugwi zugwi yana kuka yayi daki.
Hajja tace
"Ka min dai dai dan yaron nan baya ji, basan ya akayi sumayya ta bata shi haka ba, shekarar sa 8 amma ya iya fitina iri iri"Ak ya ci gaba da mita a parlor har yana cewa ze kira summayyar itama yayi mata fadan ya akayi ta bar noor yake kiriniya haka.
Hajja ta bashi hakuri da cewa
"Yaran ne yanzu se Addu'a mutum yana iya kokarin sa amma ka rasa daga ina suke dauko rigima kala kala.Shide ya gama fadan sa sanna ya shiga daki saboda hayaniyar ta hau kan shi, ya bar hajja da maryam a parlor.
Da magrib ya fito ze tafi masallaci kenan ya tarar da hajja tana dannawa maryam kafa da ruwan zafi da towel Kafar ta kumbura tayi sintim, maryam kuwa ta saki baki se ihu take. Abdulkareem yana ganin haka yace hajja ta bar dannawa yana dawowa daga masallaci ze kaita asbiti a duba ko wani abun ne.
YOU ARE READING
Sarkakiya
RomanceLabarin tsantsar soyayya me cike da sarkakiya ce ta kullu a tsakanin su. Ummulkhair ta zamo Allura cikin ruwa wanda me rabo ne ze dauka. Shin wa zata zaba a cikin su? Boyayyen masoyi Abdulkareem wanda yayi dakon soyayyar ta na tsahon lokaci ko kuma...