Aure

172 11 0
                                    

🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Yadda taga rana haka taga dare, ko gyangyadi bata yi ba saboda tashin hankali. Ko sallah asuba se karfe shida ta iya yi. Tun jiya ta kafa wa agogon dakin ta ido tana kallon lokaci, Ji take ina ma duniyar ta tsaya chak kar gari ya waye. Wani abun takaici ma kamar agogon kara gudu yake.

A cikin sujuda tayi ta adduan Allah yasa wani abu ya faru a fasa auren nan. Allah kar ya nuna mata auren nan. Ba dan illata kai haramun bane yau da se ta yi ma kanta lahanin da ze sa a fasa auren nan.

Wayyo Abdulkareem dinta, sede yaji an daura mata aure da umar. Tana tausayin kanta tana tausayin Abdulkareem, ta tabbata baze taba yafe musu ba ita da iyayen ta. Wani zaffafen hawaye ya kara zuba daga idanun ta

Tana zaunen ta kafawa agogo ido umma ta shigo dakin rike da cup din shayi a hannu, Umma tayi ta magana khairi bata ansa ba, bata ma kalli umma ba idon ta yana nan fixed kan agogo.

Umma ta karaci maganar ta khairi tayi kamar bata san akwai wani hallita a dakin ba. Ta na zaune a kasa ta hada tagumi se girgiza kafa take alamun restlessness.
Umma ta ajye cup din shayin ta zauna a kusa da ita sannan tace

" ki dan sha tea dinnan kar ki sa ma kanki wani ciwon daban, ina so na fada miki shi aure kudura ce daga ubangiji. babu yadda zakiyi idan Allah ya kadarta akwai aure tsakanin ki da umar. Ki dauki hakuri da dangana sannan kiyi addua Allah ya kawo miki salama a cikin zuciyar ki, idan ki dauki aure a matsayin bauta ubangiji ze shige miki duk Al'amuran rayuwar ki na gidan aure"

Haka umma tayi ta mata nasiha da bada hakuri hade da lallashi, khairi ko uffan bata ce, duk wannan surutun ba shi take son ji ba. A hankali tace da umma
"Dan Allah ki fita ki barni"

Ba musu umma ta ja kafa ta bar dakin, umma na fita khari ya rufe dakin tasa sakata. Bata son kara ganin kowa ma a duniya. Ta koma ta ci gaba da tagumi.

Karfe 9 dai dai aka daura auren Ummulkhair ishaq da Umar ibrahim mijinyawa a kan sadaki dubu 100, liman ya gama nada aure da mutanen da kwata kwata basu fi 20 ba, masallacin ma ba ango ko abokan ango. Aure ne aka nada kamar na bazawara.

Alh ibrahim se murmushi yake kamar bakin sa ze yage saboda farin ciki. Abba kuwa kana ganin shi kasan a cikin damuwa yake, wadanda suka zo daurin auren se Alhini suke ba abun da zasu iya cewa se Allah ya basu zaman lafiya.
Bayan kamar minti 30 da daura auren magana ta fara yaduwa, wannan fada ma wannan haka har dangi duk aka sani.

A cikin gida kuma kamar gidan mutuwa, daga umma se matar Alh shehu da ta shigo se khairi da ta rufe kanta a daki.
Kiran wayar umma aka dinga yi ana tambayar ta wai dagaske ne an daura auren khairi? Umma har ta rasa bakin da zata ansa. Yan uwanta duk suka hasala suna ganin cin fuska ne da zaayi irin wannan auren sirri yan uwa basu sani ba. Ba abun da umma take se bada hakuri, tana bada hakuri tana hayawe. bata taba tunanin auren khairi yar ta mace tilo ze zo mata da irin wannan tashin hankalin ba.

Aunty maimuna ma ta kira tana fada, wani irin aure ne zaa daura haka cikin gaggawa. Umma tayi ta bata hakuri, aunty m tace tana airport ma yanzu Duk available jirgi da ta samu zata shiga ta taho.

Khairi daman tun jiya ta kashe wayarta saboda tasan Abdulkareem ze kira kuma bata da karfin zuciyar da zata daga, tana ji ana ta shige da fice a cikin gidan yan daurin aure sun dawo, wasu yan uwan da basuyi fushi ba na abba da umma sun fara zuwa. Umma uwar biki ko wanka ma ta kasa yi tana zaune guri daya.

Abba ya dawo ya tarar da umma yace a fara shirya khairi saboda karfe 2 na rana zaa kaita gidanta. Har abba ze tafi umma ta riko babbar rigar sa
"Ban ga umar ba, ko ba da shi aka daura auren ba?

Abba yayi murmushi me ciwo sannan yace
"Maganar nan da nake fada miki umar be san an daura masa aure yau ba, yanzu na bar Abdullah ze raka Alhaji gidan umar. Wayar umar ma a kashe take gaba daya"

SarkakiyaWhere stories live. Discover now