Alkawari ya cika

228 5 0
                                    

🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Yau kam a duniyar nan ina ganin babu wanda ya kai Abdulkareem farin ciki. Ya dibo kayan sa kala 4 duk anyi musu dinkin babbar riga sun sha aiki me kyau ya yo dakin hajja duk da akwai baki a gidan ana ta hada hada,
Hajja na ganin shi da kaya niki niki a hannu ta fashe da dariya.
"Zo zo muje dakin ka kaga akwai mutane a nan"

Hajja ta ja hannun sa suka koma dakin nashi, ya dire kayan a kan gado ya baza su sannan yace
"Hajja zaba min wanda ze fi min kyau, ni na kasa zaba tun jiya"

Hajja ta kara yin dariya.
"To kasa wannan farar tunda kaine ango, kaga fari ze nuna wannan farin cikin da kakeyi"

Ak ya kara wangale baki
"Yauwa hajja shiyasa nake son ki wlh, bari nazo na fara shiri"

Hajja ta watso mishi hararar wasa
"Be se lokacin masallaci yayi ba tukunna, yanzu fa karfe 9 ina ganin 9 dinma bata karasa ba"

Ak yayi dariyar jin kunya
"Wlh gani nake lokacin ma yaki gudu, daren ma ji nayi yayi nisa"

Hajja ta kyalkyale da dariya
"Allah ka shirya mana yaran zamanin nan. dan rashin kunya wato ni kake fadawa Allah Allah kake a daura auren nan ko"

Ak ya sosa keya yana murmushin jin kunya
Hajjja ta ci gaba da dorawa
"To yanzu abokan naka wa ze kai musu abun karyawa, an gama komai da komai ga saddiq baya nan na aike shi. Zo ka tafi ka kai musu saboda naga Alama ma ka manta da ka gayyato abokan ka"

Hajja ta fito daga dakin tana murmushi Ak na biye da ita, suna ta wuce yan uwan da suka zo bikin ana ta gaishe gaisge. Se tsokanar sa suke ana mishi kirarin Ango Ango, ba abun da yake se murmushi kamar bakin sa ze tsage.

Maryam tana kitchen dan ita ta hada ma abokan sa breakfast din. tana jiyo muryar Ak ta shige store da sauri ta rufe saboda bata son ganin shi. . Kuka de kam babu kalar wanda batayi ba, amma idan tana tare da mutane se ta shanye tayi ta kwakulo murmushi dan de ta tabbatar wa da dangin ta itace tace bata son shi.

Ak ya shigo ya kwashe abincin tare da taimakon kanwar shi suka kai mota, daga nan ya fice ya tafi hotel din da abokan sa suka sauka.
A can ma yasha tsokana, abokanai ne tun na secondary wanda an riga an zama daya, yana zuwa ya tarar da abokin sa Ahmad har yasa matarsa ta dafa breakfast ya kai musu.

Ak yaji dadin karamcin da Ahmad yayi masa, gaba daya abokan suka hadu a lounge din hotel din aka baje abincin da ahmad ya kawo da na Ak ana ci ana hira
Ahmad ya kula da Ak baya cin abincin cikin wasa ya ce masa
"My guy kaci abinci fa saboda kana bukartar shi yau"

Ai kuwa ragowar abokan suka tuntsure da dariyar shekiyanci suka bar Ak cikin confusion
"Ban gane me kuke nufi ba"
Ak ya fada yana ware hannu alamun tambayar su

Nan ma suka kara shekewa da dariya, wani abokin sa da ake cewa munkaila yace
"Ina zuwa bari nayi maka dalla dalla"

Ya kamo kunen Ak y rada mishi wani abu wanda yasa Ak ya wangale baki.
Suka kara fashewa da dariya harda tafawa ganin reaction din Ak.

Abun ya bawa Ak dariya, yana dariyar yace
"Ay daman ku duk yan iska ne"

Ahmad yace
"Shiyasa mukayi committee daban daban, akwai yan kai amarya sannan ni da munkaila zamu tafi mu nemo dajjaja bankararre tare da laban saboda abu ya kara armashi. Ni daman madam bata yarda nabi ayarin dauko amarya ba"

Munkaila yace.
"Ka fadawa madam ta kwantar da hankalin ta dan yau ta biya mu da wannan dabga da akayi mana, ko mace bazan bari ka kalla ba"
Suka kara fashewa da dariya
Daga nan suka ci gaba da surutu anayi ana dariya,

Da abdulkareem yaga hankalin su na kan surutun da sukeyi se ya matsa gefe saboda yana son yaji muryar sahibar sa, se da wayar ta tsinke ya kara kira sannan tayi picking da sallama

SarkakiyaWhere stories live. Discover now