Al'ada

184 13 0
                                    

🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Tunda khairi ta shiga gida take jin yanayin ta ya chanza, kafarta tayi nauyi. Tana duba mudubi taga fuskarta ta dan kumbura tasan lokaci yayi, Al'adarta zata iya zuwa ko wani lokaci.

Marar ta fara mata ciwo, ta dafa hulba ta sha dan ta samu sassauci. Abinci ma kadan ta iya ci sannan ta kwanta.
Da asuba ta tashi zatayi sallah tana shiga toilet ta tarar bakon yazo, ta gyara jikin ta tayi wanka sannan ta dawo ta samu guri ta kwanta, marar ta ci gaba da murdawa Bayan lokaci ta samu sassauci har bacci yayi awon gaba da

Kamar a mafarki taji karar waya, da kyar ta iya janyo wayar ta kara a kunne ba tare da ta duba ba don idonta yayi nauyi  dishi dishi ma take gani.

"Assalamu Alaikum"
Tayi sallama da murya a dashe alamun daga bacci ta tashi

"Waalaikissalam, bacci kiki yi ne"

Jin muryar Abdulkareem yasa taji baccin ya yaye daga idonta. ta ciro wayar daga kunen ta don ta tabbatar Abdulkareem dinne.

Sunan Oga Abdulkareem ne kuru kuru a kan screen din wayar, ba shiri ta mike zaune ta fara gyaran murya.

"Na tashi, ina kwana sir"
Ta gaishe shi tana murza idanu

"Lafiya kalau ummulkhair, kin zarce da bacci ne haka, yanzu fa karfe 8:45"

"Dan Allaah??"
Khairi ta fada tana zare ido, nan da nan idon ta ya kai kan agogon da ke manne a bangon dakin, 8:45 dinne yadda ya fada.

Ak ya dan yi murmushi sanan yace
"Yanzu zan fito daga gida, se nayi tunanin kiran ki idan kin shirya se na biyo mu tafi"

Khairi tayi shiru na dan lokaci sannan tace
"Bazan bata maka lokaci ba kuwa"

Da sauri Ak ya katse ta,
"Ban ma yi breakfast ba, nasan kafin na gama kin shirya. Se nazo"

Be bari ta bashi answer ba ya katse wayar saboda baya son ta kara kawo wani excuse din.
Yana kashe wayar murmushi yayi sannan ya kwantar da kansa a kan kujerar motar sa ya rufe ido.

A lokacin ma yana kofar estate dinsu, jin se a lokacin ta tashi yasa yayi mata karyar yanzu ze fito daga gida harda cewa se yayi breakfast. Shida yaronsa Yayi ta rokonsa ya tsaya yayi breakfast din yaki yi, shayin kawai ya kurba sannan ya fito da sauri sauri. Daga maitama zuwa garki ma se anyi minti 20 a hanya.

Da sauri khairi ta shiga toilet ta kara gyara jikinta, daman tayi wanka don haka bata dade ba. Ta bude woredrop tana tunanin abuda zata saka wanda baze dame ta ba. Wani skirt ta dauko me budewa da sweater me dogon hannun, ta dauko dogon jalbab dinta mustard color ta saka.

flat slipers dinta ta zura ta ratayo jaka, har ta kai bakin kofar dakin ta tuno bata sa kwalli ba, da sauri ta koma ta saka kwallin ko tayi kyaun fasali. fuskarta ta kumbura haskenta ya kara fitowa har wani ja ja ja tayi saboda zuwan period dinta.

Ta zaro wayar ta ta kira Abdulkareem ta sanar masa ta gama shiryawa, yace mata shima ya fito gashi nan zuwa nan da 3mins ta fito

Ta fito parlor ta tarar da Aunty M tana yin breakfast fast itama tayi shirin tafiya aiki. Ta gaishe ta sannan ta sanar da ita wannan abokin aikinta da ya dawo da ita jiya shine ya biyo mata zasu tafi.

"Kina ta sauri, ki tsaya kiyi breakfast mana"
Anty maimuna ta fada ganin saurin da take

"Aunty M kar yazo yana jirana. kisan nace miki a gaban layin nan yake ba dadewa zaki ga yazo"
Khairi ta fada tana kokarin daukar Apple din da ke cikin basket a kan table

"Zan dauki apple de" ta fada tare da zura shi a jaka

Aunty M ta kalli me aikin ta sannan tace mata
"Sa mata shayin nan da aka dafa a karamin flask, akwai ragowar meatpie din su salma ki hada mata da shi a pack"

Khairi tayi dariya.
"Yauwa anty M kina ji da ni sosai"

Auntie maimuna ta harare ta
"Dalla can, ni nasan baza ki iya jure rashin abinci ba. idan kin kai office din kya ci"

Zubaida ta shiryo mata abunda aka ce mata a karamar jaka. Khairi ta karba sanan tayi ma Auty M sallama.

"A kula da kyau, Allah ya kiyaye".

Tunda ta kira Abdulkareem cewar ta gama ya gyara zaman sa. Ya maida hular sa da ya cire. Ba lefi shima yayi kyau dan Manyan kaya ya saka dayake juma'a ce. Ajiyar zuciya yayi yayi kokari yayi calming kansa sannan ya zubawa gate din ido.

Ko da ta fito kallon ta yakeyi ta mudubi, baya tunanin akwai ranar da ze gaji da kallon ta, so kenan.
Tana iswowa jikin motar ta kwankwasa masa jikin window a hankali. A tunanin ta be ganta.

Da sauri ya mika hannu ya bude mata kofar motar ta ciki. Khairi ta shiga motar sannan ya ja suka tafi.
Sun fara tafiya sannan ta gaishe shi, ya amsa cike da annashuwa a fuskarsa. Yau ma kamar jiya taki sakewa da shi sunyi magana. ya kula idan ya saci kallon ta yana ganin tana dan yamutsa fuska, kamar wani abun na damunta.

"Akwai abunda ke damun ki ne"
Daga karshe ya samu karfin halin tambayar ta.

"Bana jin dadi ne"
Ummulkhair ta amsa hade da kara yamutsa fuskan

"Subhanallah, sannu, me yake damun ki? ko mu koma gida ne? Kin sha magani?
Tambayoyi ya fara mata wanda be bata daman ansa ko daya ba, yana sauke tambaya daya yake daura wata. Duk yabi ya rude

Khairi ta danyi murmushi ganin yadda ya damu sannan tace
"Ba wani abu bane ina tunanin stress ne, amma Tunda weekend zaa shiga nasan zan warware"

"Ayya sannu. Allah ya sawake, kiyi kokari ku samu ki huta weekend dinnan"
Ya fada fuskarsa duk a dagule, shi de yasan ta fada haka ne amma yasan wani abun ne. Allah yasa ba babban ciwo bane yayi addu'a a ransa.

Tun daga nan ba su kara magana ba, se aikin satar kallon ta da ya samu. Ya tausaya mata yadda yaga har ciza lebe takeyi. Se yanzu ya kula ma har kumbura fuskar tayi, gashi tayi ja kamar an mare ta , Ko shi yasa ma take ta bacci. Ko de shi ya tashe ta batayi niyan zuwa aiki ba yau.
Bini bini se ya ce mata "sannu" ya fada mata sannu yafi cikin charbi, tun tana amsa masa har sannun ya fara bata haushi tayi mishi banza. A haka har suka isa company.

Tun kafin motarsu ta karasa shiga cikin gate din company jidda ta hango shi, abun da ya bata mamaki ganin wata a passenger seat. Daga gani mace ce don hijab din ta hango amma bata ga fuskar ba.

Ba shiri ta kara gudu a mator ta . Ta shigo company a miliyan kamar wadda aka biyo. Tana karasowa tayi parking a dai dai gefen da Abdulkareem Yayi parking, wa zata gani 👀👀. Ummulkhair daro daro a gaban motar Ak. Abdulkareem dinta💔

🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Bintu. A
09034346763

SarkakiyaWhere stories live. Discover now