Alh ibrahim ya bar kano bayan yayi kwana biyu, duk da basu furta sun yafe masa ba haka ya gama borin kunyar sa ya tafi. Ya ajye makudan kudi a jaka da yaje gidan su zuhra yi musu sallama.
Iyaye mazan gidan duk sun rasu (iyayen su zuhra) se kannen su maza 3 da suka rage. Se kuma matansu matayen da duk sun tsufa, se yaya da jikoko da suka cika gidan makil
Tun bayan Alhinin da aka sha umar be samu daman kebewa da khairi ba, duk inda yaje yana zagaye da yan uwa da abokan arziki ana ta zuwa ganin dan zuhra.
Khairi kuwa har yanzu a shock take, gani takeyi karya ne, ta yaya umar ze zama cousin dinta. Wannan wani irin sarkakiyar rayuwa ce. Ko cousin ko ba cosin ba babu abun da ze chanza game da alakar ta da shi, ta san matsayin sa ya tashi daga boss dinta ya koma na dan uwa, dole ta sa wa kan ta son shi a matsayin sa na dan uwan ta amma hakan ba yana nufin zata yarda ta so shi a matsayin saurayiAlakar su da Abdulkareem tana nan tana habaka, duk wannan hayaniyar da akayi ba ta fada ma Ak ba, bata san ta yadda zatayi mishi bayanin umar ya koma dan uwan ta, sannan ta tabbata hankalin shi baze kwanta ba jin wannan labarin.
Ta yanke shawarar idan ya dawo yaji komai tunda daman sun yanke shawarar yana dawowa ze turo magabatan sa don su nema masa iznin auren khairi. Duka su biyun suna ta zumudin dawowar sa.
Umar kuma a dayan hannun yana ta planning yadda ze fada ma dagin sa asalin abun da ya kawo shi kano har ya kai da gano yan uwan sa ne, yana so ya fada musu abun da ke zuciyar sa game da khairi da burin sa na ganin ya aure ta.
Umar Yayi ta facaka da kudi dan se da ya sallami duk yan uwansa da makudan kudi, umar ya zama wani cele a dangi kowa se nan da nan ake da shi, abinci ma se ya zabi na wanda ze ci don haka ake jera masa flasks da abinci kala kala, kowa ya girko ya kawo. Haka yake yini a gidan kakannin shi se dare yake komawa hotel, yadda yake yini haka kowa yake yini a gidan Ayi ta hira ana dariya.
Yan matan dangi kuwa kawacce chaba ado take idan zasu zo saboda ya gani ya kyasa, suyi ta iyayi suna zubar da aji a gaban sa. burin su yace yana son wata a cikin su. Khairi se de tayi dariya a ranta tace baku san waye umar ba shiyasa.
Shi be ma san abun da suke ba don hankalin sa yana kan khairiKo ana hira idon sa yana kan khairi yana kallon duk motsin ta, hakan yana sawa duk ta tsargu. Duk sanda ta dago se sun hada ido da shi wanda ke sa gaban ta ya fadi.
Tana mamakin ganin umar me zafin zuciya ya dawo wani salihi kamar idan aka sa mishi yatsa a baki baze ciza ba. Se take ganin kamar wani umar dinne ba umar din da ta sani ba.
Gashi yayi ta jan ta da hira shi a lallai se ya nuna yayi mata farin sani. Hakan yana sa taji ta kasa sakewa, da yawan lokaci ma se de tayi musu sallama tace ma umma zata je gida tayi musu abinci.Ko gidan taje zuciyar ta na yawan tuno shi, Wani irin abu take ji game da shi da ta kasa tantance menene, Inde so ne Abdulkareem take so for sure amma ta kasa fahimtar sabon yanayin da take ji a kan umar. Tun ranar da suka kwana a office din dss ya samu wani gurbi da matsayi na daban a zuciyar ta wanda take tunanin girmamawa ne
Yau kam cewa tayi baza ta je family house din su ba saboda ta gaji an fi sati ana abu daya. Umma ta yi ma umar bandashen gurasa har tana adduan Allah yasa ya iya ci saboda ta kula baya iya cin abincin gargajiya sosai.
Bayan tafiyar umma gidan ya rage ba kowa se ita kadai ta dauko waya suka fara sana'ar da suka saba ita da Abdulkareem wato video call.
Ak ya fara bata labarin yadda ya je wani restaurant ya tarar da waiter da be iya turanci ba shima Ak be iya french ba. Sukayi ta kwaba shirme kowa yana magana ba wanda yake gane me dayan yake cewa, se da wani mutumi da ya iya turanci ya shiga tsakani sannan ya fassara musu.
Khairi tayi ta dariya jin yadda Ak yake kwantanta french din da waiter ya ke"Ces tes la maison cets voir"
Ak ya fada yana kakkarya harshe, khairi na dariya tace me hakan yake nufi"Ta ina na san me yake fada , kawai ina kwatanta miki abun da yake fada ne"
Khairi tana dariya tace
"To gaskiya se mun kara maka shekara daya, se ka iya french sannan zaka dawo""Inaaaaaa kinsan yadda nake ji na a garin nan kuwa, wlh kamar ina kan kaya. Allah Allah nake Thursday tayi na dawo saboda nayi missing din ki sosai, I really want to see badly"
Ak ya fada yana wani murmushi me kayatarwaKahiri tayi murmushi tare da juya ido
"To ba gani kana kallo ba""Ba irin wannan kallon ba, ina so na ganki a zahiri. I really missed you, bana tunanin idan na dawo Thursday zan iya kwana ban zo na ganki ba. Bazan iya bari se friday ba"
"To wa ya fada maka friday din zaka ganni, ku da zaku zo tambaya ay baza ka samu damar gani ba"
Ak ya dan bata rai irin na wasa tare da fadin
"Haba ya zaki ce haka, zan ganki mana, zance dan Allah abba ya bani damar ganin ki"Khairi ta kyalkyale da dariya
"Lallai abba ze ce Allah ya hada shi da mara kunyan siriki"Suka kwashe da dariya gaba daya. Ak yace
"To shikenan Thursday din zan zo kawai tunda flight dinmu 2 ze iso kano, Zuwa 4 ko 5 Insha Allah zaki ganni"Khairi na dariya tace
"Me yasa ka fiye zumudi ne, Allah ya sa hajja ta hana ka fita ranar"A haka khairi da Ak suka kashe mintuna suna video call cikin shauki da kewar juna. Da kyar suka rabu shima se da khairi tayi ta damun shi zata je ta daura
Girki, be so ba amma haka ya barta tare da cewar se tayi mishi Alkawarin tana gamawa zata kira shi, tace ta yardaTa shiga kitchen ta dafa tuwon shinkafa da miyar taushe wadda taji naman rago, ta zuba komai a flask, ta dauki abincin abba a cikin nashi flask din hade da gurasar da umma tayi ta hada ta kai parlour sannan ta shiga wanka.
Ta fito daga wanka kenan taji ana buruntu a parlour, ta san ita kadai ce a gidan zuciyar ta ta raya mata magen su ce (kuliya) har zata wuce daki se ta tuno bata rufe kwanon gurasar sosai ba kuma kuliyar zata iya shinshinawa koma ta ci, cikin hanzari ta nufi parlour da sauri tana mita a ranta tana cewa 'wata rana se na karya kuliyar nan, ba dama mutum ya ajye abu se ta bi"
Tana bude kofar parlour wa zata gani, —umar zaune a kan kujera yana ta karkada kafa ga alamun damuwa kuru kuru a fuskar sa. Yana ganin ta yayi saurin mikewa
"Yauwa ummulkhair......"
Se da ya fara magana sannan ya lura towel ne a jikin ta ga ruwa duk a skin dinta alamun daga wanka ta fito. Da sauri ya juyar da kansa gefe.Se da khairi taga ya juya sannan ta tuno towel ne a jikinta, bata san lokacin da tayi saki kara ba tare da juyawa da gudu ta koma daki.
Ta ina ya shigo ita da ta rufe kofar gidan da key ma. Wannan abun kunyar da me yayi kama? Ita kan tana yawan yin abun kunya a gaban sa
Ta saka kaya amma ta kasa fitowa ta zauna a bakin gado tana tunanin da wani ido zata kalle shiKofar dakin taji an turo wanda ya sa tayi tsalle ta tashi daga gadon tare da fadin "waye!"
Aminu ne (yayan ta) ya ja tsaki sannan yace
"Nine fa duk kin razana""Yauwa yaya ya Akayi umar ya shigo gidan nan"
"Ni na bude masa, mun hadu a kofar gida muna ta knocking baki bude ba shine na bude da key dina"
Khairi ta sauke ajiyar zuciya sannan tace
"To me ya kawo shi"Aminu ya harere ta
"Ya zaki ce me ya kawo shi nan din ba gidan su bane, kije ma gurin ki yazo"Tasan dole gurin ta ya zo din amma fadar da Aminu yayi ne yasa abun ya kara sinking a kwakwalwar ta, da dukkan alamu da rigima yazo ganin fuskar sa a turbune
Ta tashi jiki a sanyaye ta nufi parlour don taji da me yazo🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Bintu. A
YOU ARE READING
Sarkakiya
RomanceLabarin tsantsar soyayya me cike da sarkakiya ce ta kullu a tsakanin su. Ummulkhair ta zamo Allura cikin ruwa wanda me rabo ne ze dauka. Shin wa zata zaba a cikin su? Boyayyen masoyi Abdulkareem wanda yayi dakon soyayyar ta na tsahon lokaci ko kuma...