Asbiti

157 10 0
                                    

🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Se da ya gaji da tuki sannan ya samu guri yayi parking a bakin titi. Kuka ya fara kamar karamin yaro dan komai ya fita a ransa, baya jin dadin komai a duniya.
Yanzu ya gane Bashi da wanda ze kalla yaji dadi a rayuwar sa, yaji cewar rayuwar sa is worth living, his world came crashing right in front of his eyes.
Se da yaci kuka me isar sa sannan ya fara tunanin a ina ma yake? Yana daga kai yaga signboard din wani private asbiti, beyi wani tunani ba ya rufe mota ya shiga cikin asbitin.

Yana shiga ya tarar da nurse wadda hankalin ta ya tashi da taga yadda idanunsa sukayi luhu luhu sukayi ja. Ta tabbata ba lafiya ba

Umar ya fada mata yana neman doctor saboda yazo a kwantar da shi ne. Da farko nurse din tayi mamaki Daman patient ne yake cewa ze kwata a asbiti ba likita ba. Haka de ta barshi ta tafi ta fadawa doctor.
Likitan yace a shigo da shi office, dr yana ganin shi yasan ba lafiya, ya auna su temperature, jikin sa sanyi kalau. ya auna bp ba wani matsala though de blood pressure sa yayi high kadan amma ba abun damuwa bane. Ya tambayi umar ko akwai inda yake masa ciwo,

Umar ya nuna kirjin sa yana fadin
"Right here dr, right here"
Dr ya dauko stethoscope ya saka a girjin don yaji heart beat, da gaske zuciyar na bugawa da sauri amma ba abun damuwa bane, ko stress ze iya sa haka.

Dr yace masa
"Yallabai kayi hakuri ka saki jikin ka kayi mana bayanin abun da ke damun ka yadda zamu iya taimakon ka"

Umar ya fashe da kuka wanda yasa dr ya zama speechless gaba daya. Cikin kukan umar yace masa
"ku kwantar da ni dan Allah ko zan samu saukin abun da ke damu na, my heart is aching doctor"

Dr ya rasa yadda zeyi da umar saboda ya gane ciwon nasa na dumuwa ne, matsalar da ke damun shi daga social issue ne. Ya rubuta masa mild maganin bacci ya bashi yace ya siya ya sha. Umar yace shi fa ba inda ze je a nan ze kwana
Dr yayi yayi da umar ya tashi ya tafi gida umar ya turje, dole suka hakura aka bashi daki.

Dr ya fada ma nurse ba wani babban abu bane, tasan yadda zata karbi contact din yan uwan sa dan a sanar dasu abun da ake ciki idan yaso washe gari da safe zasu sallame shi ya tafi gida.

Haka umar ya kwanta a gadon asbiti yana kallon ceiling, ko paracetamol baa bashi ba balle a sa mishi drip
Babu yadda nurse bata kada ta raya akan ya bata number yan uwansa ba yaki bayar wa. Da ta ishe shi cewa yayi ta fita ta bashi guri ta ishe shi da surutu. Yan asbitin sunga karfin hali a wajen umar.
Ko da dare yayi umar kasa bacci yayi, yayi ta juye juye har se da aka fara kiraye kirayen sallah asuba sannan ya samu baccin da be wuce na 1hour ba

Washe gari da safe ma likitan yazo cikin lallama akan umar ya tashi ya tafi gida, umar yace be san zance ba.

Har likitan ya tashi ze tafi umar yace masa shi fa har yanzu be ga an bashi magani ba bayan yazo a matsayin mara lafiya, likitan ya tambaya

"Ka samu kayi bacci kuwa"

Umar ya girgiza kai alaman aa sannan ya daura da cewar
"Da zan samu nayi bacci na sati guda ba tare da na farka ba da naji dadi saboda damuwar da take damu na. I don't want yo know where i am"

Jin haka yasa likitan ya kara tsorata da lamarin umar, duk yadda akayi ba karamin damuwa yake ciki ba. ya fito daga dakin ya sa nurse ta bashi maganin bacci ko ya samu bacci duk da be san menene matsalar sa ba

Bayan umar yayi baccin ne nurse ta dauki wayar sa ta kira last call dinsa, daman wayar babu password

Su khairi na zaune duka a parlor suna ta shan hira da abba, kwana biyu umma bata shiga harkar su sosai, yanzun ma tana zaune a parlor amma bata tanka musu ba.
Wayar abba ce tayi ringing yayi picking fuska babu yabo babu fallasa ganin sunan umar a screen. Yana dagawa yaji muryar mace.
Nurse ta gaida abba sannan ta sanar masa me wayar yazo asbitin tun jiya shi kadai kuma anyi anyi ya bada number yan uwa yaki, yanzu ma don yana bacci ne ta kira.

SarkakiyaWhere stories live. Discover now