Sarah

252 15 0
                                    

🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Kwana biyu umar ya samu sasasaucin damuwar sa domin yakan fito farfajiyar gidan ya zauna don ya sha iska

Zaune yake akan kujera yana kallon tsuntsayen da ke ta yawo a sama, daga wannan bishiyar su tsallaka dayar. Garin akwai rana amma saboda yalwar bishiyu yasa gidan yayi inuwa, ga iska ta ko ina. Yana zaune iska na kada shi fuskarsa babu yabo babu fallasa.

Yana zaunen de ya ga me gadi na fitowa da akwatuna daga cikin gidan. Nadiya ce da mamanta suka biyo bayan me gadin da manyan jaka a hanunsu, kallo daya yayi musu ya kawar da kansa. Nadiya ce ta karaso gurin yayan nata ta gaishe shi, ita kuwa mamanta na tsaye tana ta watso ruwan harara ma umar din da be san me take yi ba.

Nadiya ta fada ma yayan nata da turanci cewar zasu je saudiya yin umara daga nan zasu biya turkey sanan su dawo.
Okay kawai ya ce mata, ta dan tsaya ko ze kara yin magana amma beyi ba. Jiki a sanyaye ta koma gurin mummy ta suka nufi gurin parking.
Me gadi ya zuba musu akwatunan su a boot din motar, driver ya ja motar suka bar gidan.

Dogon tunanin umar ya shiga, duk wannan bushashar da akeyi a gidan da dukiyar mamansa SARAH akeyi. Da bazarsa suke rawa daga mahaifin shi har matar sa.
🍒🍒🍒🍒🍒🍒
ASALIN LABARIN

Alhaji Ibrahim mijinyawa asalin mutumin kano ne, iyayensa mutanen RANO ne hausa fulani. Yayi makarantar sa ta secondary a RANO sanan ya dawo cikin kano inda yayi diploma a business administration a kano state polytechnic. A kano ne ya hadu da asalin mahaifiyar umar wadda ta haife shi me suna ZUHRA. Itama mahaifiyarsa a kano aka haife ta. A yadda labari yazo mahaifiyar umar ta rasu yana da shekara 2 a duniya.

Kafin rasuwar nata ne Ibrahim ya hadu da wata baturiya me suna SARAH, yar Atlanta Georgia na kasar AMERICA.  Sarah sunzo yawan bude ido ne da suka saba yi duk karshe shekara tare da iyayenta, sukan zaga kasashen Africa.

Sarah ita kadai ce a wajen iyayen ta. Mahaifin ta MR. COLT ALFRED dan kasuwa ne yana da babban construction company na gine gine a can America.
Tunda sarah ta hadu da ibrahim  a OBUDU cattle ranch dake CROSS RIVERS. taji  ya kwanta mata a rai. Soyayya ce ta kullu me karfi tsakaninsu a tsahon lokacin da zuka zauna a ranch din.

Hutun na su ya kare suka koma America. Takan ruboto masa wasika ta post office, wasikar se yayi wata biyu bata iso ba, shima yana rubuta mata.  Anan ne yake sanar ta ita yana da mata har da yaro ma. tunda taga wasikar hankalinta ya tashi tayi kuka sosai sannan ta hanke hukunci dena tura masa wasika.

Ana cikin wannan yanayin ne ciwon ajali ya kama zuhrah Allah yayi mata rasuwa, ta bar yaronta umar me shekara 2.  Ibrahim yaji mutuwar matar sa matuka. Bayan watatani da rasuwar zuhra ibrahim ya tura ma sarah wasika saboda yaga shirun yayi yawa. A nan ne yake sanar da ita rasuwar matar shi.

Da jin labarin rasuwar matar sa sarah ta kwaso kayan ta se Nigeria. Tazo nigeria da niyar auren ibrahim sanan su tafi america da shi.

Iyayen sa sun so su turje amma haka ibrahim da sarah suka dage da lallashi da bada hakuri har suka amince.

Tunda sarah taga umar jininta ya hadu da shi, tace zata rike shi tamkar danta domin kuwa zatayi adopting dinsa a matsayin nata.
Anyi auren sarah da ibrahim a nan Nigeria sanan suka wuce America. Suna zuwa America ta samawa umar takardun zama cikakken dan kasa sanan akayi cike ciken takardu da ya nuna umar ya zama danta halak malak, ma'ana de tayi adopting dinsa legally.

Rayuwa ce sukayi ta tsantsar soyayya tsakanin ibrahim da sarah duk da de sarah  bata musulunta ba, shima ibrahim be matsa mata se ta musulunta ba tunda Allah ya hallarta masa auren Ahlul kitab.
Ibrahim ya koma makaranta a America inda yayi degree dinsa na farko da na biyu.

Tsantsar soyayya ce ta zahiri wadda babu sirki sarah ta nuna ma umar. Ta dauke shi tamkar dan cikinta da ta haifa. Umar ya tashi cikin ainayin gata na hakika ba irin namu photo copy ba.

Ta sa shi a makarantar boko tare da islamic school a can America. Yadda ibrahim be takura mata a addinin ta ba baza ta takurawa yaronsa akan  addinin da mahaifinsa yake so yayi ba. Tayi kokarin tarbiyar  sa domin har tashin  sa sallah takeyj, wata rana har kwatanta masa takeyi.

Umar yana dan shekara 7 mahaifin sarah ya rasu da heart attack. A will (wasiyya) da ya bari ta yadda zaa raba dukiyar sa. Kashi 50 na matar sa LINDA ne, kashi 30 na yar sa sarah,  sanan kashi 20 na jikokinsa ne. Sarah bata taba haihuwa ba se yaronta guda daya umar

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya cikin jin dadi da kwanciyar hankali. Ibrahim da sarah suka ci gaba da kula da company marigayi Mr colt. Dukiya ta ci gaba da habaka, Ibrahim ya bata shawarar bunkasa company su zuwa wajen America, ya bata shawarar bude branch a Nigeria. Sarah ta yarda da shawarar sa. Ibrahim ya fara shirye shiryen dawowa gida Nigeria don bude company

A lokacin da ibrahim ya dawo Nigeria umar yana da shekara 16. Ya gama high school kenan ya samu admission zuwa college

Ibrahim ya kafa company su a Nigeria. Company se godiyar Allah, Maaikatan company rabinsu turawa ne rabi kuma yan Nigeria ne.
Kusan ko wani lokaci suna magana da sarah ta email yana bata update na yadda abubuwa suke gudana duk da suna da manyan manajoji guda 3 da suke kula musu da company.

A kwana a tashi ibrahim ya shekara 5 a Nigeria ba tare da ya koma america ba. Ko ziyara be kai musu ba. kullum idan sarah tayi complain se ya bata uzirin aiki ne ya hana shi. Sarah ta damu matuka domin se tayi mishi email yafi a girga be mata reply ba.

🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Bintu. A
09034346763

SarkakiyaWhere stories live. Discover now