Iv

178 6 0
                                    

🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Hajja na fita daga dakin Ak ya durkusa kasa ya fara tattaro kayan da hajja ta watsar ya maida cikin ledan su sanna ya zauna a gefen gado yana tunanin lafazin da hajja tayi. Wankan da yayi gidansu khairi ze nufa da zummar ya kai mata kayan tsarabar da ya siya ma zuhra, ba wai cewa zeyi ta fito ba saboda yana ganin hakan be dace ba. Ze aiki yaro ne ya kai kayan gidan shi kuma ya juyo ba tare da ya nemi ganin ta ba. be taba tunanin hajja zata zo neman sa har daki ba shiyasa ya bar kayan a kan gado.

Se da ya shafe mintuna a kan gado daga baya de ya yanke shawarar ze je gidan nasu, ba ganin ta zeyi ba kawai tsaraba ze kai. Ya shirya cikin milk din yadi me laushi an yi masa dinkin short khaftan, ya zura slippers dinsa me dan karin kyau, ya feshe jikin sa da turarruruka masu kanshi.

A kyau kam yayi kyau amma kana kallon fuskar sa zaka gan ta cike da damuwa, Duk fadan da hajja tayi be hana shi tafiya gidan su khairi ba shiyasa zuciyar ta kasa nutsuwa.

Yana zuwa kofar gidan su khair ya fito daga mota ya fara dube duben neman dan aike saboda layin shiru ba yara duk an tafi islamiyya. Gidan su khairi ya chanza gaba daya an gyara shi sosai, lokacin da suka zo taaziya ya san an gyara amma beyi tunanin haka gidan yayi kyau ba.

Can yaga wani yaro yazo wucewa da leda a hannun sa da Alama aiken yaron akayi. yayi saurin tsare shi tare da fadin
"Dan Allah shiga gidan na ka kai wannan sakon ciki"

Yaron ya tsaya turus yace
"To me zan ce idan na kai"

"Kawai kace kayan zuhra ne zasu gane"
Yaron ya karbi kayan yayi knocking gate din, yanzu gate gare su shiyasa suke kullewa se anyi knocking, Ak yana jin yaron ya fara knocking yayi sauri ya koma mota ze tayar ya bar gurin saboda baya son kowa ya ganshi,
Yayi ma motar key taki kawowa,

'ya salaam!! Ya fada a ransa, ya mata cewa battery motar yayi sanyi da be kashe motar ba. Dazu ma da ze fito se da ya dauki battery motar hajja ya tada tashi saboda motar ta dade baa hawanta.

Yayi yayi motar ta tashi taki tashi. Har ya gaji ya ya sa kansa a kan stiring din motar, dago da kan da zeyi ya kula an bude ma yaron gidan har yaron yana nuno direction din shi da dan yatsa. Abun da yake ta tsoro kenan baya son kowa ya ganshi. Yayi sauri ya sunkuyar da kanshi kar ma a gane shi.
Bayan minti kadan yana dagowa ya nemi yaron ya rasa ba kowa a kofar gidan, ya sauke wani nannauyen ajiyar zuciya ya ci gaba da kokarin tada motar sa.
Hankalin shi yana kan motar be kula ba yana kara dagowa se ganin khairi yayi a gaban motar sa.

Subhanallah, nan da nan ya rude ya rasa me zeyi.

Fuskarta babu yabo ba fallasa kallon sa kawai takeyi, sanye take da dogon hijab har kasa. Ta kara haske ta dan yi qiba, kyaunta yana nan se ma karuwa da yayi. He missed her sooooo much.
Khairi ta dan yi murmushi da ya tsaya iya lebe tare da fadin
"Barka da yamma"

Abdulkareem ya sauko daga motar yana kallon ta kamar wani dolo
"Lafiya kalau ya zuhra?

"Zuhra Alhamdulillah an dawo lafiya?"
Khairi ta tambaya tana kokarin saukar da idon ta daga kan shi, har yanzu tana jin kunyar sa

"Lafiya qalau Alhamdulillah"
Ak ya fada a sanyaye. Daga nan kuma se sukayi shiru gaba daya duk sun rasa me ma zasu ce. Bayan minti kadan Abdulkareem yace
"Daman tsarabar zuhra na kawo, i will be on my way now"

"Allah sarki mun gode sosai Allah ya saka da Alkhairi"
Khairi ta fada idon ta a kasa, daga nan suka kara yin shiru, ita bata yi yunkurin komawa gida ba shima be motsa ba, bayan mintuna kadan khairi ta daure tace
"Naga kamar motar na baka matsala ko"

Ak yayi charab yace
"Eh wlh battery ne yayi sanyi saboda ta dade baa hawan ta"

"Zan sa Abdullah ya kawo maka battery se ka tada motar"
Khairi ta fada tare da juyawa zata fara tafiya

SarkakiyaWhere stories live. Discover now