Karshe

320 9 0
                                    

Yana tsaye a jikin mota a lokacin kofar gidan an watse se mutane kadan, motar masu maida yan kawo amarya sun watse.
A hankali ya fara jin sheshekar kuka a bayan shi a cikin wani dan lungu dake jikin gidan inda akayi famfo saboda masu diban ruwa a waje. Ji yayi kukan yaki karewa curiosity yasa ya leka lungun.
A zaune ya ga suffar mace ta hada kai da gwiwa tana kuka. Da farko har ya tsorata tunda gurin da duhu, se kuma ya zaro wayar sa a aljihu ya kunna toch ya haska yarinyar da ke zaune.

Bata ji zuwan mutum ba saboda kukan da take se gani tayi an dallo ta da fitila wanda yasa tayi saurin dagowa a firgece.
Shima me hasa fitilar se da ya firgita tare da fadin
"Subhanallah, lafiya??"
Ya Tambaya

Maryam ta sa hannun ta biyu tana kare hasken fitilar da ke damun ta a ido, da sauri ya kashe fitilar tare da fadin
"Dan Allah kiyi hakuri"

Ta ja tsaki tare da share fuskar ta tana kokarin gyara veil dinta da ya kusa faduwa.
Daga ganin ta yasan itama yar bikince saboda kayan da ta saka. Lace ne me kyau ta saka da veil da takalmin ta high heel, sai dai face dinta babu kwalliya.

Kamar baze yi magana ba se kuma yace
"Nide nasan amarya ce kawai take kuka ranar auren ta. Shima kuma yawanci kukan farin ciki ne, amma ke ba amarya ba kukan me zakiyi?"

Maryam ta bata rai
"To ina ruwan ka da ni"

"Babu kawai ina tambaya ne.
Ya amsa mata

Maryam ta mike tsaye ta fara kokarin fitowa daga lungu inda yake tsaye ya tare mata hanyar wucewa
"Mallam matsa na wuce"

"Naam......"
Ya fada yana kifkifta ido, beji abun da ta fada ba saboda gaba daya idon sa na kanta

"Zan wuce nace"
Ta maimaita.

Yayi saurin matsawa dan ya bata space ta wuce.

ta fito daga lugun zuwa cikin haske, se a lokacin ya tabbatar da gasken kyan da ya gani da ya haska fitila ba na tsoro bane, kyakyawar ce.
Har ta ci gaba da tafiya yace mata
"Afwan dan Allah, zan iya sanin sunan ki?

"Ina ruwan ka da suna na"
Ta fada ba tare da ta juyo ba, ta ci gaba da tafiya

"To atleast ki fada min ta wani bangare kike, bangaren ango ko amarya?"

Maryam ta dakata da tafiyar ta ta juyo ta kalle shi a wulakance
"Saboda me zan fada maka"

"Saboda nasa ta ina zan fara neman ki"
Ya amsa mata tambayar tare da yi mata kayattacen murmushi. Se a lokacin ta ga kamannin shi. Dogon saurayi ne me dan haske.

Maryam ta girgiza kanta sanan ta juya ta ci gaba da tafiya ba tare da ta bashi answer tambayar sa ba. Har ta bace Aminu na kallon ta. Be taba yarda da love at first sight ba se a lokacin. Yaci gaba kallon kofar gidan su Abdulkareem kamar har a lokacin maryam din yake kallo, be ganta ba se fitowar Aunty maimuna
Daman ita tace masa ya kaita saboda bata son bin ayarin yan kai amarya, tafi son ta tafi at her convenience ita da wasu cousins din khairi masu aure guda biyu. Shiyasa ma se da aka fara wastewa sannan suka iso.

Muryar Aunty m ce ta dawo da shi daga shaukin da ya shiga zuwa reality
"Yauwa aminu bude min booth zan dauki su surveniers din da umma tace a kawo".

Aminu Ya taya ta suka dauko buhun surverniers din har bakin gate inda cousin dinshi ta taya Aunty m shiga da kayan cikin gidan. Se leken gidan yake ko Allah ze sa ya kara ganin maryam amma be ganta ba.

A bangaren Abdulkareem ango kuma baki ya kasa rufuwa su Ahmad ne suka dauke shi zuwa yawon neman kaza. Allah Allah yake su dawo da shi gida, su kuwa se yawo suke duk inda aka je se su ce kazar batayi ba. Kamar yayi musu duka haka yaji saboda ya kagu yaje ya ga amaryar sa. Se wajen 9:30 sannan aka gama siyan kaza suka dawo da shi gida tare da niki niki din ledoji cike da kaji, kusan tukubar gaba daya suka siye.

SarkakiyaWhere stories live. Discover now