Tsefe

312 18 0
                                    


Wasa wasa khairi an tsufa a orientation camp dake TSEFE jahar ZAMFARA, ta hadu da mutane kala kala, tayi kawaye da yawa domin ita me  faran faran da mutane ce ga saurin sabo.

A cikin sabbabin kawayen da tayi akwai wadda jininsu yafi haduwa me suna Aisha bature. Aisha bature asalinta yar MINNA ce amma mazauna abuja.

Ta ji dadin zamanta a camp sosai  amma tayi kewar iyayenta da yan uwanta.Kullum a cikin girga kwanakin da ya rage musu a camp take.

Khairi tayi degree dinta a BUK  inda ta karanta accounting. Kawarta aisha bature medicine ta karanta don haka kusan kullum khairi se ta bi kawarta zuwa clinic don ta buya saboda ta tsani zuwa drills.

A kwana a tashi Yau su Ummulkhairi suka fito daga orientation camp. Cike suke da farin ciki, kowa yana murnar komawa gida.
Da safe suka fito da Akwatunan su na tafiya suka fito bakin gate, A kan Jakar kayansu suka zauna suna   jiran motar da zata fito dasu daga TSEFE zuwa tasha. Har ga Allah tasan zatayi missing camp da kawarta aisha Amma zumudin komawa gida ya rinjaye ta

Aisha ta zaro karamin mirror daga purse dinta tana duba fuskarta sannan tace

"camp dinnan ya sa nayi baki wlh. Ga wahalar parade, ga shi a shanya mutane a cikin rana Kamar kilishi"
Ta ci gaba da  banbanin mitar ta ita kadai.

Khairi ta dan mike wuyanta tana so ta hango kanta a mudubin. Aisha tayi sauri ta rufe mudubin da hannun ta

"me zaki gani ne a ciki, ke ay idan kika sha rana jaa kikeyi ba baki ba"
ai kuwa suka tuntsure da dariya. Khairi ta dan hade rai
"Kin fara tsokanar taki kenan"

"kin manta sunan da Adnan yake kiranki ne -jan bado "      
suka kara kwashewa da dariya.

Adnan coper ne da suke shiri sosai a camp din. Idan ya hangota ta dawo daga parade ground ta sha rana fuskar tayi jaa, se ya ce mata jan bado .

"yauwa nikam aisha ya maganar relocation din da zamuyi Saboda gaskiya bazan iya zama a zamfara har shekara daya ba. Nafi son na koma gida kano"
Khairi ta fada da damuwa a fuskar ta

"kar ki damu insha Allah ina komawa zanyi ma uncle dina magana duk yadda ake ciki zan kira na fada miki"

aisha ta kalli wayan da ke hannun khairi ta tabe baki sannan ta ci gaba

"dan Allah kiyi kokari de ki chanza waya kina ta fama da nokia me touch, yanzu  ta ina zaki turo min callup letter taki dan nayi mana processing relocation dinmu"

khairi ta daga wayar tana juyata tana fari da ido.     
"a kyale min baby ta, kin sa min waya a gaba"

Aisha ya ja tsaki.     
"Se kiyi ta fama ana barin ki a baya , bakya sanin abin da duniya take ciki.
kinga dauko callup letter ki nayi snapping saboda kar nazo ina kiranki ki turo kice babu wayan da zaki yi snapping"

khairi ta daga hanchi
"ay bazan rasa wayar da zanyi snapping ba
Tana magana tana duba cikin jakarta don ta dauko callup letter tata. Ta mikawa aisha

"gashi nan har video se kiyi ma"
Aisha ta karbi letter tana kokarin daukan hoton takardar.

Khairi ta dan juya tana kallan titin da ke gaban su. can ta hango mota tana shigowa a hankali saboda titin bashi da kyau. Ta tsurawa motar ido kamar wadda aka bawa aikin kallonta. Ta cigaba da bin motar da kallo har motar tazo gefen inda suke zaune.

A gaba driver ne ke tuka motar se wani katon mutum a gurin me zaman banza yasha bakin glass da bakin suit, a kujerar baya idonta ya kai fuskar da ta kasa mantawa,

Fuskar mutumin da akayi kidnapping. Tabbas shine saboda bazata taba matawa da wannan fuskar ba.

Ta mike zumbur tana ci gaba da kallon motar baki a wangale, kamar ance ma mutumin ya juyo suka hada ido. Idonsa a bushe kamar matattce.
nan da nan ta ji gabanta ya fadi rasss!!!!  Shi kuma ya cigaba da kallonta har motar ta wuce.

Innalillahi wa inna ilaihi rajiun haka ta cigaba da mainatawa a ranta. shikenan tayi gamo, me yake faruwa da ita ne? Mutumin da ta gani a kano me ya kawo shi ZAMFARA. zamfaran ma cikin garin TSEFE. Kode gizo ya fara mata ne.

Aisha bature da ke aikin daukan hoto ta dago kai tana kallon kahiri tana mamakin yadda ta tashi zumbur kamar soja
"lafiyan ki kuwa"
Ta tambaya

Inaaaaa khairi ba ta ita takeyi ba, motar kawai take kallo har suka kule. Aisha bature ce ta kara taba ta

"Kehhh!!! Me ya faru ne, kin sansu ne kike binsu da kallo haka?"

Daga kai kawai khairi tayi  saboda bata san ta inda zata fata mata bayani ba.....

SarkakiyaWhere stories live. Discover now