Shakku

159 8 0
                                    

🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
A take duk wani annurin fuskar sa ta dauke, fuskar ta mamaye da zallan bakin ciki da tashin hankali, tunanin me ya kawo shi gidan su khairi yake. Me ya kawo shi kano ma in the first place?
Cikin zafin nama ya taho gadan gadan gurin da umar yake jingine da motar sa. Kamar ya kai masa naushi amma se ya dakatar da kansa

"Me ya kawo ka nan,"
Ya fada Muryar da kyar take fitowa saboda bacin rai.

Umar yayi wani hatsabibin murmushi sannan yace
"Kai ya kamata na tambaya me ya kawo ka kofar gidan mu"

Baa taba raina masa hakali ba irin na yau cikin ihu Abdulkareem yayi magana
"Get lost , ka bar kofar gidan nan idan har kana son kanka da arziki kuma kana so ka bar garin nan da body parts din ka intact"

Umar ya sheke da wani irin dariya me sa takaici.
Kafin ya budi baki yayi magana suka ji muryar abba a bayan su

"Lafiya naga kunyi chirko chirko a nan, Aa umar ya baka shiga ciki ba kuka tsaya a waje"

Abba ya dawo daga masallaci lokacin, tun daga nesa ya ga motar umar a parke yayi tunanin ma ya shiga gidan se da ya karaso ya ga umar din ya fito daga motar suna magana da wani saurayin

Umar yayi murmushi sannan yace
"Yanzu zan shiga abba, ina yini"
Ya dan rusuna yana gaishe shi

"Lafiya mu shiga ciki mu gaisa sosai"

Abdulkareem kasa motsi yayi kuma, daga ganin dattijon yasan baban khairi ne saboda yadda suke kama da khairi ' me yake gani ne? kode mafarki yake? Umar ya zama dan gida ne da ake masa iso ciki? Yaushe ma umar din ya san baban khairi.
Tambayoyi ne suka cika kwakwalwarsa wanda yake bukatar answer da wurwuri.

Har abba ya gota ya kula da Abdulkareem beyi magana ba, abba yayi ma Ak sallama wanda yasa Ak ya dawo cikin hayyacin sa

"Waalaikassalam"
Ak ya amsa tare da durkusawa har kasa yana gaishe da abba

"Barka da Rana Alhaji"
Abba ya amsa cikin jin dadi ganin yadda saurayin ya tsugunna masa

"Tashi tashi, akwai datti a gurin"
Abba ya mika masa hannu akan suyi musabaha"

Ak ya dago ya mika masa hannu suka gaisa amma ya dan durkusa na girmamawa.

Abba ya juya ya kalli umar
"Abokin ka ne umar?"

Da sauri Ak yace
" ahh..... gurin ummulkhair nazo"

Abba yayi murmushi irin na manya da dukkan Alamu shine wanda akace zasu zo tambaya gobe, sanna yace
" to shikenan"

abba ya sake juyawa ya kalli umar
"Umar mu je ko"
"To abba"
Umar ya taho yana wani tafiyar tinkaho yana kallon Ak tare da yin wani murmushin keta.

Ak kuwa ji yayi kamar ya shako shi ya nana da kasa, he needs urgent answer.
Haka abba da umar suka jera suka shiga cikin gidan.

Bayan tafiyar su Ak ya dauko waya ya kira ummulkhair
"Ina kofar gida"
Ya fada murya cikin bacin rai ita kanta khairi se da ta lura da bacin ran sa

Tana fitowa tsakar gida taci karo da umar, gaban ta yayi mumunar faduwa. Yanzu ta gane dalilin da yasa Ak yayi mata magana da wannan lafazin, se ta ji jikinta yayi yamm kamar mara lafiya. Falon da ta gyarawa Ak ma tasan umar zaa sauke a ciki.

Ta fito kofar gida jiki a sanyaye, tana ganin fuskar Ak gaban ta ya kara faduwa saboda babu annuri a fuskar

"Me ya kawo umar gidan ku?
Tambayar da ya fara mata tun kafin su gaisa, fuskar a turbune

Kahiri ta fara kame kame
"Umm labarin ne da tsaho dole se mun zauna"

"Ban gane se mun zauna ba, why is umar in your house!!"
Ya fada da lafazin masifa Yanzu kam hakurin shi ya fara gazawa

"Maganar baza ta yu a tsaye ba se mun samu gurin zama"

Ak ya koma mota ya bude mata kofar me zaman banza sannan yace Bismillah

Khairi ta zagaya ta zauna a cikin motar tare da fito da kafafuwan ta waje, shi kuma Ak ta tsaya a gabanta tare da sa hannun sa ya jingina da jikin kofar mota, bashi da nutsuwar da ze iya zama ma

Khairi ta kwashe duk labarin abun da ya faru daga office din ss har zuwan umar kano har yadda alakarau take da umar.

Ak ji yayi kamar kansa ze fashe saboda zafi, har wani jiri ya fara ji saboda tashin hankali. Wannan shine an rabu da bukar an haifi habu, yana murnar ta bar Abuja gaba daya ashe ba'a nan gizo yake saka ba.

Se maimata "Allahuma ajirni fi musibati" yake. yau umar ya zama masifar da ke neman ruguza rayuwar jin dadin da yake mafarki. Duk wannan murnar da yake ta koma ciki

Da murya kamar zeyi kuka Ak yace da khairi
"Ummulkhair na fara jin tsoro kuma, ina tsoron ranar da zaa ce baza a bani ke ba se dan uwan ki. Ban san ina zan daura raina ba idan hakan ta faru"

Khairi ta ja dogon numfashi sannan tace
"Dan Allah kar ka daga hankalin ka akan abunda be faru ba tukunna. Ni na san abba baze taba min auren dole ba, zabi na ze nema kuma kai ne zabi na"

Ita kanta hankalin ta ba'a kwance yake ba, tana tsoron hakan zata iya faruwa, amma gwara ta kawntar ma da Ak hankali duk da nata hankalin ba'a kwance yake ba.

Abdulkareem yayi ajiyar zuciya
"To shikenan mu dage da addu'a kawai Allah ya tabbatar mana da mafi alkhairi ya cika mana burin mu"

Khairi ta amsa da ameen sannan ta daura
"Yau ga mutanen paris sun dawo amma banji ana ta barin french ba"
Ta fada da lafazin tsokana duk dan ta kaudar masa da hankali akan matsalar da ke tukarar su gaba daya

"Idan nayi you will surely fall in love with me over again"

Khairi tayi dariya
"Allah ko, to shikenan ina sauraro i want to fall again"

Gaba daya sukayi dariya duk da dariyar bata kai har zuci ba, fake dariya ne saboda su kwantarwa da juna rai.
Sukayi ta hira a haka, daga baya yace mata ze tafi saboda zuciyar sa ba'a nutse take ba.
ya bata tsarabar da ya kawo mata. Itama ta shiga ta fito da snacks da kunun ayan da tayi mishi ya tafi da su.

Da kyar de suka rabu akan gobe idan Allah ya kaimu zasu zo da magabatan shi karfe 4 na yamma

Ko da ta koma gida daki ta wuce, umar yana cikin parlour da Abba da umma ana ta hira, sadaf sadaf ta shige saboda kar wani ya ji motsin ta bare ace tazo su gaisa. Se bayan sallar isha da ta tabbatar ya bar gidan sannan ta fito, ko da ta fito hirar gaba daya akan umar ake, magana daya biyu se an ce umar. Ji tayi zuciyar ta na zafi ta koma daki tayi shirin kwanciya.

Shima Ak haka ya koma gida zuciya a dagule se tunani kala kala yake. Ya shiga shakku Zuciyarsa ta kasa nutsuwa gaba daya

🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Bintu. A
09034346763

SarkakiyaWhere stories live. Discover now