Night call

169 9 0
                                    

🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
A kwance take a gado tayi rigingine tana danna wayar ta. dare ya fara nisa lokacin karfe 11 na dare sun gama waya da Abdulkareem kenan. Abubuwan da suka faru a ranar se dawo mata sukeyi, tana mamakin yadda rayuwar ta take neman chanza salo.
Gaba daya events din anniversary da akayi ya sata a physical and emotional stress, event din kwana uku amma abubuwan da suka faru a cikin kwana ukun nan sun chanza abubuwa da yawa

Wayarta ce tayi ringing, da farko tayi tunanin Abdulkareem ne, tana dagawa taga number ce wadda bata sani ba Kamar baza ta daga ba saboda dare ya riga yayi amma ta daga da sallama.

Se da tayi sallama sau biyu sannan ya ansa. Tana jin muryar ta gane umar ne, ranar da ya kira ta a tasha batayi saving number sa ba. Da ta san shine ba lallai ta daga ba.

Da kyar ta daure gaishe shi sannan ta ci gaba da cewa
"Lafiya ka kira ni a daren nan"
Ta fada murya a dashe

"Ina son magana da ke ne shiyasa na kira"
Shima ya ansa da lafazin da tayi mishi murya a disashe

"Ina jin ka"

Umar yaja Dogon numfashi sanan yace
"i just want to hear your voice"

Khairi ta Tabe baki a ranta tace 'ka wahala' amma a zihiri tace
"To ni bacci zanyi se da safe

"Kiyi baccin ki amma kar ki kashe wayar"

Ta kara tabe baki sannan ta ajye wayar a can gefe, a ranta tana fadin 'kai ka sani Credit dinka ne ze kare, idan ka gaji ka kashe wayar'

Ta tashi ta danyi buruntun ta. Ta kai ta kawo a cikin dakin tana shirye shiryen bacci. Duk buruntun da takeyi yana jin ta har ta gama komai ta kwanta.
Ko kara duba wayar batayi ba ta ja bargo ta lulluba se bacci

Tun yana jin motsin ta har ya dena ji, gurin yayi shiru da alama tayi bacci. Hakan be sa yayi tunanin ya kashe wayar ba. Yasan yau da kyar ya iya yin bacci me dadi duba da abun da ya faru. Gwara yayi ta sauraron wayar duk da ba maganar zatayi ba

Wayar tana sa yaji kamar tana kusa da shi wanda hakan yake saukar masa da wani nutsuwa.
Yafi awa yana sauraron shiru kafin daga baya shima bacci ya dauke shi. Haka suka kwana wayar tana yi kamar ba credit ake ci ba

Se da aka fara kiraye kirayen sallaar asuba sannan ya farka. Wayar sa ya fara dubawa yaga har a lokacin wayar tana yi bata kashe ba. Murmushi yayi sannan yace

"good morning babe" a fili
Yasan ba lallai ta tashi ba. imagining yakeyi gashi ga ta, irin tare suka kwana
Ya katse wayar saboda baya son tasan ya bar wayar har asuba sannan Ya tashi yayi yan nafilfilu sannan ya wuce massalaci don yin sallar asuba.

🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Abdulkareem yana fitowa daga motar sa yaci karo da jidda a parking lot inda tayi parking tata motar tana jiran karasowar sa.

Da fara'a ta gashe shi, shima ya daure ya maida mata da fara'ar duk da mood dinsa se a hankali dan dazu yaje gidan su khairi yayi ta kiran wayar ta batayi picking ba, ya jira ko ze ga futowar ta amma be ganta ba. Daga karshe de yayi concluding gudun sa take, haka ya ja mota a sanyaue ya bar kofar gidan nasu.

"Ya gajiyar taro"
Jidda ta tambayeshi tare da karasowa jikin motar sa. shi kuma ya bude motar kenan yana kokarin fitowa

"Lafiya kalau, ya gajiyar ki"
Ya amsa bayan ya fito daga mota

"Yau ina mutuniyar taka"
Ta tambaya tana masa kallon tuhuma.

"Wa kenan?"
Ya maida mata tambaya da wata tambayar

"Ummulkhair ishaq nake nufi
Ta kira sunan ta in full dan yasan ba se yayi mata wani kwana kwana ba.

Murmushi ya saka me kayatarwa tare da shafa keya, yasan ta rafko shi kawai. Hakan yasa zuciyar jidda ta fara kuna

"Me yasa kike tambayar ta"

"Saboda abun da ke tsakanin ku"
Ta fada a fusace zuciyar ta har tana kuna.

"Kar de mutane sun sani?"
Ak ya tambaya yana zare ido tare da kallon gefe da gefe yana dubawa kar wani ya ji su.

be san kara bata mata rai yake yi ba amma ta daure ta danne zuciyar ta da ta tuna abun da ya kawo ta.
Shi kuwa Ak be san tana yi ba don ba nutsuwa yayi ya kalli fuskarta ba

Murmushi ta kwakulo sannan tace
"Aa ba kowa ya sani ba amma idan kuka cigaba da abunda kuke kowa ze sani kam"

"Allah ko jidda"

"Da gaske, sede wani hanzari ba gudu ba"
Jidda ta dan dakata kamar me dogon nazari

"Me ya faru, menene"
Ak ya tambaya muryarsa da alamun damuwa a ciki

"Bana son aji mutuwar sarki a baki na"

"Dan Allah ki dena ja min rai ki fada min"
Ya fada idanun sa har sun fara kadawa

"Kasan MD yana son ummulkhair"

Ak yayi wani ajiyar zuciya tare da jan karamin tsaki sannan yace
"Na sani, haukar sa kawai yakeyi amma ita ba son shi take ba"

Jidda tayi wani murmushin keta har tana tafa hannu

"Wa ya fada maka. Amma kasan ummulkhair ta yarda zatayi dating dinsa......."
Kafin ta gama rufe bakin ta ya katse ta

"Whattt!!! No no no "
Ya fada tare da girgiza kanshi in disbelief sannan ya cigaba

"Khairi bazatayi haka ba, Ban san a ina kika ji wannan labarin ba amma ko waye ya fada miki ya fadi karya. I repeat this is not true"

Jidda ta tuntsure da dariya sannan tace.
"Allah ko? To shikenan kar gaba kace ban fada maka. Wait and see.

Tana gama fadin haka ta juya ta barshi a tsaye zuciyar ta fess, farin ciki fal a cikin ta Fuskarta cike da fara'a.

"Inde ina nan bazan taba bari ku zauna lafiya ba"
Ta fada a cikin ranta tare da fadada murmushin ta

🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Bintu. A
09034346763

SarkakiyaWhere stories live. Discover now