Mari

158 8 0
                                    

Abdullah yana gaban mota yana directing hanya ma driver. ALH ibrahim yana baya yana kokarin gane hanyar gidan ko dan gaba. Suna zuwa gidan me gadin ya wangale musu kofa ganin Abdullah tunda ya san shi, driver yayi parking sannan suka fito gaba daya.

Tsohon gida ne na GRA irin na turawa, gidan yana da yalwar fili babba me dauke da bishiyu kala kala da flowers iri iri. Asalin cikin gidan karamin flat ne a gefe me dauke da 3 bed rooms da 1 parlor, se kitchen da laundary

Abdullah yayi ta knocking a kofar parlor baa bude ba har ya fara tunanin ko umar din baya nan, se da suka shafe mintuna a tsaye sannan suka ji muryar umar a kasalance yana tambayar waye

Abdullah yace
"Ni ne, Abdullah ne"
Daman umma takan aiko Abdullah ya kawo mishi abinci. be kara tsayawa bata lokaci ba ya bude kofar. Yana budewa yaga Alh ibrahim a bayan Abdullah. Nana da nan bacin rai ya ziyarci fuskar sa

"Me ya kawo ka gida na"
Ya fada da kyar

Alh ibrahim ya kalli Abdullah
"Je ka mal habu ya maida ka gida, nagode sosai"

Abdullah ya amsa da "to" ya nufi inda sukayi parking yana mamakin lafazin da umar yayi ma mahaifin nasa magana

Alh ibrahim ya ce da umar
"Won't you invite me in"

Kamar umar zeyi magana se kuma ya fasa ya karkata daga jikin kofar don Alhaji ya wuce ba tare da yayi magana ba

Alh ya shigo cikin gidan yana kalle kalle, gidan yayi kacha kacha kamar ba mutum ke kwana a gidan ba, packs din su fast food duk a kasa wanda yaci ya zubar. Ba abunda yake ci se junk food.
Alhaji ya tsugunna ya dauki park din kfc chicken da ke kasa yana kallo, ya juyo ya kalli umar

"Amma kasan junk food is not good for your health"

Umar ya karaso inda baban shi yake ya karbe takardar daga hannun sa tare da fadin
"Ba abun da ya shafe ka da health dina, just say what you wanted to say a leave please"

Alhaji ya matsar da tarkacen kayan da suke kan kujera sannan ya zauna. Yasa hannu a aljihu ya fito da kullin goro da Alawa ya ajye a kan center table.
"Na kawo maka goron daurin auren ka ne"

"Aure kuma? Waye yayi aure"
Umar ya tambaya da mamaki

Alhaji ya ja dogon numfashi sannan yace
Auren ka Kai da ummulkhair"

"Ummulkhairi kuma????"
Umar yayi ta nanatawa in disbelief, yaji abun banbarakwai kamar almara, wani zazzafan gumi ya karyo mishi. Cikin tsananin rudani ya fara magana

"Idan ma wasa kake kayi aborting mission din nan, na fada maka i never wanted to get married, ku bar ta a auri wanda take so. Ni na dade da hakura da maganar nan. Idan ma abun da kuke shirin yi ne to ku dakata bana bukatar aure yanzu"

Alhaji ya kara yin ajiyar zuciya sannan yace
"Bakin Alkalami ya bushe saboda yanzu daga wajen daurin auren ka nake. An daura muku aure da ummulkhair dazun zan"

Umar jin kanshi yayi ya sara, tabbas yasan babanshi baze masa irin wannan wasan ba. Ya shiga wani irin rudani har kafarsa ta kasa daukar gangan jikinsa saboda shock
Umar ya sulale a gurin ya fara kuka
"You have ruined her life, I always wanted her to be happy, i never wanted to force her into marrying me. Da gaske ina so na aure ta a baya amma banda yanzu, not in a situation like this, she will hate me for life. Idan har da gaske kake anyi auren nan to ni a shirye nake na sawwake mata a yanzu ba se anjima ba"

Kan Alhaji ya kulle ' to wai shi umar me yake so a rayuwar sa ne, shi baa taba yi masa daidai ba kenan?Wani irin baudadden mutum ne haka

Cikin bacin rai Alhaji yace
" Umar me kake so a rayuwar ka ne, you hate me to the extent da ko abun da kake so idan nayi maka se ya zama bacin rai. I am your father not your enemy i will always do whats best for you"

SarkakiyaWhere stories live. Discover now