Alfarma

157 8 0
                                    

🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Washe gari labarin umar yana asbiti ya bazu a dangi, akai ta tururuwa zuwa gaishe shi a asbiti. wani cousin din umma me kaikayin baki ya nemi number Alh ibrhaim ya kira ya fada masa saboda neman gidin zama. Hankalin Alh ibrahim ya tashi jin umar a asbiti. Ya kira umma a waya don yaji abun da ya samu umar. Umma cikin jin kunya ta zayyanawa Alh ibrahim komai, Alh ibrahim yasan umar na son khairi amma be san Abdulkareem yana son khairi ba shima.

Alh ibrahim ya kira doctor don yaji me ya samu umar din, Dr iliyasa yayi ma Alh ibrahim bayanin ba wani abu bane kawai hysteria ne yake damun sa

ALH ibrahim cikin mamaki yace
"Dr menene hysteria kuma?kasan yaren nake se ku"

Dr ilyasu yayi dariya sannan yace
"Condition ne da mutanen da ke da damuwa suke fakewa da ciwo saboda su samu abun da suke so. A takaice de patient ze yi karya ko yayi exergerating ciwo saboda ya tada ma yan uwanshi hankali domin a biya masa bukatar sa"

Alh ibrahim yayi dariya sosai sannan yace da dr
"Ba komai dr ku ci gaba da rike shi idan hakan yake so. Duk lokacin da ya gaji da kafar shi ze tafi. Kar ka damu i will cover all the bills"

har dr ilyasu zeyi magana Alh Ibrahim ya dakatar da shi da fadin
"Turo min acct number in fara tura maka wani abu"

Kudi da yawa Alhaji ya turawa dr iliyasa, se ranar ya dada tabbatarwa umar dan gata ne, umar ya kwana dubu ma inde irin kudin nan zaa turo

Yan gidan su khairi kullum se sun je asbitin se dare suke dawowa, khairi ma kullum tana asbitin ba dan ta so ba, gashi yana ganin umma se ya fara langwabewa ita kuma tayi ta biye mishi.

Saboda takaici khairi ji take kamar ta rufe shi da duka wata rana.
zaman asbitin da take baya barin ta tayi waya da Ak yadda ya kamata. Shima Ak yana mamakin yadda a kwana biyu ta shiga busy haka, ta de yi mishi karyar uncle dinta ne ba lafiya kullum suna asbiti. Hankalinsa ya kasa kwanciya tunda yasan umar yana kano har yanzu. Amma ya ze yi tunda khairi bata nuna masa akwai wata matsala ba.

Yana nan yana shirye shiye a gefen sa, har ya fara tara lefe saboda yana son idan ya dawo karshen wata a kai kudi sannan a sa rana da baze wuce wata biyu ba. kanwar sa sumayya ce take siyo kayan tana tarawa a wajen ta

A kwana a tashi seda umar yayi kwana 8 a asbiti, asbitin da Ko paracetamol ba'a bashi. Khairi ta yi hamdala ga ubangiji ranar da aka sallami umar. Ko ba komai Allah ya raba ta da azababben kallon sa na tsiya.
Umar ya koma gidan da ya siya a hotoro CBN quaters dan bashi da ranar komawa abuja. Kusan kullum se umma ta je gurin umar kai mishi abinci, idan bata je ba zata tura Aminu ko Abdullah.

Bayan kwana biyu da dawowar umar daga asbiti se jin labarin ya koma asbitin har an kwantar da shi a karo na biyu su umma suka ji. Kowa se da yayi mamaki saboda kowa ya san ba wani ciwon azo a gani yake ba. Khairi ma dariyar takaici tayi a ranta tana cewa lallai umar ya iya kisisina.

Kullum se anyi rikici da ita gurin zuwa asbiti, wata rana taje wata rana ta ki zuwa, wani lokacin abba ne yake goya mata baya yace baza ta ba tunda iya alakar yan uwantaka ne tsakanin su. umma tayi ta banbami a gida tana mita abba baya biye mata. Se da umar ya kara yin sati a asbiti sannan aka sallamo shi.

A bangaren Abdulkareem kuwa shar da shi. weekend dinnan ze dawo saboda zuwa gidan su khairi kai kudi da sa rana. Yana ta murnar ze zo ya ga khairi saboda office din gaba daya babu dadi tun da ta bar shi.
Tunda ya dawo aiki yake gudun abun da ze hada shi da jidda, baya son ganin ta saboda abun da tayi ma khairi, ta wani bangaren abun da ya faru yayi favoring dinsa dan ta dalilin haka manya sun shiga maganar aure tsakanin shi da khairi, Ta wani fanni kuma idan ya tuno tashin hankalin da khairi ta fuskanta se ya ji jidda ta fitar masa a rai.

Ita kanta jidda se da ta sha jinin jikin ta, tana san haduwa da Ak tayi mishi bayanin abun da ya faru tare da bashi hakuri amma tana shakkar sa. Saboda duk lokacin da sukayi clash fuskarsa a daure take kuma ko ta gaishe shi baya amsawa se de ya wuce, tayi kuka tayi kuka har ta godewa Allah.

🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Ranar laraba da daddare abba na zaune a parlor Alh ibrahim ya kira sa a waya ya sanar dashi yazo kano kuma yana so su hadu suyi magana cikin sirri, maganar da baya so kowa ya ji. shiyasa ma baze iya zuwa gidan ba dan ko zarah baya so ta sani.

Abba yace ze zo ya same shi a hotel din da yake suyi maganar, Ya ce ma zarah ze fita baze dade ba.
umma tayi mamakin fitar tashi saboda tasan duk inda akayi magrib baya zuwa ko ina se masallaci.

Ya fito ya tari adaidaita sahu se hotel din da Alh ibrahim ya sauka. Alh ibrahim yayi masa iso har cikin daki, Bayan yan gaishe gaishe Alhaji ya fara bayanin Alfarmar da yake so Abba yayi mishi

Sun dau kusan awa 2 suna tattaunawa sannan daga bisani abba yayi ma Alh ibrahim sallama ya fito jiki a sanyaye. Ko da ya dawo gida daki ya wuce ya kwanta saboda damuwar da ta addabe shi sanadiyar tattaunawar da sukayi da Alh ibrahim.

Washe gari ma Abba a dagule ya tashi, be sake anyi wasa da dariya da shi ba yadda aka saba kafin ya fita ba hadali da wuri ma ya fita saboda kar kowa ya gane damuwar da yake ciki kuma be dawo gidan ba se bayan isha.

A bangaren Abdulkareem kuma yana ta zumudin zuwan sa kano yau juma'a. Zaa zo kawo kudi da sa rana ranar Asabar.
Khairi ma se shirye shirye take, daman kwana biyu ba zama take ba kullum tana hanyar kasuwa siyan kayan kitchen. umma ma ta saduda ta sauko tana nata yan shirye shiryen, inde khair matar Abdulkareem ce babu yadda zatayi se anyi auren bata isa ta ja da hukuncin ubangiji ba. Case din yayarta zuhra ya ishe ta i-shara

Abdulkareem yace ba se sunyi komai ba tunda a apartment dinsa na abuja akwai komai na gida sede abun da baza a rasa ba. kitchen din namiji baze taba zama daya da na mace ba shiyasa Abba ya bata kudi take dan siyan kayan kitchen a hankali. Sannan abba ya kudurce kafin auren ze yi ma khairi kayan gado set daya a saka a dayan dakin saboda baya san nan gaba ayi ma yar sa gori.

Alh shehu da abba suka jera zuwa masallacin juma'a. A hanyar su ta dawowa Alh shehu cikin farin ciki yace da abba

"Munyi magana da Alh wada, suna so gobe idan Allah yasa sun zo a sa auren nan da wata biyu, ya kake gani Alh ishaq?

Nan da nan fuskar abba ta chanza, bacin rai ne ko damuwa ne? Allahu A'alam. Abba ya sauke nauyayyen ajiyar zuciya sannan yace
"Alh daman ina son muyi magana da kai yau akan maganar zuwan su Alh wada. Bana tunanin auren nan zai yu gaskiya, ban san ta ina zan fara basu hakuri ba"

Cikin mamaki da bacin rai Alh shehu yayi magana
"Haba Alh ishaq ya zaka maida mu kananan mutane, yaushe yaushe muka ce mun basu dama yanzu kuma zaka ce an janye. Me yayi tsanani haka? Ko shi yaron yayi wani lefin ne?

"Ba daya Alh, larura ce ta taso da yasa babu yadda na iya dole mu hakura da maganar auren nan.

Abba ya kwashe duk yadda sukayi da Alhaji ibrahim ya fada ma Alh shehu sannan ya dora da

"Nasan duniya zatayi min kallon me son kai, amma wallahi nayi tunani, nayi tunanin amma banga mafita a cikin wannan sarkakiyar ba. Ina son khairi ta auri zabin ta amma ina tausayin umar. Ni kaina a matsayi na uba zan iya yin abun da Alh ibrahim yayi idan har umar dana ne"

Abba ya dan matse kwallar da ta fito masa sannan ya kalli Alh shehu.
"Nasan ba lallai ka fahimci dalilin da ya sa har na amince da bukatar Alh ibrahim ba. Dalilin baze wuce soyayya da uba ke ma yayan sa ba"

Shi kansa Alh shehu se da jikin shi yayi sanyi jin abun da abba ya fada, ya kasa tofa komai, se girgiza kai yake cikin tausayawa daga bisani yace

"To yanzu ya zakayi da ummulkhair, da bakin ka ka fada min ba umar take so ba Abdulkareem take so"

Abba ya kara sauke ajiyar zuciya sannan yace
"Wallahi da abun nan nake kwana nake tashi tun ranar da na hadu da Alh ibrahim. Ban san da wani baki zan fada ma khairi an fasa auren ta da Abdulkareem ba da umar za'ayi, sannan a yadda Alh ibrahim yake so auren kar ya wuce nan da sati daya. Wannan maganar da nake fada maka ko zarah bata sani ba. daga Alh ibrahim , sai ni , sai kai muka san zancen auren nan, shi kanshi umar be san da maganar auren ba tukunna"

Alh shehu yayi shiru yana nazari, haka suka ci gaba da tattauna matsalar da ta tunkaro su har suka isa gida. A kofar gidan ma se da suka fi awa suna magana sannan daga bisani suka yanke shawarar Alh shehu ze kira Alh wada ya basu hakuri akan maganar auren Abdulkareem da ummulkhair.

🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Bintu. A
09034346763

SarkakiyaWhere stories live. Discover now