Alhaji Audu 2

175 12 0
                                    

🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Tun bayan abunda ya hada ta da Alh Audu a kitchen take taka tsantsan dashi, daga taji shigowar sa take shigewa daki bata bari su hudu. Allah Allah take su inna asabe su dawo daga kano duk da sunce kwana 10 zasuyi.

Yau ake kwana na 5 amma duk gidan ya fita a  kanta, ji takeyi kamar a kan kaya take. Saadatu ma ta lura da hakan, itama abun yayi mata dadi yadda khairi take gudun sa. Mace dole tasan halin mijinta balle na Alh Audu da a fili yake nuna maitar sa

Yau kam be yi sallama ba ya shigo gidan da sanda kamar barawo. Ita kuma ta fito falo zata saka wayar ta a chaji.
Tana ganin sa gabanta ya fadi tasan be cika dawowa da wuri ba shiyasa tayi mamakin ganin sa a wannan lokacin. Da sauri ta gaishe shi sannan ta nufi hanyar daki

"Ummulkhairi"
Ya kira sunan ta a hankali sannan ya ci gaba
"Naga alama kina gudu na ne a gidan nan"

Nan ma bata ce komai ba sannan ya dore

"Sa'a tana daki ne?
Ya tambaya

Eh tace masa sannan tayi daki da sauri,
Tana shiga daki ta kwanta a gado ta fara tunani.
Secret admirer, ita de tana jin dadin message dinsa amma daga ranar da ta gane mal jabir ne se ya fita a zuciyar ta. Amma kuma yanzu da ya dena mata message se take jin ba dadi. Tayi missing din messages dinsa sosai

Tana cikin wannan tunanin ne message ya shigo wayar ta, tana dubawa taga silver construction.
Message ne akayi mata na interview da zaayi ranar monday. Ita bata taba tuananin ma aikin na gaskiya bane don ta manta ma tayi applying

Tana duba address din taga GARKI 2 Abuja.
Dankari kenan, tasan babu wanda ze barta tayi aiki a abuja ma. Allah Allah iyayen ta suke ta gama service din ta dawo gida.

Ta dauki waya ta kira abban ta don ta fada masa domin tasan shine ze fada mata abunda ya dace sannan duk abinda ya yanke shi zata bi

Abba ya daga suka gaisa, bayan sun taba hira ne ta Bijiro masa da maganar

"Abba nayi applying wani aiki ne a nan abuja kuma sun kira ni yin interview"

"Aiki kuma ummu, wani irin aiki?"
Abban ya tambaya da mamaki a muryar sa

Khairi ta fada masa sunan company da adress dinsu sannan ta ci gaba da cewa

"Wlh abba ban san abun na gaske bane se yanzu da suka tura min message din interview, bansan me zanyi ba shiyasa na kira na fada maka"

Abba ya ja dogon numfashi sannan yace

"Toohh ummu, bansan ma me zance ba. Zamuyi shawara da maman ki duk abunda muka yanke zaki ji."

Sukayi sallama da abban nata sannan ta ci gaba da tuanin me ze zame mata maslaha, aiki a abuja ne ko kuma ta koma gida kano ta nimi wani aikin a can.

Ta ci gaba da kwanciya har akayi sallah magrib sannsn tayi sallah. Tana fita falo ta tarar da saadatu tana kallo a falo.

"Kin fito ne uwar daki"
Saadatu ta fada tana dariya

"Eh wlh kema naji ki shiru yau baki fito ba. Ko kukan khalifa (jaririn da saadatu ta haifa)  ban ji ba"

"Ga khalifa nan baya jin dadi ne. Nima din tun dazu nake ciwon kai"

"Ayya sannu, Allah ya sawake" khairi ta fada sannan ta karbi khalifa daga hannun saa ta zauna, daga nan sukayi ta hira har akayi sallah isha suka ci abinci. Wajen karfe tara da rabi na dare saadatu tayi mata sallama suka shiga dakinsu don suyi barci. Daman yaran saadatu guda biyun sun bi su inna asabe kano

Itama khairi ta shiga daki don tayi barci, gata da saurin bacci nan da nan bacci ya dauke ta

Tana cikin bacci taji kamar ana taba kafar ta, amma se abun yazo mata kamar mafarki. Khairi akwai nauyin bacci don se ayi party a dakin da take bata san anayi ba.

Haka ta dinga ji kamar ana shafa ta ta ko ina, cikin magagin barci ta bude idonta da sukayi nauyi  tana kokarin tashi zaune taga me ke faruwa. Alh audu ta gani kurukuru hannun sa a kan cinyarta.
Ihun da ta kurma ne yasa yayi  saurin saka hannu sa ya toshe mata baki. Da murya kasa kasa yace

"Mene haka, kiyi shiru mana"

Kokarin kwacewa tayi daga rukon da yayi mata da yadda ya toshe mata baki.

"Kiyi shiru mana, ba wani abu zan miki ba"
Ya fada yana kokarin daga mata riga sama.

Wayyo Allah, da ace da wuka a hannun ta yau kam se de uwarsa ta haifi wani, se de duk abunda ze faru ya faru. Wani karfi taji a jikinta da duk kankanta Allah ya bata nasarar kwacewa daga rukon da Alh audu yayi mata ta kwasa da gudu se falo Tunda gidan mu hadu a falo ne.

Tana shiga falon taga saadatu ta nufo dakin ta da sauri domin taji kamar ihun ta.

Turus tayi a gaban saadatu tana haki, tana kokarin maida numfashi

Alh audu da ya biyo bayanta a guje shima turus din yayi da ya ga saadatu a gabansa.

Kallon kallo aka fara yi a falon duk da tashin hankali a fuskokinsu

🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Bintu. A
09034346763

SarkakiyaWhere stories live. Discover now