🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Bayan sati daya da interview din su khairi aka turo mata email na anyi accepting dinta ta zo ta karasa service dinta a company. Da murna ta kira abban ta take fada masa abun da ya faru. Abba yayi mata adduan Allah yasa hakan ne yafi alkhairi. Umma ma tayi murna domin hankalinta yafi kwanciya idan tana gidan kanwarta maimuna.Ita kanta Ummulkhairi tayi murna duk da batayi zaton zasu dauke ta ba bayan abun da ya faru a reception a gaban mutane da yawa. Yanzu de finally zata bar ushafa gaba daya. Zata bar gidan inna asabe. Zata dena ganin babban makiyin ta Alh audu.
Da sassafe ta shira se bwari domin ta gama processing komawar ta cikin gari.
Tun a bakin gate ta hango mal jabir yana shiga da machine dinsa cikin makarata. Ta tsaya ta kare masa kallo, tabbas bashi da aibu Amma zuciyar ta bata kwata da shi a matsayin masoyi ba.
Shima yana hangota yayi saurin shigewa makarantar dan baya son wani abu ya hada shi da ita don be san da wani manufa take masa mugayen kallo ba.Ta isa office din principal tayi mata bayanin zata bar makarantar. Da farko principal taji babu dadi amma daga baya ta mata fatan alkhairi.
Ta shiga staff room domin yi ma sauran malaman sallama. Ta gaishe su sannan ta fada musu cewar zata bar makarantar ne gaba daya. Basu so haka ba amma haka suma sukayi mata fatan alkhairi.Ko da ta kalli mal jabir rubutun sa ma yakeyi a cikin littafi, a ranta har wani dariyar mugunta take masa.
' ba kai Romeo ba, zanga wa zaka ci gaba da rainawa hankali' ta fada a cikin ranta.Dama da biyu ta shigo staff room din dan taga yaya zeyi. Da mamakin ta be damu da sallamar da take yi ba hasali ma yi yayi kamar bata gurin.
Haka ta bar makarantar zuciyar ta fess. Allah yayi zata bar abunda ze hada ta da Gidan inna asabe da Alh audu, Daman kuma a satin tayi ta sintirin zuwa secretariat inda take clearance domin ta nemi a chanza mata gurin PPA. Duk da bata san zata samu aikin ba amma ta san dole se ta bar bwari koma menene.
Straight ta wuce secretariat domin ta karasa process dinta na barin LGA din.Bayan ta gama wannan kujuba kujiban gida ta dawo domin ta huta, ko ushafa gidan inna asabe bata je ba saboda har hanzu bata samu karfin komawa unguwar ba.
🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒Tunda Abdulkareem ya samu labarin daukar Ummulkhairi a aiki ya kasa zaune ya kasa tsaye don murna. Burinsa ya cika, yanzu zata kasance kusa da shi. Ko da be iya mata magana ba da farko yasan sannu a hankali ze samu damar yi mata magana daga nan har su kulla alakar da yake son ta kaisu har ga aure.
Jiya monday ya kamata sababbin maaikatan su fara zuwa aiki amma bata zo ba.
Yauma haka yayi ta dube dube ko ze ganta amma be ganta ba. Hakannan ya hakura ya koma office zuciyar sa cike da kunci.Khari tana isa office din tayi ma receptionist bayanin sabuwar copper ce da zata fara aiki a company. Receptionist din ta gane ta sarai domin ita tayi mata magana lokacin da suka samu sabani da umar,
"Zauna a can zan kira ki"
Receptionist din ta nuna mata gurin zama sannan ta dauki waya tayi kira"Ummulkhairi ta zo"
Abinda ta fada a wayar kenan sannan ta ajye. Bayan kamar minti 5 se ga jidda ta iso farfajiyar reception din. Tun daga saman bene take kallon khairi. Kallon kwakwaf, kallon Wacece Ummulkhairi nan tunda bata taba ganin ta ba.
Direct gurin da khairi take zaune ta je.
Murmushi ta sakar mata sannan tace"Ummulkhair???"
"Yes"
Khairi ta answer tare da murmushi itamaJidda ta mika mata hannu sukayi musabaha sannan tace mata ta biyo ta.
Khairi ta bi bayanta sannan suka nufi wani office da ke kusa da reception din.
Office ne tangameme me yalwa da maikata sun kar 10 a ciki kowa da desk dinsa. Maaikatan suka gaishe da jidda sannan jidda ta ce"Na kawo muku sabuwar colleague ne, sunanta Ummulkhair. Daga yau zata dinga aiki tare da ku, sabuwa ce game da aikin da fatan zaku bata goyon baya da taimaka mata a duk inda wani abu ya shige mata duhu"
Maikatan da ke office din suka answer da "yes ma"
Ta juya ta kalli khairi sannan tayi mata nuni da wani empty desk
"Ga desk dinki can"
Khairi ta wuce sum sum, gaba daya maikatan suka bita da ido. Murmushi tayi musu har ta isa desk dinta.Jidda ta kalli mr Patric wanda shine head a office din sannan tace
"I will leave her to you"
🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Bintu. A
YOU ARE READING
Sarkakiya
RomanceLabarin tsantsar soyayya me cike da sarkakiya ce ta kullu a tsakanin su. Ummulkhair ta zamo Allura cikin ruwa wanda me rabo ne ze dauka. Shin wa zata zaba a cikin su? Boyayyen masoyi Abdulkareem wanda yayi dakon soyayyar ta na tsahon lokaci ko kuma...