Rejection

153 7 0
                                    

🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Tun daga ranar da aka zo tambaya gidan su khairi bata kara samun kwanciyar hankali a gidan ba saboda mitar umma, ta hada khairi da kawaye da yan uwa suyi mata magana akan ta yarda da auren umar, Ita kuwa khairi ta sa taurin kai saboda babu wanda ze juya mata ra'ayin ta. Fada da mita babu wanda umma batayi ba amma khairi tayi kunnen uwar shegu.

Abba ma tun ranar be sake tofa wani abu a kan maganar ba, umma tayi ta mita baya biye mata, Idan ya gaji ma bar mata gidan yake.
shi kansa abba ya rasa hukuncin da ze yanke.
Bincike de an gama shi kuma baa samu wani abun aibu a tattare da Abdulkareem ba, ba dan maganar umar da ta bullo ba da tuni abba ya basu go ahead an fara shirye shiryen kawo kudi da sa rana, amma maganar umar tasa ya kasa gaba ya kasa baya.

Su ma su Abdulkareem jira suke suji an neme su amma shiru ba wanda ya kira gashi har anyi sati biyu, duk da de sunyi tunanin binciken ze iya daukar lokaci shiyasa basu damu sosai ba.

Abdulkareem ya koma abuja bakin aikin sa amma alakar su da khairi na nan se kara karfi da take. Ko da wasa khairi bata taba nuna masa akwai matsala ba, idan ma yayi sensing damuwa se ta kwantar masa da hankali cewar kar ya damu Insha Allah babu wata matsala

A gefen goga umar shiru kake jin sa, ya koma ya labe a hotel saboda yasan abun da ya aikata, baya zuwa gidan kakanin nasa ma balle gidan su khairi. Yan uwa se kiran shi suke sana taya sa murna, suna dada jaddada masa inde khairi ce kar ya damu ya samu. Amma maganar su batayi wani tasiri sosai a wajen sa ba tunda yasan me bashi auren khairi har yanzu beyi magana ba.

Tun ranar da yaje ya sanar ma abba kudirin sa abban yace ya dakata tukunna ze tambayi khairi sannan yayi shawara daga baya ze neme shi ya sanar da shi duk yadda ake ciki, har yanzu shiru yake ji.
Sukan yi waya da umma amma kunya tana hana ta tayi masa maganar khairi, shima kuma yana jin nauyin ya tambaye ta.
A duk lokacin da yayi magana da umma se yaji kamar da maman sa yake saboda yadda suke tsananin kama da umma.

Tsoron kiran khairi yake yi saboda yasan ba lalle tayi picking ba, idan ma ta daga ya tabbata ba magana me dadi ze ji daga bakinta ba, shima baze ga lefin ta ba tunda shi ya janyo koma me zata fada masa.

Har yanzu be koma abuja ba dan baya son ya bar kano har se ya san menene matsayar sa.
Ba ya so ayi ma khairi dole a auren sa yafi son taji tana son sa sannan ta aminta da auren shi da karan kanta. amma da dukkan alamu idan ya tsaya sanya za ta kubce masa. Babban burinshi shine kar a aminta da Ak balle har a kai ga maganar aure.

Yafi san a mance da maganar auren gaba daya shi kuma a hankali se yayi kokarin cusawa khairi son sa a cikin zuciyar ta. He will be the most luckiest person idan khairi zata so shi ko da kwatan kwatan kwatan yadda yake son ta ne, yana neman wannan son a idonta wanda ya kasa gani se ma kallon tsana da yaga take masa wani lokacin

Khairi kuwa addu'a take Allah yasa umar ya fita daga sabgar ta. Akwai ranar da taje taron suna na cousin din ta da duk dangi an hadu. Khairi bata je sunan ba ma se gab magrib, tayi mamakin yadda zancen ta da umar ya zaga dangi. Duk inda ta zauna tana tashi zaa kafa maganar ta.

Yan matan family kamar zasu cinye ta da kallon tsana, bakin ciki da hassada suke mata ganin inde kyaun ne suma suna da shi dan Babu abun da khairi zata nuna musu, Wasu a ciki ma sun fi khairi kyau nesa ba kusa ba.
akwai wata cousin dinta da ta kasa rike bakin cikin ta se da ta nuna a fili . Khairi na zaune a inda yan matan suke ta fara yar da mata maganar banza a fakaice, daga karshe ta kasa hakuri kuru kuru tayi mata magana
Nana ta dafa kafadar khairi tace

" daman ina ta son tambayar ki, ni kam wani malami ne yayi miki aiki akan yaya umar? gaskiya aikin shi yana kyau Ya kamata ma ki kara masu kudi ma"

Ragowar yan matan suka kwashe da dariya har da tafawa. Khairi ma ta bi su sukayi dariya har dariyar ta tafi tasu kara, se sukayi shiru suna kallon ta da mamaki.
khairi tace
"Ni wlh kin bani dariya. Wlh inde akwai malamin da ze juya son da umar yake min ya koma kanki ni zan biya kudin aikin ma, idan haka ta faru ki rubuta ki ajye se na zuba ruwa a kasa na sha saboda murna"

Nana ta mike cikin fishi ta nuna wa khairi dan yatsa
"Kar ki fada min magana mana Wa zaki raina wa hankali"

Khairi ta mike tana dariya tace
"Allah ya huci zuciyar ki, Ni banga abun fada akan abun da na yar a kasa nace bana so ba, dauka kawai zakiyi daman yau kika saba tsintar kwance a kasa ba"
Daga haka khairi ta wuce ta bata guri ta bar nana kamar zata fashe saboda bakin ciki
Wannan kenan

Bayan kwana biyu Alh shehu ya tare abba bayan sun dawo masallaci ya fada masa su Alh wada sun kira suna kara tunin neman su da aka ce za'ayi kuma sun ji shiru. Abba ya bawa Alh shehu hakuri sannan yayi masa alkawarin washe gari duk shawarar da ya yanke ze fada masa.
Yana zuwa gida ya kira khairi ya kara tambayar ta, khairi ta jaddada masa Abdulkareem take so, Kwata kwata bata son umar kuma bata sha'awar auren sa.

Washe gari abba ya samu Alh shehu ya fada masa cewar ya kira su Alh wada ya sanar musu An amince , zasu iya ci gaba da process din neman auren tunda an amince masa. Shi kansa Alh shehu yaji dadin wannan labarin. Da farin ciki ya kira Alh wada ya sanar masa.

Ko da labarin ya kai kunnen hajja tayi farin ciki matuka, burin ta a duniya be wuce Ak yayi aure ba. shi kuwa gogan naku ji yayi kamar ya zuba ruwa a kasa ya sha don murna, gani yake kamar ma ya auri khairi an wuce gurin.
Fargabar da yake ya ragu da kaso 50 cikin 100 sauran kuma se ranar da aka daura masa aure da khairi ze dena fargaba. Har sujudur shukur yayi bayan Alh wada ya kira ya masa Albishir

A bangaren khairi kuwa murna babu irin wanda batayi ba. Ta dawo walwala a gidan kamar ba abun da ya dame ta, umma kuwa ji tayi kamar ta kama daga khairi har abban ta zane.
🍒🍒🍒🍒🍒🍒

Washe gari Abba ya kira umar yace yazo ya same shi a gida, umar ya taho jiki a sanyaye saboda be san me abba ze fada masa ba. It is either good or bad news. Da yazo gidan umma kasa fita tayi su gaisa saboda bata san da wani ido zata kalle shi ba. Zata so ace ta cika masa burin auren khairi a matsayin ta na uwa a gare shi.

Bayan yan gaishe gaishe abba yayi gyaran murya sannan ya fara magana
"Ba wani abun yasa na kira ka ba illa na fada maka shawarar da muka yanke amma da farko ina me baka hakuri da abun da zaka ji na fada, ba haka naso ba amma babu yadda zan yi"

Abba yaja dogon numfashi sannan ya ci gaba
"Munyi magana da ummu ta fada min wanda take so ni kuma bana son nayi mata dole. Wlh umar zan so ka auri khairi saboda kai ma da ne a guri na. Ni me iya shigewa gaba ne wajen nema maka aure a ko ina a fadin duniya, amma kasan dan yau ba'a iya masa."

Abba ya ci gaba da magana da bada hakuri hade da nasiha amma abun mamaki umar be san me yake fada ba ma, tun daga lokacin da abba yace 'da farko ina me baka hakuri" tun daga nan ya dena fahimtar komai. Ji yayi brain dinsa ta kulle har duhu yake gani. Ya tabbata da a tsaye yake jiri ne ze kwashe shi ya fadi kasa. Zuciyar sa se bugu take kamar ya kwana yana gudu.

Abba ya gama surutun sa amma umar be iya motsi ba kwata kwata se ido da yake kiftawa kamar wanda abu ya fadawa ido.
Shi kansa abba se da ya tausayawa umar ganin yanayin da ya shiga. Shima ze so khairi ta auri umar din to amma baze iya forcing dinta ta auri mutumin da bata so ba. Auren dole baya cikin tsarin rayuwar da ze dora yaransa a kai.

Abba ya tashi sum sum ya bar wa umar falon, umar se gumi yake duk da fankar dake parlour.
Se da ya shafe awa daya a hakan sannan daga bisani ya tashi jiki a mace ya fita ya shiga mota ya zuga a guje ya bar kofar gidan.

Tafiya yake a mota be san inda yake ba, titi kawai ya mika duk kwanar da yaga tayi masa ya sha ya kara zurar motar. Shi ba dan gari ba amma se kutsa kai yake ba tare da lissafi ba. Tukin da yakeyi babu nutsuwa kwata kwata a ciki. Duk wanda yake biye da shi a baya sede yayi fatan Allah ya raba su lafiya saboda tukin babu kan gado.

🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Bintu. A
09034346763

SarkakiyaWhere stories live. Discover now