Tafiya

171 10 0
                                    

🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Tun dawowar umar estate  khairi ta kasa sukuni, se ya daidaci lokacin fitowar ta daga gida shima yake fitowa sai de kawai tayi kicibus da mutum a corridor, da kyar take iya gaishe shi murya ciki ciki Sannan ta wuce ta barshi
Abdulkareem kuwa dole ta san hanyar da tayi ta bashi hakuri ya dena zuwa daukar ta tun ranar da sukayi wani karamin drama a kofar gida lokacin Ak ya zo daukar  ta umar ya kafa ya tsare baza ta shiga motar Ak ba se de ta shiga tasa motar.

Se a lokacin Abdulkareem ya san umar ya dawo estate dinsu da zama. Dawowar tasa ba karamin bata masa rai yayi ba yadda yaga da gaske umar so yake ya raba shi da abun kaunar sa.

Abunda basu sani ba daga abdulkareem har khairi shine umar baya kwana a gidan da sassafe yake zuwa ya shiga apartment din daga yaki khairi zata fito shima se ya fito da zummar tafiya aiki, haka da yamma ma tana barin office yake biyo ta. Kusan a tare suke shiga gidan.
Se kuma bayan magrib yake barin estate din ya dawo gidan su.

Duk wannan abun yayi ne saboda ya hana Abdulkareem daukar ta a mota zuwa gurin aiki ko ya dawo da ita gida. Hakar sa ta cimma ruwa domin Abdulkareem ya dena zuwa daukar ta duk da shima ba yarda zatayi ta bishi ba. Ta gwammaci tayi bolt ya kaita gurin aiki.

A gurin aiki ma be barta ta huta ba se ya kira ta office dinsa yace tayi aiki a wajen. Tana aiki shi kuma yana aikin kallon ta. yana yawan hana ta tafiya da wuri, Se tayi mita har ta  gaji ta koma magiyar sannan yake barin ta. Shiyasa ma take yawan saka face mask don ta rufe fuskarta daga tsananin kallon da yake addabarta da shi.

Shi kuwa rufe fuskar da takeyi be dame shi sosai ba muddin ze ga kyawawan fararen idanuwan ta. Shikam ze ji dadin kasancewa da ita ko da inuwar ta ne.

Yau ma tana fitowa ta tarar da shi a bakin kofar apartment dinsa a tsaye ya jingina bayansa a jikin bango tare da nannade hannayen sa a girji. Umar yana da tsaho dai dai musali amma be kai Abdulkareem ba, me samun tsayin Abdulkareem ko a maza se an tona. Yayi kyau sosai saboda dan manyan kaya ya saka wanda akayi  mishi dinkin south south simple amma yayi kyau. Zata iya kirga lokacin da ta ganshi da manyan kaya, yawanci  se kananan kaya ko three quater ma.

Kallo daya tayi mishi taji gaban ta ya fadi, da sauri ta dauke idon ta daga kallon sa. Wani lokacin tana son yi mishi rashin kunya amma takan kasa musamman idan ya tsare ta da ido.

"Ina kwana"
Ta gaishe shi murya ciki ciki, idan ba shi da yasan hakan take gaishe shi baza ka ce tayi magana ba.

"Hope you slept well"

"Alhamdulillah"
Ta ansa a takaice

Ta daga kafa ta fara tafiya ya dakatar da ita

"I want us to talk"
Ya fada fuska babu yabo ba fallasa

Kamar ta kurma ihu, to maganar me zasuyi ne wai
"Ina jinka"
Ta ansa ba dan ta so ba

"har yanzu bakiyi taking relationship dinmu serious ba"
Ya ja dogon numfashi sannan ya ci gaba

"Kinsa cewar saboda ke ne silver construction is still standing, saboda ke nayi considering abubuwa da yawa, saboda ke nayi abandoning plans dina, saboda ke nake zaune a kasar nan har yanzu."

Khairi tayi shiru tana jin maganganun sa tana tunowa da yadda ta yarda zata bashi damar yayi dating din ta.  Ita kam har ta manta da hakan, dayake ko a lokacin ba har cikin ranta ta amince masa ba

Maganar sa ce ta katse mata tunani
"Yau ina so mu tafi office tare"
Ya fada fuska babu alamun wasa

Khairi ta kasa cewa komai saboda jikinta yayi laushi sosai, bata san da wani baki zata ce baza ta bishi ba.
Ganin bata bashi answer ba kuma bata tafi ba yasa ya nuna mata hanya

"Bismillah"

A hankali ta ja kafarta kamar wanda kwai ya fashewa  a ciki. Umar ya sata a wani yanayi me wahala, bakin ta nason ya furta  baza ta bishi ba amma kafarta jan ta take

Suna zuwa bakin motar  ya bude mata kofar ta shiga jiki babu kwari.

Suna isa office ta fice daga motar da sari dan bata san wani ma ya ganta saboda gani takeyi kamar tayi lefi babba. ji takeyi kamar ta ci amanar Abdulkareem

Umar ma wucewa conference room yayi saboda suna da meeting da safen. Ko da ya shiga conference room din se da mutanen ciki sukayi mamakin yadda yazo da wuri, umar din da se ayi meeting sau 100 be je ba balle ace shine ya zo da wuri haka.

Ya riga Abdulkareem zuwa, shima Abdulkareem se da yayi mamakin ganin shi.
Alh ibrahim yana shigowa aka fara meeting daman shi ake jira.  
Meeting ne akayi akan za'a tura mutane biyar  paris yin wani course na wata 1 wanda a ciki harda Abdulkareem

Lokacin da aka kira sunan Abdulkareem shi kanshi se da yayi mamaki saboda a iya sanin sa babu shi a cikin wannan tafiyar,  kwatsam se ga sunan sa a cikin list din. Abdulkareem ya juya ya kalli umar wanda ke wani irin murmushi na mugunta.
Ko ba'a fada ba yasan umar ne ze iya sawa a sa sunan sa a ciki.

Ba wai baya son zuwa bane tsoron sa  ze bar ummulkhair tare da babban abokin adawar sa, kuma yasan saboda hakan umar yayi abunda yayi.

Bayan an gama meeting Ak ya samu Alh ibrahim a office. Bayan sun gaisa Ak yake kara tambayar sa dalinlin da yasa aka sa sunan sa a last minute

ALH ibrahim yayi dariya sannan yace
"Rabon da kai za'ayi tafiyar. Kasan bana so ka matsa ko ina a company nan saboda ina jin dadin aiki da kai sosai, amma ya zanyi.
Nayi considering recommendation na MD ne shiyasa zan barka ka tafi ba don naso ba se dan ilimin da zaka koyo ze kara bunkasa company nan"

Cike da damuwa a fuskar Ak yace
"Sir Amma banso nayi tafiya a lokacin nan ba, babu yadda zaayi ayi shifting tafiyar ta se wani lokacin?

"Alh ibrahim yayi murmushi sannan yace
"Nayi tunanin zakayi farin ciki da tafiyar nan. Da yanzu da  anjima daya ne a gurin Allah. I trust you Abdulkareem and i trust you will do well there. Kaje ka fara shiri tafiyar ku is in few days"

Abdulkareem ya lura da Alh ibrahim ba yarda zeyi da kudirin sa ba Dole ya hakura ya dawo office dinsa fuska a dagule. Khairi is gradually slipping daga hannun sa a Critical time din da ya kamata yayi cementing soyayyar sa a zuciyar ta.

🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Bintu. A
09034346763

SarkakiyaWhere stories live. Discover now