🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Ko a mota bata sake fuskar ta ba, idan ta tuno tambayar da likita yayi mata se taji takaicin binshi asbitin da tayi. Kar Allah ma ya hada ta aure da umar ballantana ta haihu da shi.Shima umar din shayin yi mata magana yake saboda da be ce matar sa bace da likitan be tambayeta ko ciki gare ta ba.
Suna isa kofar gida ta fita daga motar da sauri tare da buga masa kofar motar da karfi, ko juyowa batayi ba ta shige gida. Tana shiga daki ta dau wayar ta dan a gida ta bar wayar. missed call din Abdulkareem ta gani rututu a wayar ta. Tayi dailing wayarsa bugu daya ya dauki wayar kamar daman jiran kiran yakeSuka gaisa cikin girmama juna sannan Ak ya tambaye ta
"Lafiya yau baki zo aiki ba kuma ina ta kiran wayar ki tun safe bakiyi picking ba"
Khairi ta danyi shiru tana tunanin excuse din da zata bashi
"Naje asbiti ne na bar phone din a gida shiyasa"
Shima karyar rashin lafiyar zata yi mishi duk da da gasken taje asbiti"Subhanallah waye ba lafiya"
Ya fada muryar sa cike da damuwa"bana jin dadi ne Amma Alhamdulillah yanzu da sauki"
Ta fada har tana rau rau da murya ita a lallai mara lafiya"Baki da lafiya? me ya same ki? me ke damun ki? Subhanallah ya jikin"
Duk yabi ya rude"Da sauki ba wani abun damuwa bane fa, fever ne Amma Alhamdulillah nasha magani ya sauka"
Ta fada tana kara narkewa, tana jin dadain yadda yake nuna kulawarsa a kantaHaka de suka taba hira wanda rabi da kwata sannu yake mata, yayi mata sannu yafi cikin carbi tare da yi mata adduan Allah ya sawake mata. Daga karshe sukayi sallama yace ze barta ta huta tun da bata da lafiya, ya sanar da ita ze tsaya ya duba ta a hanyar sa ta dawowa gida.
Ko da Ak ya ajye wayar damuwa ce ta kara bayyana a fuskar sa, ga damuwar maganar da jidda ta fada masa da safe, ga damuwar rashin lafiyar khairi. Gaba daya se yaji ranar tayi masa zafi.
Agogon hannun sa ya kalla yaga lokacin meeting yayi, ya baro office dinsa ya haura conference room don yin meeting
Meeting ne na manyan ma'aikatan company da heads din department wanda harda MD da CEO.Ko da Ak ya shiga conference room mutanen da suke ciki kalilan ne, a hankali sauran sukayi ta zuwa har aka cika. Kowa ya hallara har Alh ibrahim amma babu umar babu dalilin sa. Kowa ya san umar dan ganin dama ne se yaga dama yake zuwa meetings,
Ko jiran sa ba'ayi ba suka fara meeting din.Se bayan kusan miti 40 sannan uamr ya turo kofar conference room a gadararce ya shiga, babu wanda ya kalle shi bare ya tanka masa har ya samu guri ya zauna se Alh ibrahim da Abdulkareem da ke ta watsa masa killer look, kowa da dalilin da yasa suke masa wannan kallan a zuciyar sa.
Umar kuwa ko a jikin sa wai an mintsini kakkausa, duk da shima da nashi kalar bakin cikin da ya birne a cikin ransa.Aka gama meeting mutane suka fara watsewa, abun mamaki shine umar da Abdulkareem ko motawa basuyi daga gujerar su ba, da alama akwai magana a bakin su su biyun. se da aka gama watsewa tas saura su biyun sannan Abdulkareem ya taso ya tunkaro inda umar yake zaune.
"Kayi maganar da ta kawo ka ka tsaya min a kai"
Cewar umar ganin Ak ya tsaya masa a gabansa, shi beyi magana ba shi be zauna ba"Ba kasa maganar nayi ba, maganar da zan fada ce ba lallai tayi maka dadin ji ba"
Ak ya maida masaUmar yayi murmushin da gefen bakin sa
"Nasan maganar ummulkhair ce ko"
Ya kwashe da dariyar mugunta sannan ya ci gaba"Bari na saukaka maka maganar. ina so ka sani cewar i love ummulkhair and i can trade the world for her. Kar ka bata yawun bakin ka saboda eventually khairi will be mine"
Yana gama fadin haka ya tashi ze bar gurin, da sauri Ak ya dafa kafadar sa alamun tsayar da shi
"Baka saurari abun da zan fada ba ay"
Umar ya dan girgiza kafadar sa saboda hannun da Ak ya daura masa. Ak ya daura da cewar
"Dont get your hopes high, kana ikirarin kana son ummulkhair kana son ummulkhair, ka taba zama kayi tunanin ita wa take so?"
Ak yayi murmushi mugunta sannan ya zagayo yana facing dinsa, sannan ya ci gaba"Do whatever you want ummulkhair will never love you"
Yana gama fadin haka ya kama hanyar fita daga conference room din ya bar umar da tunani tunani kala kala, tabbas yasan khairi bata son shi amma be taba bawa abun mahimmanci ba, shide burin shi ya mallake ta, to idan ya mallaketa kuma bata san shi ya za'ayi kenan
🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Bintu. A
09034346763
YOU ARE READING
Sarkakiya
RomanceLabarin tsantsar soyayya me cike da sarkakiya ce ta kullu a tsakanin su. Ummulkhair ta zamo Allura cikin ruwa wanda me rabo ne ze dauka. Shin wa zata zaba a cikin su? Boyayyen masoyi Abdulkareem wanda yayi dakon soyayyar ta na tsahon lokaci ko kuma...