🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Ko da khairi ta tashi a bacci 4 ya wuce na yamma. Da sauri ta shiga toilet tayi alwala ta yi sallah. Tana zaune a kan sallayar taji ana knocking kofar dakin ta. Se da ta amsa sannan Aunty M ta shigo. Da murmushi khairi ta gaishe ta"Aunty kin dawo kenan" ta tambaya
"Na dawo naji ki shiru,nayi ta knocking dakin naji ba ansa. ina budewa naga kina ta sharar bacci shi yasa ban tashe ki ba. Yanzu ma naga lokacin sallah na kurewa shi yasa nazo tashin ki"
Khairi ta saki wani hamma tare da fafin
"Ayya aunty yanzu na tashi, ba wani aiki nayi ba amma duk na gaji""Ya interview din naki?"
Aunty maimuna ta tambayaSe a lokacin ta tuno drama da akayi a company, bakin cikin umar ne ma ya sa ta bacci.
Ta dan yi yake sannan ta ce
"Alhamdulillah, se de mu jira abunda Allah zai yi""Allah yasa mu ji alkhairi"
Aunty m tayi fata"Ameen"
Khairi ta ansa a sanyaye, domin a kasan zuciyar ta tasan abun ne me wuya. Duk da bata san me ya kaishi company ba, zata iya yuwa maaikaci ne a company ko client. Ko ma de wanene tasan rashin kirki da tayi masa a gaban mutane ze sa suyi rejecting dinta, duk da daman jikin ta yayi sanyi tun sanda sukayi mata tambayar yaya zatayi handling service din da take yi.Aunty maimuna ce ta katse mata tunani
"Ki je ki ci abinci, zan je dauko su zahra a makaranta, driver nasu yana gurin gyaran mota ba'a gama ba har yanzu""To shikenan a dawo lafiya" ta ansa a gajerce
Aunty M ta fita daga dakin ta bar ta a kan sallayar yadda ta same ta.
Bayan fitar ta tunanin ta ci gaba dayi daga karshe ta dauki wayarta da ke kan gado ta fita falo don cin abinci.Tana zuwa falon kan dinning table ta nufa. abinci ne aka jera a manya manya flask kamar yadda aka saba. Ta zauna sannan ta zuba abincin ta fara ci ba kama kafar yaro, daman khairi da abinci 5 and 6 ne.
Tana ci tana ainayo yadda arzuki yayi a rayuwa. Yanayin gidan ya isa ya sa maka wani kwanciyar hankali da nutsuwa na musamman. Ko ina ya sha kaya na alfarma, ga gidan tas tas baza ka ce akwai yara a gidan ba.
Tunda tazo bata aikin komai daga ci se bacci domin akwai masu aiki har biyu, daya tayi share share dayar kuma tayi girki da kula da karamin yaron aunty M.Gidan apartment ne, amma apartment wanda ya ansa suna apartment domin dakunan dake gidan sun kai 5. Ga falo har biyu, se ka gama rayuwar ka a gidan baa san kana ciki ba.
Allah sarki gidan inna asabe😂 ta fada a rantaBayan ta gama cin abincin ta kai plate din kitchen sannan ta dawo ta zauna a kan sofa ta fara kallo, wayar ta ta janyo dan ta duba. Nan kuwa taga messages rututu kuma duk daga mutum daya "UNKNOWN" (sunan da tayi masa saving)
Lafiya?? Ta fada a cikin ranta tun kafin ta duba message din. Ita de tasan tun lokacin da tayi mishi titsiyen shine malam jabir be kara yi mata message ba se yau. Message na farko da ta gani
"I hope you are doing well"
(Da fatan kina nan lafiya)Na biyun
"Hope everything is fine"
(Fatan komai de kalau)Na ukun
"Don't get so stressed up please"
(Dan Allah kar ki tada hankalin ki)tsayawa tayi da karantawa ' guy lafiya? ' ta fada a fili tana mamakin messages dinsa.
Duk yadda akayi rashin zuwanta makaran ta ne kwana biyu yasa yayi mata messages dinnan. Ta sheke da dariya 'Lalli malam jabir kana ruwa' .
ta kara fada a fili sannan ta ci gaba da karantawa"Please say something"
(Dan Allah kice wani abun)Na shidan
"Your silence is killing me, at least type something"
(Rashin maganar ki yana daga min hankali, ki daure ki ce ko da wani abun ne)Na bakwai
"I hope you'd cooldown"
(Allah ya wuci zuciyar ki)
" yours secret admirer"
(Boyayyen masoyi)Dariyar da takeyi ce ta koma murmushi, tayi missing messages dinsa. Ba wai ta fara son mal jabir bane, kuma ita ba tsanar sa tayi ba. Wani lokcin se ta dinga tunanin anya ba wani bane yake mata messages dinnan. Tana fatan ace wani ne ba mal jabir ba. Wani bangare na zuciyar ta yana fada mata wani ne daban. Amman dukkan evidence ya nuna mal jabir dinne.
Yanzu ma dan ta kwana biyu bata je makaranta bane zeyi bombing wayarta da messenges
🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒ALH ibrahim ne a zaune a office dinsa ya dan kwantar da kansa a jikin kujerar da yake zaune yana jujjuyawa, Hannun sa dauke da biro Shi ba rubutun yake ba amma ya rike biro kamar me rubutu. Da ganin sa kasan ya fada cikin zurfin tunani ne. Tun jiya abun da ya faru ya tsaya masa a rai.
ALH ibrahim yana bayan umar lokacin da suka samu sabani da khairi don haka a gaban idon sa akayi komai.
lokacin da ya sanya idonsa a kan ummulkhair se da yaji wani abu ya dake shi.Yanayi da kamanin ta ya tuno masa da gaggarumin abun da yake ta kokarin birnewa a cikin zuciyar sa shekara da shekaru. Be san me yasa ganin ta ya taso masa da tsohon ciwo dake zuciyar sa ba.
Gashi de a zahiri be san ta ba, be taba ganin ta ba ma, amma wani abu game da ita ya sa kwakwalwar sa ta binciko wani shafi na rayuwar sa da yake ta kokarin kullewa.Wayar telephone ya dauko sannan ya kira jidda
" shigo office ina neman ki"
Abunda ya fada kenan sannan ya ajye wayar.🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Bintu. A
09034346763
YOU ARE READING
Sarkakiya
RomanceLabarin tsantsar soyayya me cike da sarkakiya ce ta kullu a tsakanin su. Ummulkhair ta zamo Allura cikin ruwa wanda me rabo ne ze dauka. Shin wa zata zaba a cikin su? Boyayyen masoyi Abdulkareem wanda yayi dakon soyayyar ta na tsahon lokaci ko kuma...