Kiran assalatu ne ya tashe shi. Yana tashi ya janyo wayar sa. Ba lokaci ze duba ba, dubawa zeyi ko tayi mishi reply, nan ma ya ga babu message dinta. Tun bayan ya tura mata message din jiya da yamma yake duba wayar ko ze ga reply dinta amma babu.
Ya tashi yayi raka'atanul fajr sannan ya nufi massalaci.Ya tsaya yin azkar da lazumi se karfe 6:20 ya dawo daga massalaci nan ma ya duba wayar babu reply dinta, sannan yayi tunanin kara tura mata wani message din yana ta adduan Allah yasa tayi replying.
"I wish today could be so bright and calm as you are, good morning
Secret admirer........"Ya tura message din sannan ya tashi ya fara shirin tafiya aiki. Har yaje wajen aiki hankalinsa yana kan waya. Daga yaji kara ko yaga tayi haske se ya dauko ya duba, amma babu reply. Se yanzu ya tabbatar akwai yaki babba a gabansa
Aikin da zasuyi a bwari ya kan kama domin kuwa saura kwana kadan a fara aiki, duk wani design da ake bukata an gama shi. Abdulkareem yayi kokari sosai a aikin. Umar ma baa barshi a baya ba domin yayi iya bakin kokarinsa duk da ba wai ya goge a aikin ba amma yayi nashi iya abunda ze iya.
Har yanzu depression dinsa yana nan, ya kan tashi lokaci zuwa lokaci. Mutanen office din kowa taka tsantsan yake kar ya shiga hurumin shi. Wani lokacin ma baya ma kowa magana haka ze shiga office dinsa ya kulle se ya tashi ze fita. Babu wanda ya taba ganin murmushi ko dariyar sa.
Abunda yake bawa kowa mamaki a office din shine, Umar ba da mota yake zuwa aiki ba. Kullum se de ya kira motar uber ta kaishi aiki sannan idan ya gama ya kira a dauke shi. Managing director guda bashi da mota, maaikatan da suke kasan kasan sa ma suna da motocin su.
A gidan ma haka yake babu yabo babu fallasa, baya shiga harkar kowa. Se suyi sati basu ganshi da idon su ba. In banda hajiya binta da ke sintirin kai masa abinci daki ba
🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒Anyi sati kullum Abdulkareem se ya tura ma khairi message. Har ya saba ma idan ya tura ba za tayi mishi reply ba. A juri zuwa rafi wata rana tulun ze fashe, ya tabbata wata rana zatayi mishi reply. A hankali sakon sa ze isa inda yake so yaje
Wasikun nasa gajeru ne, wadanda basa bukatar reply. Wasiku ne masu dauke da sakon zuciya wanda shi wanda ya tura burinsa shine ya sanar da ita yanayin da yake ciki.
Safe, rana, dare kamar abinci haka yake turawa."Look at the hazy cloud isn't it beautiful? just like you" ko kuma ya rubuta
"There is something about the sun. Its rays are hash sometimes but we can't live without it"
A dukkan sakon sa idan yazo karshe se ya rubuta secret admirer
Ummulkhairi kullum taga wasikun nan se abun ya daure mata kai, wani lokacin se tayi tunanin tsohon saurayin ta khalid ne, amma idan taga yanayin zurfin ma'ana da ke kunshe a cikin sokon se tace ba khalid bane. Domin khalid bayi da wannan nutsuwar da ze fadi jimla daya ko biyu amma ya bada ma'ana sosai.
To waye secret admirer nan, Tana so ta kira number don ta san wane yake wasa da hankalin ta, amma se tayi tunani koma wanene ze kira yayi magana idan yaji bata kula shi ba. Gwara ta kama ajinta ta jira har se ya kira ta.
Yau ma kamar kullum sakon aka turo mata, ta dauko wayar ta har da zumudi domin taga me ya rubuta yanzu kuma, ta fara sabawa da sakonnin sa da har idan be turo da wuri ba se tayi ta jin ba dadi. Ba ta san wanene ba amma tana jin dadin yadda yake nuna kulawar sa a gare ta. Idan ma khalid ne yana gab da shanyo hankalin ta a kanshi.
Ta janyo wayar ta karanta, murmushi sosai tayi yayin da ta tsurawa sakon idanu se maimatawa takeyi a ranta. Tana jin dadin kalaman sa, yana sa tana laakari da abubuwa da dama wanda a da bata basu mahimmaci.
" whenever i set my eyes on you my world comes to a complete stand still. I adore every moment i see you. From the first day i set my eyes on you I knew you are something different that is why I captured every details of you, deep buried in my heart"
Ta dade tana kallon wayar ta tana kallon ko wani kalma da ya rubuta.
Na rubuta masa reply?,
me zan rubuta ne,
bawan Allah beyi fishi ma da rashin tura masa reply,
Duk wannan maganar a zuci takeyi
yau kan zatayi kokarin rubuta masa reply.
Ta fara rubutawa"can I know who this may be"
Se kuma ta goge, tunda be fadi waye shi ba baza ta tambaye waye shi ba. Ta rubuta wani abun kawai sannan ta tura. Ta ajye wayan ta ci gaba da hada kayanta a akwati domin hutun makaranta ya kare zata koma Abuja washegari.
🍒🍒🍒🍒🍒🍒Abdulkareem ke tuki ya baro gurin aiki ze je gida, wayarsa yaji tayi kara alamar sako ya shigo, be kula wayar ba saboda tukin da yakeyi. Se da ya isa gida ya dauki wayar don ya duba wani sako ne ya shigo.
A screen din wayar ya ga CHERRY. Mamaki ne ya kama shi, be taba tunanin zatayi mishi reply ba. Da sauri ya bude wayar ya shiga message din da ta turo
"Thank you"
Abinda ya gani kawai kenan. Kwashewa yayi da dariya sosai , Ya ci gaba da yin dariyar na wani lokaci kamar tabbabe . Shi kansa ya rasa me yasa shi dariyar ma.
Thank you din tata kamar wadda aka matsawa se ta bada answer. Abunda ya tura mata baya bukatar thank you. Da alama ta rasa abun da zata ce ne. Haka ya ci gaba da Dariyar Sannan ya rufe motar ya shiga gida.
Daga ya tuno "thank you" se yayi dariya haka yayi tayi har dare kamar wanda ya zare.
YOU ARE READING
Sarkakiya
RomanceLabarin tsantsar soyayya me cike da sarkakiya ce ta kullu a tsakanin su. Ummulkhair ta zamo Allura cikin ruwa wanda me rabo ne ze dauka. Shin wa zata zaba a cikin su? Boyayyen masoyi Abdulkareem wanda yayi dakon soyayyar ta na tsahon lokaci ko kuma...