🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Karfe 4 na yamma Aunty maimuna ta lando gidan su khairi hankali a tashe, har a lokacin khairi bata bude kofa ba. Anyi bugun duniya khairi ta bude taki budewa don babu inda zata je. yadda suka daura auren nan su san yadda zasu kunce shi.Ant M ta shigo ta ga kowa cirko cirko a bakin dakin khairi ana ta yi da ita ta bude ta ki, Ba ta tsaya gaisuwa ba itama tayi joining queue din masu lallashi da bugun kofa.
Khairi tana jiyo muryar Aunty M ta karaso jikin kofar da sauri tana wani irin kuka tana cewa
"Aunty maimuna kinga abun da su abba sukayi min, ki fada musu bana son umar kin fi kowa sanin wanda nake so"Aunty M cikin rarrashi tace
"Na sani khairi, nasan komai yanzu de ki bude kofar nan na shigo""Babu inda zanje, ki fada musa baza su kaini gidan wanccan mugun ba , wallahi babu inda zanje"
"Babu inda zaa kaiki nayi miki Alkawari, ba wanda ze kaiki, yanzu de ki bude kofar"
Se da khairi ta dau lokaci kamar baza ta bude ba sannan ta bude a hankali, Auty m ce kadai ta samu damar shiga dakin kafin khairi ta kara banko kofar ta rufe da sakata.
A nan Aunty m ta fara aikin lallashi tare da bada hakuri. Ba abun da khairi take se kuka, fuskarta tayi ja idanu sunyi luhu luhu, gaba daya ta fita daga kamannin ta.
Aunty M taga abun baze yu ba ta fita ta samu su abba tace suyi hakuri su bar kai khairi yau saboda wlh baza ta yarda ta tafi ba. A bari idan abun yayi sanyi a hankali se a kaita saboda har hanzu a state din denial take.
Shi kuwa umar tun bayan fitar Alh ibrahim daga gidan babu wanda ya kara zuwa ko ya kira shi a waya, har ya fara damuwa ko an raba auren ne. Ko daman baa daura ba so ake a ji me ze ce? Ko rashin mutuncin da yayi ma babansa ne yasa aka fasa? Duk ya shiga cikin damuwa gashi ba wanda ze tuntuba yaji me ya faru.
🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Se bayan kwana biyu sannan aunty M ta neme umar a waya tace yayi mata kwatancetace gidan gata nan zuwa, tana zuwa ta tarar da gidan kacha kacha kamar ba mutum ne ke rayuwa a ciki ba. cikin mamaki take tambayar sa
Haka zasu kawo mishi matar? Se a lokacin ya samu kwanciyar hankali da ya tabbatar an daura da gaske kuma baa ware auren ba.Da shi da aunty M da me gadi ne suka gyara gidan tsaf, aunty M da umar suka fita shopping aka siyo dukkan abunda zasu bukata na gida na yau da kullum.
Gyaran gidan se da ya dauke su kwana biyu, suka kintsa gidan ya koma kamar na mutane. Har turaen wuta ta siyo ta ban banka a gidan.Ba'a kawo khairi gidan ba se bayan kwana 5 da auren su, nasihan umma ce ta shige ta a lokacin da ta fada mata cewar
"Aure ne an riga an daura miki, ki sani cewar akwai hakki me girma da ya rataya a wuyan ki. Aure ba abun wasa bane ki dauke shi a matsayin ibada. Yanzu ko ni ko abban ki bamu isa mu kunce auren nan ba saboda wannan hurumin mijin ki ne"Wannan maganar ce tasa khairi tayi tunanin to ay gwara ma taje gidan ta titsiye shi ya sake ta kawai, idan ta ci gaba da zama a gidansu igiyar auren de tana kanta shiyasa ta yanke shawarar zata gidan umar din.
Ranar da aka kaita kamar ba amarya ba, umar ya bawa Abdullah motar sa a ka kawo ta a ciki, daga khairi se Aunty M, se wata kakarsu umman luwa, se Abdullah da ke driving. Abun de lami ko bazawara baza a kai haka ba
Umma ta hada kayan sawar ta tas aka sa akwatuna aka tafi mata dasu a bootSuna isa kofar gidan khairi ta birkice ta fara kuka ganin da gaske abun ya tabbata. Aunty m tayi ta rarrashin ta da haka har ta shigar da ita gidan.
Da suka shiga babu kowa umar ma baya gidan dan baya so su tarar da shi a gidan
Har daki aunty m ta shigar da khairi, ita de khairi ba abun da take se kuka saboda ta gaji da fighting. She is exhausted completely, kaddara ta riga fata dole she has to comes to terms with her destiny.Bayan magrib aunty m tace ma khairi zata je ta fadawa me gadi ya kunna generator, bayan mintuna kadan umma luwa ta bi bayan ta aunty m. Khairi tana jin haka tasan kawai raina mata hankali sukayi dan ta tabbatar tafiya sukayi, ta kula sun maida ta karamar yarinyar da zaayi wa saurin wayo.
Da ta tabbatar sun tafi khairi tasa key ta rufe dakinUmar ya dawo gidan bayan isha rike da tarkacen kayan ciye ciye saboda yasan ba lallai ta ci abinci ba.
Tunda ya dosa gidan yaji gabansa na faduwa, be san me ze ce mata ba, da wani idon ma ze kalle ta.
Yana tafe bugun zuciyar shi na karuwa, jiki a sanyaye ya shiga parlon yaji shiru, ya nufi dakin da shine nata cike da tsoro da fargaba, wannan wani irin abu ne wai sabon ango yana tsoron shiga dakin amaryar sa.Ya lallami kansa tare da bawa kansa karfin gwiwa yayi knocking, ba ansa. Ya yanke shawarar murda kofar ya shiga, Yana murdawa yaji ta a rufe. Ashe ma shirme yake da yayi tunanin zata bar masa kofar a bude
Ya kara kwankwasa kofar a hankali sannan yace
"Ga abinci na ajye a bakin kofa"Daga haka ya juya ya bar kofar dakin ta.
Yadda ya ajye ledojin da ya kawo haka yazo ya tarar da su washe gari da safe baa taba ba. Ya kwashe ya kai dustbin saboda yasan komai ze iya lalacewa by then tunda ba a fridge suke ba sannan Ya dawo ya zauna a parlor.
kana ganin shi kasan he is restless saboda Ya kagu ya ganta, ya kagu ya san halin da take ciki, ya kagu ya bata hakuri sannan yayi mata bayani it was never in his intentions to force her to marry him. Ya kagu ya fada mata ba se ta damu da kulle kanta a daki ba saboda bashi da niyyar taba ta. Yana so tayi rayuwa freely a gidan. Idan ma tace bata son ganin shi shi me iya bar mata gidan ne.
Wajen karfe 11 me aikin 'jeka ka dawo' da Aunty M ta samo musu tazo gidan, kullum zata zo da safe tayi musu aikace aikace da girki sannan da yamma ta tafi.
Umar yayi mata bayanin komai sannan ya nuna mata dakin khairi yace ta kwankwasa ta fada mata ya fita zata iya fitowa.Bashariyya taje tayi ta kwankwasa ba ayi magna ba, da ta gaji se tace
"Me gidan ne yace na fada miki zaki iya fitowa shi ya fita"Khairi tana jin muryar mace ta karaso bakin kofar
"Wacece?"
Ta tambaya"Bashariyya ce, nice wadda aka turo nayi muku aiki"
Khairi ta bude kofar a sanyaye taga bashatiya a bakin kofar, yar buduwa ce wadda bata fi shekara 16 ba bashariyya tace
"Yallabai ma yace na tambaye ki abun da zaki ci se na dafa"Khairi tace mata
"Ba komai, ina tuananin babu aiki yau ki tafi kya dawo gobe"🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Tun daga ranar haka sukayi ta wasan hide and seek da umar, bata fitowa se taji bashariyya tazo ta buga kofar ta fada mata me gidan ya fita. Haka zalika Tana jin karar motar sa da yamma take komawa cikin daki ta rufe.Allah sarki umar ba wai wani gurin yake zuwa ba saboda ba shi da aboki ko daya a kano, be san kowa ba se dangin su na cikin gari, kullum da safe yake fito da motar sa yayi parking a kofar gida sannan ya zauna a bencin me gadi suyi ta hira, wani lokacin ma zama yake shi kadai yayi ta tunani. se yaji yunwa yake zuwa ya siyo abinci yaci a nan kofar gidan shi da me gadi. Se yayi magrib sannan yake shigowa gidan. Duk wanda yasan umar yasan yanzu yayi mugun chanzawa, ya dawo salihi bawan Allah wanda be damu da komai a duniya ba. Ya koma yanayinsa na coldness daga gani kasan akwai abun da ke damun sa
Gaba daya duniyar tayi masa zafi, gashi de ya auri khairi burin shi ya cika, ga khairi a matsayin matar sa amma ba kwanciyar hankali. Hasali ma tun da aka kawo ta be sa ta a idon shi ba har ana magara sati daya da zuwan ta gidan
A bangaren Abdulkareem kuma abun se addua, ya shiga wani irin matsainancin depression. Babu inda yake fita se masallaci, wani lokacin a can yake yini saboda gidan ma zafi yake masa. A masallacin ne yake samun dan kwanciyar hankali. ya kan dauko quran yayi ta karantawa har bacci ya kwashe shi.
Kullum yana cikin jallabiya, wanka ma se hajja tayi da gaske yakeyi, ya rame ya kara duhu, ya bar kasumba kacha kacha, duk wanda yasan Ak se ya tausaya masa saboda kowa yasan Abdulkareem dan kwalisa ne amma depression ya maida shi haka.
🍒🍒🍒🍒🍒****Depression is real. Allah ubangiji ka raba mu da shiga tashin hankalin da ze kaimu ga depression. Dukkan damuwoyin mu Allah ka yaye mana, ka hada bintu's family da mazaje na kwarai salihar yan Aljanna. Mu da muke da Auren Allah ka dawwamar da mu a ciki soyayya da rufin asiri, Arzuki , mutunta juna da zaman lafiya. Ya Allah ka Albarkaci zuriar mu wanda suka zo da wanda suke hanya. Ameen ya rabbul Arshul Azeem, ya hayyu ya qayyum
Episode din kwana biyun nan makes my heart heavy. Sending love to you all
Yours always
Bintu. A❤️
09034346763
YOU ARE READING
Sarkakiya
RomanceLabarin tsantsar soyayya me cike da sarkakiya ce ta kullu a tsakanin su. Ummulkhair ta zamo Allura cikin ruwa wanda me rabo ne ze dauka. Shin wa zata zaba a cikin su? Boyayyen masoyi Abdulkareem wanda yayi dakon soyayyar ta na tsahon lokaci ko kuma...