🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
A gefen su hajja kuma jiki duk yayi sanyi da mutuwar umar. Cikin damuwa Alh wada ya kira ta suka kara tattauna zancen hadin auren da suka kudiri niya.
Hajja ta zaunar da Abdulkareem yau akan su kara tattauna maganar da suka fara. Da farko Abdulkareem ya cije amma ganin yadda hajja ta hade rai yasa ya saukar da nashi taurin kanHajja tayi ta masa maganganu da nusar da shi hanyar da ta dace a nata ganin.
Shi ba wai auren ne baze yi ba, Aa maryam din ce kwata kwata be hango su tare a matsayin mata da miji ba. Maryam din da girman sa aka haife ta, A kalla ya bata shekara 18. Da mace ne shi kila da ya haife ta ma."Hajja nifa ba wai auren ne bazan yi ba kawai maamah ce tayi yarinta da yawa kuma wlh yar gobe kallon kanwata nake mata. Kinga kuwa mutum baze iya auren kanwar sa ba"
Hajja ta kara hade rai
"Bana san shashancin banza, Allah ya halarta maka auren ta kana neman haramtawa kanka. To bari kaji na fada maka kar ka soma wani tunani dan mijin tshuwar budurwar ka ya rasu, wallahil Azeem bazan taba lamunta da duk wani abun da zaka iya kudirtawa a ranka ba. Gwara ma na taka maka birki tun yanzu ka hakura ka rungimi yar uwar ka. Ahir dinka wallahi""Hajjja..... ni wlh...... kai innalillahi......"
Nan da nan Ak ya rude ya fara i'ina saboda be taba tunanin hajja zata kawo wannan maganar ba, shi kuma har ga Allah har a lokacin tunanin haka be zo masa kwakwalwa ba. The thought never crossed his mind wai dan mijin khairi ya rasu ya fara tunanin maye gurbin shiHajja ta tashi ta bashi gurin saboda ta gama maganar ta kuma ba jiran shawarar sa take ba. Ak ya rike kai yana jimamin kalaman hajja.
Yana cikin wannan tunanin ne yaji wayar sa na ringing, ya zaro wayar a kasalance ya duba wa ke kira
BABYMORRY ya gani kuru kuru a kan screen, har wayar ta tsinke be iya picking ba se da ta kira a karo na biyu sannan ya daga.Da yar fara'ar ta tayi mishi sallama wanda ya amsa babu yabo babu fallasa. Maryam ta gaishe shi sannan ta dora da cewar
"Naji anyi maka rasuwa shiyasa na kira nayi maka ta'aziyaa, ya hakuri?
"Da godiya maryam"
Ya amsa a kasalance"To Allah ya jikan sa yayi mishi Rahma. Hajja ma tace kazo kana gari ko?
Ta tambaye shi cikin nustuwa"Eh nazo ta'aziyar nan ce"
"Allah sarki Allah ya sa ya huta muma Allah ya kautata namu zuwan"
Ak yayi ajiyar zuciya ya amsa da
"Ameen Ameen nagode maryam, hajja tace kinje gida ko? Ki gaishe da kowa da kowa dan Allah"Maryam ta amsa da insha Allah sannan tayi mishi sallama ta kashe wayar.
Tana kashewa tayi wani tsalle tana dariya, ta juya ta kalli kawar ta Rukayya"Wayyo dadi kashe ni, kullum se nayi kamar na kira shi se na kasa, se yau da na samu excuse"
Rukayya ta harare ta
"Yau din ma ba se da na takura miki ba sannan kika kira"Maryam ta karaso da gudu ta rungume Rukayya
"Wlh kuwa baki ga yadda nake ta son na kira shi ba, tunda na karbi number sa ban taba kira ba saboda basan me zan ce masa ba.
ruky baki ga yaya bane da zaki gane abun da yasa na haukace a kan shi. Kinsan ba wani dadewa nayi da fara son sa ba Amma ji nake kamar na shekara dubu da son sa a zuciya ta"Rukayya ta fashe da dariya
"Kai morry easy mana, yanzu de nuna min hoton yayan nan na gani, naga dalilin da yasa kika haukace haka""Kar fa na nuna miki fi fola"
Maryam ta fada tana dariyaRuky ta kara hararta
"Dallah ni kinsan babu ya malam habib kaf duniyar nan"
Suka kwashe da dariya gaba daya. Da maryam tasan wanda ya rasu baza tayi murnar kiransa ba.🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Har akayi kwana 3 khairi bata dawo daga shock din da take ciki ba. Ko abinci bata iya ci se ruwa se kunu, kunun ma idan tasha se taji zuciyar ta na tashi. Haka aka ci gaba da zaman makoki abun tausayi, mutuwar matashi tan da shiga rai sosai.Aunty maimuna ta shigo da fura da nono a cup ta zauna a kusa da khairin da duk ta jika hijab dinta da hawaye tana jan carbi
"Karbi furar nan ki sha ko kya samu kwari"Khairi ta dan yamusta fuska sannan tace
"Wlh Aunty bana jin shan komai, ba abun da yake min dadi shiyasa"Aunty m ta ci gaba da mika mata kofin
"Karbi de ki sha zakiyi ta zama baki ci abinci bane, ki daure ki sha ko yaya ne"Khairi ta karbi kofin ta sa a baki tana kokarin sha, karnin nonon ya bigi hancin ta nan da nan taji ta tsani ganin nonon ma, Zuciyar ta ta fara tashi.
Da sauri ta ajye cup din tare da cewa
"Aunty bazan iya sha ba yana tada min hankali"Aunty maimuna tayi tayi da khairi ta sha amma khairi taki sha, daga karshe ta hakura ta kyale ta. Se da akayi kunun sadaka sannan khairi ta iya sha shima se da ta tsula mishi ruwa sosai.
A gidan makoki mutane sun fara walwala dayake an kwana uku da mutuwar kenan. Umma ta lura da rashin cin abincin khairi, ruwan sha ma se ta zaba, Bata iya shan pure water ko bottle water se ruwan borehole na gidan. Daga shi se kunu wani lokacin ta ci tuwo shima ba da yawa ba.
Umma tana ta noticing dinta, yau har kakarin amai taji tana yi a toilet.Da dare bayan mutane sun watse umma ta samu khairi a daki ta zaunar da ita a kan gado sannan ta fara tambayar ta
"Ni kam ummu yaushe rabon ki da period?"
Khairi ta danyi jim saboda taji tambayar ba zato, se kuma ta fara lissafi a cikin kwakwalwar ta. Ta manta ma when last tayi period. Jinyar da umar yayi yasa ta mance komai ma
"Ummm.... Ina tunanin ya kamata ace nayi fa tun farkon watan nan amma kuma...... gaskiya umma bazan iya kirga yaushe na gama ba"
Umma tayi dan murmushi da ya tsaya iya lebe sannan tace
"To ba komai ki kwanta mayi maganar gobe idan Allah ya kaimu"Khairi ta kwanta tana ta tunani tunani, ita de tasan se mutum yana da cike yake missing period, ta yaya ciki ze shiga, duk abun da suke umar baya taba bari Yayi releasing a ciki. Ta ina ma ciki ze shiga gaskiya da dukkan Alamu stress ne yasa tayi missing period dinta. Haka tayi ta sake sake a cikin ranta, ta saka ta kunce
Washe gari da safe umma ta samu Abba ta sanar masa da zargin da takeyi Ummulkhairi na da ciki. Abba yayi farin ciki sosai. Se da ya jira zuwan Alh ibrahim sannan ya fasa masa labarin. Tun mutuwar Umar Alh be sake murmushi ba se yau, yau ne zuciyar sa ta samu rahmar sassauci daga kuna da jimamin rashin da yayi.
Abba be gama idar da magana ba Alhaji ya zaro waya ya kira dr ilyasu ya roke shi da yazo gidan a dauki jinin khairi domin su tabbatar da abun da suke zargiSe wajen 12 na rana dr ilyasu yazo a lokacin duk sun gama kaguwa, aka shigar da dr ilyasu har cikin dakin iya falmata inda khairi ke zaune, da farko khairi ta dauka dr yazo ya kara yi musu gaisuwa ne se da taji umma na fada ma mutanen gurin su dan bada guri likita yazo duba khairi ne ba lafiya
Kowa ya fita daga dakin daga khairi se umma se Aunty m da iya falmata, Se kuma dr da yake fito da kayan aiki na zukar jini
"Lafiya umma, ni fa lafiya ta kalau"
Khairi ta tambaya da mamaki"Lafiya lau ummulkhair, jinin ki ne zaa dauka ayi test"
'Too lalle abun babba ne, daga zargi har an kinkimo likita? Ta tabbata wannan aikin Alhaji ibrahim ne
Khairi batayi musu ba ta mika hannu aka ja jinin saboda ita ma tana bukatar sanin me ke faruwa da jikin ta.
Dr ilyasu ya gama aikin sa yayi musu sallama ya koma asbiti. Bayan kamar Awa daya dr ilyasu ya kira Alhaji a waya, bayan sun gaisa dr ilyasu yace masa
"Congratulations sir ummulkhair is pregnant"Babu abun da yake fitowa daga bakin Alh se kabbara
"Allahu Akbar, Allahu Akbar, Allahu Akbar"
Yana kabbara yana zubar da hawaye.Abba shima ya karbi kabbarar sukayi ta yi, suna hawaye suna murmushi. Abba ya shiga cikin gidan ya kira umma ya sanar mata, umma ma se da ta kara zubda hawaye ta rasa wanne farin ciki zatayi ko bakin ciki, Ashe umar yana da rabon barin me masa addua a duniya.
🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Bintu. A
09034346763
YOU ARE READING
Sarkakiya
RomanceLabarin tsantsar soyayya me cike da sarkakiya ce ta kullu a tsakanin su. Ummulkhair ta zamo Allura cikin ruwa wanda me rabo ne ze dauka. Shin wa zata zaba a cikin su? Boyayyen masoyi Abdulkareem wanda yayi dakon soyayyar ta na tsahon lokaci ko kuma...