Dinner 3

173 11 0
                                    

Se da ya gama lallashin ta ya tabbatar da ta dena kuka sannan yaja mota suka fara tafiya. Zuwan su gurin dinner ko cikakken minti 30 basuyi ba umar ya aikata abunda yayi.

Khairi de taga ana ta tafiya inda bata gane ba Ta san ba hanyar gida bane wannan
"Ina zamu je"
Ta tambaya murya a kausashe saboda kukan da sha

"Yanzu zamu karasa surprise ne"
Ya fada tare da kwakulo murmushi

Ko ina ze kaita tasan zata iya yarda da Ak 100%. Saboda shi din cikakken gentle man ne.
Basu dade da yin magana ba ta ga sun tsaya a dai dai cilantro restaurant. Kallon shi tayi a ranta tana cewa "no please".

"ba mu samu cin abinci a dinner ba shiyasa nayi tunanin mu zo nan muyi dinner mu, daga ni se ke"
Ya fada yana fadada murmushin da yake

Khairi tayi yake sannan tace.
"Baka ga yadda nake ba, na tabbata makeup dina ya lallace"

Se da ta fada sannan ya kalle ta sosai. Kasan idon yayi baki kwallin duk ya zazzago kamar wata bokanya. Hatta jan bakin da ke bakin ta duk ya zazzago har kan habar ta, kwata kwata ta manta da tayi makeup shiyasa tayi ta murza idon a garin share hawaye.

dariya yayi sosai, ko dan dazun da duhu ne yasa be gani ba ko kuma rashin nutsuwa ne yasa har be kula da bacin da fuskarta tayi ba.

"Au dariya kake min ko"
Ta fada cikin shagwaba

"idan na ganki da tsakar dare kwasa zanyi da gudu ay"
Ya fada yana kyakyata dariya

"Dan Allah haka nayi muni?
Ta fada idon ta yayi rau rau irin na shagwaba, ita bata san shagwabar ma takeyi ba.

"You looked cute"
Ya fada a cikin ransa tare da tsura mata ido amma be ce komai ba. kukan da tayi yasa kumatu da hancin ta sunyi ja. A yadda shagwabar ta birge shi ji yayi ina ma ze iya tafiya da ita gidansa ya sata a gaba da tsokana ko dan ya ga overdose cuteness dinnan

Ta zaro wipes a cikin cluch dinta zata fara goge makeup din. Da sauri ya dakatar da ita.
"Kar ki goge duka, bari na nuna miki inda ya baci"

Haka ya dinga nuna mata inda ya baci tana gogewa, yau ya samu damar kallon ta cikin sauki ba tare da ya saci kallo ba. Lalacewar kwalliyar ma gaba ta kai shi.
Se da ta gama goge inda ya baci sannan ya janyo mata mirror da ke lankwashe a gaban motar ta kalla.

"Wlh kara batawa nayi ma"
Tayi rau rau da fuska wanda yasa ya kara tuntsurewa da dariya

"Au dariya kake min ko, se de ka shiga kai kadai babu inda zanje"
Ta fada tare da hade rai irin na wasa.

Kokarin tsayar da dariyar yayi amma ya kasa cikin dariya yake ce mata

"Kiyi hakuri tuba nake, amma on a serious note Allah bakiyi muni ba. Ba ki kai dazu yin kyau ba amma its manageable"
Ya kara kwashewa da dariya

"Ni ka kyale ni"
Ta kara bata rai.

"Jira ni ina zuwa"
Ya fada tare da fita daga motar, ya shiga cikin restaurant din yayi musu booking wani section guda da su kadai zasu zauna, dubu darrirrika ya biya sannan ya dawo mota yace mata ta zo su shiga.
Da kyar ya iya lallamin ta ta yarda ta biyo shi suka shiga restaurant din.
Tana shiga ta nima toilet ta wanke fuskar ta tas. Sannan ta fito ta same shi a private gurin da yiyi booking musu.

Ya Tsura mata ido tun daga nesa har ta karaso inda yake zaune, kallon da yake mata yasa taji kamar zata fadi, amma haka ta cije ta karaso Inda yake zaune a kayatatcen open space.

Shi kuwa Gani yayi kamar an chanza ta, da ya lura da kyau se yaga ashe goge kwalliyar tayi. Da makeup kyau, babu makeup kyau. He will be the most luckiest man idan ya auri khairi.

Buffet ne aka kawo, abinci kala kala wanda da yawa daga ciki bata san sunan su ba. Daga shinkafa se chicken take iya ganewa a cikin abincin, ragowar tulin abincin bata san menene ba. Ko a kano ba yawo take ba saboda Rayuwar ta simple dai dai ita.

Abinci ya tula mata a plate dinta sannan ya tisa ta a gaba se ta cinye. Shi be kula nashi abincin ba

"Inde ba so kake na kasa tashi ba, abincin nan ya isa haka"
Khairi ta fada tana nishi irin da kyar take magana ma saboda koshi

"Me kika ci a nan, wannan dan abun da kika ci"
Ya fada yana zuba mata champagne a glass cup din da ke gaban ta

"Allah naci da yawa, kai banga ka ci komai ba"
Ta fada tana nuna plate dinshi da tunda ya zuba abincin a ciki be kara tabawa ba

"Na koshi ne kawai"

Tun break fast din da yayi wajen 11 na safe be sake cin wani abinci ba. Da gaske yunwar yake ji dazu amma damuwar da ke ran sa baza ta barshi ya iya cin abincin ba.
Tunda yaga kairi na kuka ya yanke hukuncin baze kaita gida a cikin kukan nan ba, ko yaya yana son ya mantar da ita bacin ran da umar ya sa ta, Ko da kuwa ze lullube nashi bacin ran ne.

Ya gode Allah da yaga ta sake rai har yana tsokanar ta tana dariya, ta maida komai ba komai ba kamar ma ba'ayi komai ba.
Ganin khairi a kusa da shi yasa hankalin shi ya kwanta na takaitattacen lokaci. Amma tunanin khairi zata kara hadu da umar washe gari yana daga masa hankali. Dama ace yana da damar da ze hana umar ganin khairi har abada

A bangaren khairi kuwa itama da nata sake saken da takeyi a kasan zuciyar ta. Tasan Abdulkareem yana son ta kuma har ga Allah itama ta fara son shi,
Tana son suyi maganar abunda ya faru amma tana tsoron yi, ganin yadda Ak yayi iya bakin kokarin shi yaga ya lallashe ta ta dena kuka. Bata son ta kara dawo da zance mara dadi a yanayi me dadin da suke ciki, yanayi na kwanciyar hankali.

This was her unofficial first date kuma bata son tayi ruining dinshi, duk da shima circumstance ne ya sa amma tasan zatayi cherishing wannan moment din for a long time.

Bayan ta gama cin abincin suka dan taba hira cikin nishadi. Se wajen karfen 10 na dare suka bar cilantro 🌿. Ak ya dawo da ita gida ba don ya so ba Idan ta shi ne ma su kwana a zaune suna hira.

Ya sauke ta a gida sannan ya juya ya nufi hanyar unguwar su. Daga rabuwa da ita har ya fara jin loneliness, ya fara missing dinta, ba tare da dogon tunani ba ya janyo Wayar sa yayi dailing number ta.

Da sallam ta amsa wayar daga jin muryar ta akwai mamaki a ciki ganin yanzun nan suka rabu
"Nayi mantuwa ne?
Ta tambaye shi

"Eh kinyi"
Ya fada yana murmushi shi kadai

Kallon hannun ta tayi wanda har a lokacin clutch na hannun, shigar ta gidan kenan ko daki bata karasa ba balle ta ajye wani abu

"Me na manta"
Ta tambaya tana kokarin tuno abunbuwan da ta fita da su a cikin clutch din

"My heart, kin manta kin tafi da shi"

Da sauri tasa Dayan hannun ta ta rufe fuska saboda kunya tana murmushi kamar yana gaban ta.
Kitt.... Ta kashe wayar don bata san answer da zata bashi ba.

🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Bintu. A
09034346763

SarkakiyaWhere stories live. Discover now