Kano 2

157 10 0
                                    

🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Tunda khairi ta isa gida iyayen ta suke nan nan da ita domin ta kwana biyu bata zo kano ba. Ba'a bar yan uwan ta a baya ba, sukayi ta siyo mata kayan kwadayi.
Duk yadda tayi kokarin burne damuwar da ke cinta se da umma ta gano amma batayi mata magana ba tana jiran idan ta kwana biyu se ta tambaye ta. Ita kuwa khairi jinta tayi at peace wato duk wanda ya bar gida gida ya barshi, babu inda yakai gida dadi saboda a gida ne kake zagaye da iyayen da suke sonka fiye da kansu, wadanda ganin su kawai ma yana saukar da nutsuwa. tayi missing gida sosai.

Da safe ma babu wanda ya fita har baban ta da yan uwanta maza, suka zauna a tsakar gida ana ta shan hira. Suna bata labarukan abun da suka faru lokacin da bata nan itama tana basu labarin yaran Aunty M da yadda suke shan dariya a gidan saboda fitinar yaran, duk dan ta boye kuncin da take ciki, ta ina zata fara basu labarin ta kwana a office din SS bama police ba, tasan hankalinsu ne ze fi nata tashi

Se bayan azahar sannan Aminu da Abdullah suka fita hidimomin su suka bar khairi da maman ta a gida.
Umma ta dauko comb tana tajewa khairi gashi tana cewa

"Bakya kuka da gashin ki yadda ya kamata duk kin bari ya lalace saboda rashin kitso"

Khairi tayi murmushi
"Wlh umma bani da lokacin gyaran ne, dan ina ga nafi sati ko comb ban sa ba balle ya ga mai"

"Haba khairi se kace ba mace ba"
Umma ta fada tana fizgar kan

"Aiki ne yayi yawa shiyasa"
Khairi ta bata ansa tana kanne ido saboda zafin tazar da umma take mata

"Yauwa ni kam yaushe ne zaki koma, ya kamata ki je cikin gari ki gaishe da kakannin ki, sun dade basu ganki ba"

Khairi tayi yake sanna tace
"Ay zan dade wannan karon, duk zanje na gaishe su. Akwai sakon Auty maimuna ma da zan kai can"

Daga nan suka ci gaba da hira cikin nishadi, suna zaunen ne wani yaro ya shigo yace wai ana sallama da ummulkhair

Ummulkhair tayi mamaki daga zuwan ta jiya har an san ta dawo, ita da tun da ta dawo bata leka ko kafar gida ba.

"Je ka ce bana nan"
Khairi ta fada ma yaron

"Aa tsaya"
Umma ta dakatar da yaron sannan ta juyo kan khairi.

"Ya zaki ce ya ce bakya nan. Duk yadda akayi yaron nan ne khalid dan Albarka, ko da ba kya nan yana zuwa ya gashe mu Wani lokacin har da tsaraba ma"

Umma ta juya ta kalli yaron

"Je kace ya shigo ta kofar gaba"
Kofar gaban kofar parlour ce sanna akwai kofa ta baya a tsakar gida wanda zaa iya bi a shiga parlon

Khairi ta fara mita cikin shagwaba
"Haba umma, haba umma. Ni nace bana son khalid amma kuka barshi yana zuwa har kuna karbar kayan sa. To ku tanadi kudin biyan sa don ba auren sa zanyi ba"

Umma bata kula ta ba ta ci gaba da tsince gashin da ya zuba a kasa, se da taga da gaske khairi ba tashi zatayi ta tafi parlon ba tayi magana

"Bana son iskanci, kin bar mutum yana ta jiran ki, wai mene haka. Ki tashi ki je mana"

Khairi ta zumburo baki

"Kin ganni fa, ba kayan arziki bane a jiki na, bari naje na dauko hijab, Allah saboda ke ce zan fita"
Ta tafi daki tana mita

Umma ta tashi ta shiga kitchen ta saka ruwa da lemo a kan tray, saboda tasan idan ta biye ma khairi baza ta kai masa ruwan ba. Ta saka hijab dinta ta nufi parlour.

Ta shiga da sallama wanda ta ci karo da saurayin da bata taba gani ba. Umar ta gani yana danne danne a waya. Da sauri ya dago kai don ya amsa sallamar da akayi.

Kamar an tsunkure shi ya mike tsaye da zafin nama har se da ya saki wayar da ke hannun sa a kasa ya fara salati.

Abun se ya daure ma umma kai ganin saurayin ya tashi a razane, ita ya kamata ta razana saboda a tunanin ta khalid ne tana zuwa taga wani daban.

Umar couldn't believe his eyes har ya fara tunanin ko mafarki yakeyi ko kuma kizo take masa.

A haka khairi tazo ta iske su. Tayi mamakin ganin umar a gidan su, dayan abun mamakin kuma shine yadda yake kallon umman ta, gashi a tsaye da shock a kwance a fuskar sa.

"Lafiya???"
Khairi ta tambaya

Umma ta juyo ta kalli khairi
"Waye wannan, kin san shi ne?

Khairi tayi yake sanan tace
"Tare muke aiki a abuja"
Tana gama fadin haka ta karaso kusa da umar sannan ta daure fuska tayi magana kasa kasa

"Me ya kawo ka gidan mu"

Ga de umar a gurin amma kamar gawa, ya kasa motsi bare yayi magana se kallon umma da yakeyi.
Itama umma se da taji wani iri ganin kallon da yake mata, duk se ta tsargu. Se kace yaga fatalwa.

Umma ta ajye tray din da ta dauko ta fita daga parlon da sauri.

Se a lokacin umar ya dawo da hankalin sa kan khairi da ke ta faman tambayar sa me ya kawo shi gidan su

"Wacece Wannan?
Umar ya tambaya yana nuna hanyar kofa da umma ta fita daga ciki

"Mamma na ce. me ya faru?

"Your mom, i mean birth mother?"
Ya kara tambaya kan sa duk a kulle

"Eh, menene wai?
Khairi ta tambaya dan tambayar tasa ta fara bata mamaki
Be bata amsa ba se gani tayi ya fita daga parlon ta kofar gaba, ya fita daga gidan ma gaba daya Ya bar khairi cikin confusion.

Yana fita ya dauko wayar sa ya kira number jidda yace ta turo masa number Alh ibrahim don bashi da number ma.
Bugu na biyu Alhaji ya dauka. Kafin yayi magana umar ya katse shi

"Where is my mom??"

"Mom kuma??"
Alh ibrahim ya tambaya
"Lafiyar ka kalau umar? me yasa kake tambayar maman ka bayan kasan bata raye"

"Where is my mom!!!!, dont tell me you were lying to me all this time. Ina mamana take!!!"

Kan Alh ibrahim ya daure har ya fara tunanin ko ya koma shaye shayen ne

"Where are you yanzu ka dawo gida. I think wani abu na damun ka just come home"
Alh ibrahim ya fada da lafazi tattausa saboda be san me ya samu dan nasa ba

"I am in kano"

Gaban Alh ibrahim yayi mumunar faduwa jin umar yace yana kano da alama abun da yafi tsoro a rayuwarsa ne ya faru.

🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Bintu. A
09034346763

SarkakiyaWhere stories live. Discover now