🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Zaune take ita kadai a office har gyangyadi ya fara dibar ta. Tunanin su intisar ya fado mata a rai, tasan yanzu Shirye shirye sun kankanma na anniversary. tayi missing mutanen office din musamman intisar da mahmud.
Ta gaji da zaman rashin aikin yi har karfe 11 ogan nata ma be karaso ba, ta yanke shawarar zuwa gaishe da su intisar.Batayi wani dogon tunani ba ta kwaso kafa tayo kasa. Tana zuwa ta tadda su intisar har suna ta aiki. Sunyi farin ciki da zuwanta, suka dan taba hira. Tana tuno umar ta mike saboda kar ya shiga office be ganta ba tasan zata samu matsala da shi, ba shiri tayi musu sallama ta fito
Rayuwar ta a company ta koma daga ita se umar, gashi har tayi sati daya a matsayin secretary umar, babu wanda yake shiga harkarsu su biyun kamar mayu. Bala'in sa karuwa yakeyi a kullum babu daman tayi lefi kadan se masifa, wani lokacin ma ba lefin tayi ba
Wani lokaci Idan tayi mishi magana se yaga daman ansawa. Shiyasa bata cika shiga harkar sa ba, Karkari tayi aikin dake gabanta. Idan kuma bata da aiki ta dauko waya suyi ta message da secret admirer .
Alakar su da secret admirer yayi zurfu sosai, bashi da aiki se yi mata messages, hira sukeyi sosai ta message wanda yake dauke mata kewa. Ranta be gama fita da cewar mal jabir bane duk da yace mata bashi bane. Wani bangare na zuciyarta na ce mata ba mallam jabir bane amma idan ta tuno da abubuwa da dama se taji babu tantama shi dinne. Koma de wanene tana jin dadin hira da shi.
Ta fito daga office din su intisar har ta kai farfajiyan reception taji message ya shigo wayarta, message din da ta gani ya bata mamaki har ta fara tunanin anya secret admirer nan ba aljani bane kuwa?
"You looked majestic in blue"
Message din da yayi mata kenanBlue din kayan ta saka kuma, a ina yasan ta saka blue din kaya, ta fara juye juye tana neman sa, a ina ya ganta, binta yakeyi ko me, a ina yasan ta bar bwari ma. Anya ba da aljani take magana ba kuwa. Tana kara juyawa ta ga Abdulkareem a bayan ta, murmushi ta saki wanda ya narkar masa da zuciya.
"Barka da safe"
Murmushin shima yayi sannan ya karaso inda take
"Barka da safe ummulkhair"Se a yanzu yasan beyi wahalar banza ba na kokarin kawo ta cikin Company ba, saboda yanzu ya rage tsoron yi mata magana musamman yadda ta saki jiki da shi. Kafin yayi mata magana ma ta gaishe shi.
Lokacin da ya sakko daga bene ya ga ta wuce ta shiga office din su intisar shiyasa ya zauna a reception yana jiran fitowar ta.
Wani irin farin ciki yake ji yana shigar sa ta ko ina, ya kwana biyu be ganta ba, ba wai dan ya so hakan ba kawai yana gudun kar su kara samun sabani da umar shiyasa be kara shiga office dinta ba.
Da yawan lokaci yana zuwa har bakin office dinta ya shafe mintuna a tsaye amma ya kasa kwankwasawa. Daga karshe sede ya bar bakin kofar jiki a sanyaye."Kina nan kuwa ummulkhair"
Ya tambayeta idon sa cike da annashuwa."Ina nan sir"
Ta ansa tare da fadada murmushin taDaga nan kuma se maganar ta dauke, ya rasa ma me ze ce mata. Idan a waya ne da yanzu ya cika ta da kalamai amma a fili ya kasa.
"Emmmm babu wata matsala a aikin ki de ko"
Daga karshe ya lalubo tambayar da ze mata."Babu wata matsala sir. Ba komai"
Tana gama rufe baki taga umar sandardar a gabanta, sun shagalta da magana da har umar yazo gurin basu san da zuwan sa ba, bare Ak da ya riga ya shiga wata duniyar ma.Tun shigowar sa ya gansu a tsaye suna magana, gaba daya su biyun se murmushi sukeye. Tsayuwar tasu ta bakanta masa rai matuka
Shi da yace mata be yarda ta kula kowa a company ba, me ma ya sakko da ita kasa har suka hadu da wannan wawanKhairi tana ganin shi ta hade rai, dukka annurin fuskarta ta dauke.
Haka shima Ak. cikin fushi yayi masa magana
"Lafiya ???yaya zako zo ka tsaya mana a gaba"
Kallon banza umar ya yi masa sannan ya juya kan khairi saboda bashi da lokacin sa"Me yasa kika bar office"
Khairi tayi mishi shiru"Kada ki bari na sake maimaita tambayar"
Idan da sabo ta fara sabawa da halinsa amma abunda ya bata mata rai shine yadda ze dizga ta a gaban Ak. Ko wani mutum baya so ayi masa cin mutunci a gaban wani bare ma wanda kake jin kunya.
Cikin bacin rai tace
"Wai me yasa......
Ta fara magana kenan Abdulkareem ya kalle ta suka hada ido a hankali ya girgiza mata kai alamar kar tayi magana, idonsa ya isar da sakon tayi hakuri kar ta tanka masa.Duk da ba magana yayi ba amma ta gane abunda yake nufi, tayi shiru ta sada kanta kasa,
Umar da ke tsaye gani yayi kamar ma sun raina masa wayo, wato har wani signal sukeyi da ido. Zuciyar sa yaji ta fara zafi cikin masifa yayi maganar
"Are you that stupid? ban fada miki dokoki na"
"What is wrong with you, menene matsalar ka ne wai"
Abdulkareem ya fada shima da masifa. Yayi tunani ze iya jurewa amma wulakancin umar gaba gaba yakeTun da yazo gurin khairi take jin ranta na zafi, duk kalmar da ya fada se taji bakin ciki na karuwa. Stupid din da yace mata yasa taji ta kai makura. Zuciyar ta ta fara tafasa.
Ga Abdulkareem ya hana ta magana, takaici yasa taji kwalla ta ciko mata ido.
A hankali ta dago ta kalli umar idon ta yayi rau rau, hayawe sun cicciko suna jiran kadan su zubo."Fisabillilah kayi min adalci"
Lafazin yadda tayi maganar me karya zuciya kamar abun tausayiCikin tashin hankali Abdulkareem ya kira sunan ta
"Ummulkhair"
ya kira sunan ta a hakali saboda yadda yaji muryar ta na rawa alamar kuka zatayiTa juyo suka hada ido, tana kallonshi taji hawayen da take kokarin maidawa ya zubo zirrr. Da sauri ta juya tayi hanyar bene ta barsu a gurin
🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Bintu. A
09034346763
YOU ARE READING
Sarkakiya
RomanceLabarin tsantsar soyayya me cike da sarkakiya ce ta kullu a tsakanin su. Ummulkhair ta zamo Allura cikin ruwa wanda me rabo ne ze dauka. Shin wa zata zaba a cikin su? Boyayyen masoyi Abdulkareem wanda yayi dakon soyayyar ta na tsahon lokaci ko kuma...