Ango

196 5 0
                                    

🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Ji tayi hannun da ta riko plate na karkarwa, hawaye na zirara daya na bin daya. Ta taho kawo wa babanta ruwa taji yana masifa shine ta labe a corridor da ta hada kitchen da falo tana sauraron abun da yake fada, tun wayarsa da hajja da maganar da sukayi da mamanta.

Se innalillahi wa inna ilaihi raji'un take maimaitawa, a gurin ta dire plate din pure water tayi daki da gudu ta fada a kan gado tana kuka. Baa gama maganar auren ta ba har an fara na matar da ze kara.
tasan Yaya Abdulkareem ba son ta yake ba amma ta sha Alwashin bayan auren su zatayi kokarin ta shanyo hankalin shi kanta tare da dagewa da addua har Allah yasa ya fara son ta, to yanzu da ake maganar ze kara aure yaya makomar ta ze kasance a gidan shi?
A ina zata samu damar da zata cusa kanta gare shi bayan ya auri muradin zuciyar sa. Zata iya hakurin rashin bata soyayyar shi amma baza ta iya hakurin ganin ya bawa wata kulawar shi ba alhalin itama a matsayin matar sa take.

Taci kuka me isar ta sannan ta tsurawa kayan ta da take tattarawa ido, ita a lallai aure zatayi tana sorting kayan tafiya da shi gidan miji. Aunty bebi ta shigo dakin ta zauna a kan gado kusa da maryam tare da taba kafadar ta.

"Me kikeyi a kwance kin bar kaya a barbaje a kasa"

Maryam ta dago da jajayen idanun ta ta kalli Aunty bebi
"Mummy aure yaya Abdulkareem zeyi bayan ya aure ni?"
Ta tambaya idanun hallowed.
Aunty bebi ta ja dogon numfashi sannan tace

"Idan banda abunki namiji ay mijin mace 4 ne, idan yana da ra'ayin kara aure bamu isa mu hana shi ba ay"

"Amma mummy tsohuwar budurwar sa fa, har yanzu yaya be dena son ta bane?
Maryam ta fada hawaye ya ziraro a karshen maganar ta

Aunty beni ta kara gyara zama sannan tace
"Yanzu maryam bari na tambaye ki, tunda kika dawo gidan nan Abdulkareem ya taba zuwa ganini ki a bisa matar da ze aura nan da kwana kadan?"

Maryam ya girgiza kai a hankali
Aunty bebi ta dora da cewar
"Bar maganr zuwa ma, ya taba kiran ki a waya tunda kika dawo"

Nan ma maryam ta girgiza kai
"To meyasa zaki damu kije inda ba'a mararin ki, inda ba'a damu da ke ba. Shifa namiji idan baya son mace  da wahala ya dawo ya so ta daga baya. Mace ce zaayi mata dole kuma daga baya ta so mijin har ta zauna da shi. Tun da yarintar ki zaki daurawa kanki  hawan jini akan wanda be damu da ke ba.
Har ga Allah bana son auren ki da Abdulkareem saboda nasan wahala zaki sha. Gwara ki samu wanda ze so ki, ya mutunta ki ya kula da ke. Yanzu ma kika fara rayuwa idan da tsawan rai gaggawar na menene"

Haka auty bebi tayi ta ma maryam maganganu tare da nusar da ita matsalar auren Abdulkareem, se da suka kwashe kusan minti 40 sannan daga baya Aunty bebi ta bar mata dakin, ta bar maryam da zurfin tunani. Tabbas abun da mamanta ta fada gaskiya ne to amma ya zatayi da soyayyar Abdulkareem da ke cinta a zuciya.
Da wannan tunanin tayi bacci, shima baccin rabi da rabi tayi shi.

Hajja ma haka ta kwana tana juya abun a ranta, tayi tunanin Alh wada zeyi reasoning da ita amma se taga abun ba haka bane, ya rufe idanun sa gam daga gaskiya.
Ita de ta yanke hukuncin zata bar Ak ya auri ummulkhair tunda lefin ba nasu bane, kaddara ce tazo musu a haka

Washe gari da safe hajja ta samu Ak a daki yana ta shiri, yayi wanka ya saka kaya yana zuba tarkacen shi a jaka.
Hajja ta wangale baki ganin shirin da yake yi

"Ina zaka tafi da safen nan haka"

Ak ya rusna ya gaishe da hajja tare da fadin
"Zan koma wajen aiki ne"

"Zaka koma wajen aiki ko kuma zaka kara guduwa, sauran kwana 6 auren ka fa"

Ak ya karaso inda hajja take tsaye sannan yace
"Hajja sati daya aka bamu mu huta bayan dawowar mu daga paris, dole zan koma nayi reporting sannan na dawo kafin lokacin auren"

SarkakiyaWhere stories live. Discover now