🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Jidda ta shigo office din bayan mintuna kadan da kiran da Alh ibrahim yayi mata. Yayi mata nuni da kujera akan ta zauna. Ta ja ta zauna sannan ta gaishe shi cikin girmamawa."An fitar da list din mutanen da sukayi passing interview?"
Ya tambayi jidda"Yes sir jidda ta answer"
Alh ibrahim ya nisa sannan yace
"Akwai wata da suka samu sabani da Umar jiya a reception kin san wacece?"
"No sir, amma de nasan sunan ta"
Ta amsa cikin girmamawa"Mene sunan ta"
ya fada yana kara karkato hankalin sa kan jidda"Ummulkhair, amma ban san surname dinta ba"
"Has she been selected" ya kara tambayar jidda.
"Zanyi confirming se na sanar da kai sir"
ta tsaya tana jiran abunda ze kara fada"To me kike jira? Je kiyi confirming. Idan ma baa selecting dinta ba ina son a dauke ta"
Da sauri jidda ta tashi ta nufi kasa inda office din human resource yake.Tana shiga ta tarar da miss cynthia A kan kujera da files da yawa a gaban ta. Da alama aiki takeyi sosai. Suka gaisa sannan ta nimi kujerar da ke kallon miss cynthia Ta zauna
"Akwai wata candidate na interview me suna Ummulkhairi ina son sanin status dinta ne"
Miss cynthia Ta fara dube dube a kan table har ta zaro wani file me dauke da list din candidates na interview, ta bude ta fara duba sunan
"Unfortunately she is not selected"
(An samu Akasi baa dauke ta ba)
Miss cynthia Ta fada a takaice"Menene dalilin rejection din"
Jidda ta tambaya"Bata gama service ba, Infact she is currently serving now, takardunta sunyi kyau and she is smart."
Ta danyi shiru sannan ta dora
"Amma tayi suggesting ko bamu dauke ta aiki ba tana son karasa service dinta a nan. But kin san yanzu bamu da slot na coppers so we had to reject it as well"Jidda tayi shiru tana sauraron miss Cynthia tana tunanin yadda zatayi handling abun
"Accept her as a copper and after she had finish serving we can retain her as permanent staff"
(A dauke ta ta karasa service din idan ta gama se a dauke ta a matsayin cikakkiyar ma'ikaciya$Miss cynthia Zatayi magana jidda ta dakatar da ita saboda tasan me zata ce
"Order ne na executive director"
Miss cynthia Ta gyada kai sannan tace "done"
Jidda ta fito daga office din ta nufi hanyar bene a ranta tana tunanin yadda Alhaji da kansa ya karya dokar da ya sa da kansa. Dukkan wanda ka gani a company chancanta ne yasa aka dauke shi aiki ba wai connection ba. Domin kuwa alhaji yana da tsatsauran principles shiyasa ma ko gurin neman maaikata link ake saka yadda kowa ze iya samun damar applying, ta yadda zaa tantance gwani . duk da cewa company private ne.
Ita kanta Miss cynthia yau ne case na farko da Alh ya sa baki a procession din daukar maaikata, yakan bar musu wuka da nama suyi komai bisa ka'idar aiki. bayan fitar jidda ma se da ta dauko file din khairi ta kara dubawa.
Jidda na tafiya zata koma office dinta taga Ak kamar an wullo shi yana saukowa daga bene da sauri. Murmushi sosai tayi domin kuwa yau gaba daya bata ganshi ba, shi din take bukatar gani . Shima murmushin yayi mata sannan suka gaisa
"Chief secretary" ya tsokane ta
"Ga kuma chief engineer ba"
Sukayi dariya gaba daya"Yauwa ni kam ina son tambayar ki abu, an fitar da list din wadanda zaayi hiring ne"
"Aa tukunna de, ina tunanin basu gama ba don daga can nake"
Ta bashi ansa"Yauwa dan Allah ina so ki duba min status din ummulkhair"
"Ummulkhairi kuma????
Ta fada da mamaki a fuskarta"Eh Ummulkhairi, kin gane ta ay wadda suka samu sabani da MD"
"Ehhhhh..... nagane" ta ansa a sanyayye
Annurin da ke fuskarta ne ya dauke gaba daya, hasken da ke cikin idonta ya disashe"To ita, dan Allah ki duba min ko anyi accepting dinta"
"Okay" kawai ta iya ambatawa sannan ta ja kafarta a hankali ta barshi a tsaye a gurin. Bata da kuzarin fada masa hukuncin da Alh ibrahim yayi. Koma menene ya ji daga baya
"Ummulkhairi? Wacece Ummulkhairi nan da kowa ya damu da ita, zuwanta na farko se da suka samu sabani da MD. Ga Alhaji ibrahim yace a bata aikin, abun da be taba yi ba kenan.
Sannan yanzu kuma Abdulkareem dinta ma yana tambayar lamarin ta.
Bata taba ganin Ummulkhairi ba, don ko abun da ya faru tsakanin ta da umar ma labari ta ji.Haka tayi ta sake sake har ta isa office dinta. Zuciyar ta akwai shakku game da lamarin Ummulkhairi. Addua tayi da fatan kar ta zame mata matsala. Daga baya ta ture komai dake ranta ta shiga aikin ta gadan gadan.
Ak ma office dinsa ya koma yayi ta adduan Allah yasa a dauki Ummulkhairi aiki. Ganin ta da yayi jiyan ba karamin tada masa da hankali yayi ba, ya kwana biyu be ganta ba daman. kyaunta ma kamar karuwa yayi, Ya kara jin son kasancewa tare da ita more than ever .
🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Bintu. A
YOU ARE READING
Sarkakiya
RomanceLabarin tsantsar soyayya me cike da sarkakiya ce ta kullu a tsakanin su. Ummulkhair ta zamo Allura cikin ruwa wanda me rabo ne ze dauka. Shin wa zata zaba a cikin su? Boyayyen masoyi Abdulkareem wanda yayi dakon soyayyar ta na tsahon lokaci ko kuma...