Muhawara

179 13 0
                                    

🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Yau kwanan Ummulkhairi biyu a kano, tunda ta dawo bata samu sukuni ba, kanta ya kulle gaba daya, abuja ma ta fitar mata a kai. Ta rasa me zatayi ta ji dadi. Tunda ta dawo bata fada ma iyayen ta dalilin dawowar ta ba kawai ce musu tayi zata kwana biyu sannan ta koma.

Umma ce ta shigo dakin ta tarar da ita a kwance kamar me bacci amma ba baccin take ba, Ta sa kafa ta dan shure ta kadan
"Wai me kike yi ne a kwance tun dazu"

Khairi ta dago kai ta kalli umman ta da ke tsaye a kanta
"Umma kai na ke ciwo shiyasa"

Umman ta samu guri kusa da ita ta zauna sannan tace
"Yaushe ne zaki fada min abunda ke damun ki? Tunda kika dawo na kula akwai damuwa a tattare da ke, nayi miki shiru nayi tunanin zaki zo da kanki ki fada min abunda ke damunki amma baki fada ba, hankali na ya kasa kwanciya"

Cikin raunanniyar murya khairi tace
"Ba komai umma, kawai bana jin dadi ne"

Umma ta zare ido dan ta tsoratar da ita
"Kehh!!! Kalle ni cikin ido, bana son ki raina min hankali. Ki fada min abunda ke damun ki yanzun nan ko na bata miki rai wallahi"

Khairi tasan halin umman ta, ba mace bace me sauki balle akan abun da ze shafi yaran ta.Tasan idan batayi magana ba ranta ne zeyi mumunan baci

Khairi ta bata labarin dukkan abun da ya faru daga farkon sa har karshe bayan ta gama ta fashe da kuka. Se a lokacin ta samu dan sanyi a zuciyar ta, taji kamar ta sauke wani babban nauyi a zuciyar ta.

Umma salati ta dinga yi tun daga farkon labarin har karshe. Daga karshe ta godewa ubangiji da ya kare mata yarinyar ta ya tsare mata mutuncin ta. Kuka itama umman tayi sosai har se da khairi ta koma tana lallashin ta

Se da suka nutsu tukunnan umma tace
"Barinki abuja ya kama gwara ki dawo gida na dinga jin motsin ki hankali na ze fi kwanciya"

"Umma nima ina son na dawo gidan amma ya zanyi da service dina, sauran mu wata 6 fa, se yanzu mukayi rabi

Cikin dakakkiyar murya umma tace
"Dole a san yadda zaayi ki dawo kano, bazan kara bari kiyi nisa da ni ba"
har a lokacin da hawaye a idon ta.

Haka suka ci gaba da tautauna abun da ya wakana har abban ta ya shigo gidan basu sani ba, ya shiga dakin da wasa

"Yau kuma dukkan ku daki kuka shige, to me ake tattaunawa ne"
Se da karasa shiga sannan ya lura da yanayin su, sunyi jugum jugum babu walwala a fuskar su.

"Me ya faru a gidan ne, lafiya na ganku haka"
Ya tambaya tare da neman guri ya zauna kusa da umma

Umma ta kwashe dukkan abun da ya faru da khair ta fada masa. Shima Abba salati ya dinga yi yana mamakin yadda yarinyar sa ta sha da kyar, tunanin irin halin da ta shiga a lokacin kadai ya isa ya sa hawaye a fita a idon sa

Abba namiji ne amma umma har ta ta fi shi jarumta, don umman na da zafi shi kuwa sanyi gareshi kamar ruwan sanyi. Shiyasa ya shaku da yaran sa sosai.

Suka gama jajantawa sannan abba ya yi ma khairi da sauran yan uwanta adduan kariya daga sharrin mutum da aljan a duk inda suke.
yace ma umma ta bar khairi ta huta yana san suyi magana da ita. Umma da abba suka fita suka bar ummu a dakin.

🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Washe gari ranar alhamis da safe akayi mata message na tunin interview dinta da zaayi ranan monday. Da Number da aka turo mata da link din aiki da shi aka sake turo mata na tunin interview. Ita da take tunanin ta gama zama a abuja wani interview zata je tayi ne.

Ta gama abun da takeyi ta koma falo inda ta tarar da abba da umma suna karyawa. Ta gaishe su sannan ta samu guri itama tayi breakfast, Bayan ta gama ne abba yayi magana
" ummu mun yake shawarar ki koma abuja ki ci gaba da service dinki"

Ta zaro kwala kwalan idon ta
"Abba na koma abuja kuma??"

"Eh zaki koma amma baza ki zauna a ushafa ba, zaki zauna a GARKI gurin kanwar umman ki. Don munyi mata Alkawari ma da farko a wajen ta zaki  zauna se kuma Allah beyi ba.

Khairi tayi shiru tana tunanin ko abunda abban ta ya fada din shine mafita, dole zata koma abujan ma dan tayi kokarin a dawo da ita kano, wannan process din ma ze dauki lokacin.

Ta tuna da interview da ake bukata taje ranar monday sanan tace
"Abba aikin da nayi applying a abuja ma sun kara turo min message din tunin interview"

Abba ya gyara zama
"Tooh wannan ma baze gagara ba, kije interview din muga abunda Allah zeyi"

Umma tayi sauri tace
"Aa abba, muna kokari mu rabata da abuja kano son kara tura ta"

Abba yayi dariya sannan yace
"Haba zahra'u bawa baya taba wuce kaddarar sa, sannan abunda ya faru a abuja ze iya faruwa a ko ina ay. taje tayi din Allah ya zaba mana abunda ya fi zama alkhairi. Sannan a kullum muna yi mata adduan Allah ya ci gaba da kare ta a duk inda take"

Umma ta kara cewa
"Baka tunanin maganar mutane ace mun barta a abuja tana aiki"

Abba ya sake murmushi
"To ki jira ma ta samu aikin tukunna, tun batayi interview ba kin fara kawo kabali da ba'adi"

"To aure fa"
Umma ta sake soko masa wata tambayar

"Banda abinki zahra'u  miji duk inda take ze zo ya same ta ay. aure lokaci ne mu bar wa Allah ragamar komai. Namu kawai addua ne"

Haka abba da umma sukayi ta muhawara, ita de khairi se ido, Kanta ya kulle gaba daya.

🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Bintu. A
09034346763

SarkakiyaWhere stories live. Discover now