🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Ganin ummulkhair ta shiga motar Abdulkareem ya bata masa rai matuka Ji yayi zuciyar sa na zafi. Abun takaicin ma yadda yaga Ak yana ta nan da nan da ita. Da yasan Ak ne ze kaisu baze taba bata izinin ta tafi ba kwata kwata.
Wayarsa ya zaro ya kira bolt. Cikin mintuna da basu wuce 10 ba motar ta iso. Yana shiga yace ma me bolt din ya kaishi inda ake siyar da mota, be yi niyar siyan mota kwata kwata a Nigeria ba saboda a tunanin shi ba zama ne ya kawo shi Nigeria ba. Allah Allah yake ya gama abunda zeyi ya koma America.Ganin khairi a motar Abdulkareem ne ya tunzuro shi , be tsaya wani tunani ba ya tafi siyan mota, idan da yana da mota ze ce dole shi zata bi ay.
Suna isa ya sallami me bolt ya shiga gurin siyan mota na SS motors da ke kwaryar cikin garin Abuja. Guri ne wanda ake siyar da motoci na Alfarma.
An zagaya da shi show room inda motocin suke a parke.
Wata bakar BMW ce ta dauki hankalin shi. model 230, w series. Motar iya haduwa ta hadu.
A take aka kirawo Manager gurin suka yi sealing deal. Umar ya biya milyoyin kudi sannan ya shiga sabuwar motar sa ya bar wajen.A gefen su Abdulkareem kuma suna ta yawon zaga guraren da aka shirya zuwa, se yamma likis suka gama ya sauke intisar a gidan su sannan suka nufi hanyar unguwar su khairi.
Tun bayan fitar intisar motar tayi tsit, daman itace uwar surutun.Khairi ta kasa sakewa a motar tun bayan saukar intisar , wani sabon kunyar Abdulkareem take ji, duk sanda suka hada ido se taji gaban ta ya fadi. Ga daman Allah yayi ma Ak dara daran ido masu tsananin kyau, idanun da suke kashe jikin me kallan su.
Ak yayi gyaran murya da karfi wanda ya janyo hankalin khairi ta juyo ta kalle shi. Shirun yayi yawa gashi har su kusa isa estate din su
"Dinner din gobe 7pm ne immediately bayan sallah magrib"
Abdulkareem ya fada yana dan satar kallon ta."Eh haka ne ko"
Khairi ta amsa ba tare da kalle shi ba, ta ci gaba da kallon titin da ke gabansu."Zan biyo na dauke ki"
"Da ka bari wlh, Akwai driver da ze kaini"
Khairi tayi saurin katse shi."Unguwar mu daya fa, ba se kin bawa driver wahala ba ki bari kawai zanzo mu tafi tare"
Ya fada tare da kanne ido yana Addua'an Allah yasa ta amince""Allah ya kaimu goben, zamu ga abinda ze yu"
Khairi ta fada a dai dai lokacin da suka isa kofar gidan su.
A hankali tayi mishi godiya sannan ta fito daga motar ta nufi gate din estate dinsu."Ummulkhair"
Ak ya kira sunan ta a hankali, kamar baza ta juyo ba amma wani zuciyar tace ta juyo ko ta sake kallon fuskarsa.
Ta juyo a hankali ta kalle shi. Ya dago mata hannu yana mata bye bye tare da fadada murmushin da yakeyi sannan yace
"I enjoyed my day with you"A hankali itama ta daga hannu tayi mishi weaving tare da maida mishi murmushin itama.
Da sauri ta juya ta shige gida harda dan gudinta.🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Da kyar khairi ta iya tashi washe gari saboda gajiyar da tayi na yawon jiya da suka sha. Wayan driver da ya kawo sako daga Kano ne ya tashe ta.
Tun jiya ta kira gida aka hado mata kayan da ta dinka na bikin kawar ta saboda shi zata sa yau.
Ba ta taho da kayan occation Abuja ba gashi zaayi dinner. Duk kayan da ta tawo dashi yawanci dogayen riguna ne na sawa yau da kullum.
Shiyasa ta kira gida aka kai kayan tasha da yamma.Kamar baza ta tashi ba saboda kasala, haka ta daure ta shiga toilet tayi brush ta wanke fuskarta sannan ta sako palazzo da Tshirt ta ziro hijab dinta.
A falo ta ci karo da Aunty maimuna ta fada mata zata je karban kayan ta a tasha."Tsaya nayi breakfast se na ajye ki tunda hanya ta ce"
Cewar Aunty M.Cike da jin dadi khairi ta ansa
"Yauwa Aunty M, nima bari nayi kafin ki gama"
Sai da suka gama breakfast sannan suka fito, Aunty maimuna ta ajye ta a Jabi park sannan ta wuce aiki.
khairi daman basu da aiki yau Se dinner da zasu je karfe 7 na dare.Ta shiga cikin park din kenan taji wayarta na ringing, ta zaro wayar a aljuhun palazzo da ta sa.
Sabuwar number ce tayi kiran ta. Batayi wani dogon tunani ba ta daga wayar tare da yin sallama.A dakile mutum da ya kira ya amsa sallamar sannan yace mata
"Meet me in the office now"Tun daga amsa sallamar ta gane Umar ne, saboda wannan kaukausar muryar tasa baza ta taba buya ba.
Gabanta yayi mumunar faduwa da taji yace ta same shi a office.
Office din da ba aiki yau, me zata je tayi mishi, ita da ko wanka batayi ba.Be jira answer ta ba ya katse wayar sa. Ji tayi ranta ya fara baci, ta fara mita ita kadai.
Ta karsa cikin park din Ta karbi sakon a gurin driver sannan ta fito daga tashar tana tunanin ta koma gida ta shirya sannan ta tafi office din ko kuma ta wuce a haka ne
Wayar ta ce ta kara ringing, ta duba ta ga number da umar ya kira ta ne, a tsorace ta daga wayar. Kafin ta kai ga yin sallama yace mata
"Dont make me wait for long"Nan ma be bari tayi magana ba ya katse wayar.
🍒🍒🍒🍒🍒
Bintu. A
YOU ARE READING
Sarkakiya
RomanceLabarin tsantsar soyayya me cike da sarkakiya ce ta kullu a tsakanin su. Ummulkhair ta zamo Allura cikin ruwa wanda me rabo ne ze dauka. Shin wa zata zaba a cikin su? Boyayyen masoyi Abdulkareem wanda yayi dakon soyayyar ta na tsahon lokaci ko kuma...