Tun farko

165 12 0
                                    

🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Labarin ya fara shekara 34 da suka wuce. A lokacin da Alh ibrahim yake tashen samartakar sa. Ko da girman sa kana kallonsa kasan handsome dattijo ne bare kuma ace lokacin da yarinta.

Ibrahim malami ne da ke koyarwa a DALA boarding school ta mata a kano, nan ya hadu da ZUHRA wadda a lokacin tana aji uku na secondary. Soyayya ce me zafi ta kullu tsakanin zuhra da ibrahim yadda kusan ko da yaushe suna tare, idan anyi hutun makaranta ma yana zuwa wajenta su sha hira. Soyayyar da ibrahim yake ma zuhra ba abun mamaki bane ganin yadda itama Zuhra kyakyawar budurwa ce wadda take dauke hankali maza duk inda ta gifta

A family din su zuhra suna da wani al'ada na auren dangi, shiyasa duk inda ka ga yan family zaka gane su saboda tsananin yadda suke kama da juna.

Ibrahim da zuhra Sun gamu da tashin hankali lokacin da zuhra ta gama makaranta aka hada ta aure da cousin dinta, zuhra ta balle tace nan duniya bata ga mijin da zata aura ba se ibrahim. A kayi ta rikici, iyayenta suka dage se ta auri zabin su itama ta nuna nata taurin kan.

Daga karshe de ibrahim da zuhra suka gudu daga kano sukayi wani gari a katsina. Da isar su suka samu limamin masallacin garin da suka je ya daura musu aure.

Bayan wata uku da bacewar su ibrahim da zuhra suka koma gidan iyayen ibrahim a Rano. ko a can gidan iyayen sa ansha rikici kafin suka yarda suka karbe su saboda babu yadda zasuyi, Aikin gama ya gama tunda ga zuhra har da karamin ciki.

Ibrahim da zuhra suka ci gaba da zama a rano har zuhra ta haihu ta haifi yaro namiji aka sa mishi suna umar. Se da zuhra tayi arba'in sannan suka yanke hukuncin zuwa kano gidansu zuhra domin su nemi yafiyar iyayen ta.

Bayan zuwan su kano an sha gwagwarmaya, iyayen zuhra suka ki karbar su, karshe ma suka ce basa san su kara ganin kafar su a gidan. Haka suka ja kafa jiki a sanyaye suka koma rano.

Gidan su zuhra babban gida ne, dukkan su a gida daya suke (family house). Gida ne tun na kakanin su da kasuwanci ya kawo su kano daga libya. Yayan gidan (iyayen su zuhra) a gidan sukayi aure, kusan kowa se da yayi mata a kalla 2 ko 3 suma suka hayyayafa. Daga nan aka yan yanka gidan kowa ya samu sashen sa da kofa da ta raba. Aka ci gaba da auratayya a tsakanin yan uwa. Gida ne wanda kusan yara matan gidan duk sunan su fatima ne sede a samu banbancin lakani. A nasu Aladar gida be cika gida ba idan fatima basuyi yawa a ciki ba.

A sashi daya zaka iya samun fatima sun kai biyar. A sashin su zuhra ma haka abun yake, yayan babanta sun kai 16, mata 9 maza bakwai wanda rabi a cikin matan sunan su fatima. Akwai zahra, zuhra, zakiyya, bintu, fatum, batula, duk wani nau'in sunan fatima akwai a gidan

Zahra ( mamna khairi) kanwar zuhra ce (maman umar). Zahra ke bin zuhra uwarsu daya ubansu daya.

Idan yaro yayi lefi a gidan jajaye iyayen shi ya jawowa abun kunya, Ga gida da yawa se ayi ta gutsiri tsoma. Zuhra ce mace ta farko da ta fara guduwa saboda an hada ta aure da dan uwanta, ta shafawa yan sashin su bakin jini da abun kunya. Shiyasa iyayen ta suka kasa yafe mata

Zahra tana kallo yayarta ta tafi tare da dan ta rike a zani. Tayi kuka da bakin cikin rabuwa da yar uwar ta,

Ibrahim da zuhra suka dawo rano suka ci gaba da zama, bayan wata 6 da haihuwar umar ibrahim ya samu Aiki a calaba Ya bar zuhra a rano ya tafi calaba. A nan ya hadu da baturiya sarah.

Tun bayan haduwar sa da sarah ibrahim ya chanza gaba daya, se ya dade be dawo rano ba, ko yazo ma se suyi ta samun sabani da zuhra har ta gwammaci ya zauna a can calaba tafi samun kwanciyar hanklai. zuhra ta ci gaba da rainon yaron ta har aka shekara daga nan kuma ta hadu da ciwo.

Akayi ta magani ciwo yaki ci yaki cinyewa, anyi na gida da asbiti duk babu wanda aka dace. A wani zuwan da ibrahim yayi ne ya tarar da matar sa a wannan yanayin. Wata rana ya dauke ta zuwa kano ya bar umar a rano wajen mamansa. Ko da suka isa gidan su zuhra yace mata ta shiga ze biyo ta a baya. Tunda ta shiga gidan ibrahim yayi gaba abun sa, be tsaya a ko ina ba se calaba.

Dole iyayen zuhra suka karbe ta ganin halin ciwon da take ciki. A ka ci gaba da magani tare da sa idon dawowar ibrahim. shiru shiru ibrahim be dawo ba har Allah yayi ma zuhra rasuwa.

Se bayan ya ji rasuwar zuhra sannan ya dawo kano a lokacin anyi bakwai da rasuwar ta. Ta rasu da ciwon hanta wanda ba'a gane ciwon ba da farko se da taci karfin ta, ta rasu da kewar dan ta umar wanda aka tsige daga nono lokacin yayen shi beyi ba, ta rasu da bakin cikin ibrahim wanda ya watsar da ita bayan yaci moriyar ganga.

Bakin cikin abun da yayi ma zuhra ne yasa iyayen ta da yan uwa sukayi ma ibrahim rashin mutunci da yazo ta'aziya. Bakin cikin abun da yayi musu ya tsaya a zuciyar duk dangin su. Taki kowa se shi amma daga karshe shine mutum na farko da ya watsar da ita a lokacin da larura ta same ta, a lokacin da ta fi bukatar sa. A zafin ciwo har ta kan ce ubangiji yasa ciwon da ya same ta ya zama sillar kaffaran bijire ma iyayen ta da tayi.

Tun daga abun da ya faru a kan zuhra aka hana auren dangi a family, aka bar kowa ya kawo zabin sa. Jefi jefi ana samun wanda jininsu ya hadu har suka kulla soyayya a dangi, amma da yawan su a waje sukayi aure harda zahra (maman khairi)

Dangin zuhra basu kara ganin ibrahim ba se labarin auren shi da baturi da suka ji, har ma ya tafi da dansa umar America. Tun daga wannan ranar basu kara jin labarin ibrahim ko dan sa umar ba.

🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒

"Wannan shine labarin ka umar, labarin mahaifiyar ka"

Ba abun da umar yakeyi se kuka har da shesheka, tabbas maman shi ta wahala. Be taba sanin irin wahalar da ta sha ba kenan. Se yau ya kara tabbatarwa baban shi ba mutum bane, mutumin da ya zalincin matan sa duk biyun. Ji yayi ya kara tsanar sa, da ze iya chanza uba da yau kam ya chanza. matansa duk biyun sun rasu da bakin cikin sa a zuciya.

Alh ibrahim ma kukan yake ta yi yana tuno zuhra da yanayin rayuwar soyayyar da sukayi da yadda tayi mishi halarci ta rabu da iyaye da yan uwa duk saboda shi. Amma ga abun da ya saka mata da shi, kaico, tun bayan rasuwar zuhra ya fara nadama amma nadaman da yayi a yau ya fi na ko yaushe.

Kowa kuka yakeyi a dakin har abba da ya zama dan kallo. Khairi ma kuka takeyi sosai jin labarin abun da ya faru da Aunty ta, yayar mamanta kuma mahaifiya ga umar . Tasan mamanta tana da yaya zuhra wadda ta rasu da dadewa amma bata san tayi aure ba ma balle tasan tana da da.

An dena maganar ta ma a gidan sede jifa jifa idan an tuno ace Allah ya jikan zuhra. Yan uwanta da suka fito ciki daya suna mata addua kullum tare da addu'an Allah ya kare danta a duk inda yake

Bayan an dau lokaci ana jimami da koke koke suka tattara gaba daya suka nufi can cikin gari gidan kakanin khairi da umar, kakannin da umar be san da su ba se a ranar.

A can ma haka akayi ta kuka da jimami, duk yan uwa aka hallara ganin umar. Washe gari Aunty M ta duro kano tare da yaran gaba daya, tana ta mamaki da alhinin sabon Alamari.

🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Bintu. A
09034346763

SarkakiyaWhere stories live. Discover now